Ambaliyar Neja: Babban Masallaci Ya Rufta kan Musulmai, Sama da Mutum 100 Sun Rasu
- Rahotanni daga garin Mokwa na jihar Neja sun nuna cewa zuwa yanzu an ciro gawawakin mutane sama da 115 a ambaliyar ruwa
- Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja (NSEMA) ta tabbatar da hakan, ta ce har yanzu ba a gama gano waɗanda ibtila'in ya rutaa da su ba
- Mazauna Maokwa sun ce ambaliyar ta rutsa da wani babban masallaci da mutane suka fake a ciki, da yawan masu ibada sun rasu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Niger - Tawagar masu aikin ceto da neman rai a wurin da ambaliya ta auku a Mokwa, jihar Neja, ta ce akalla gawarwaki 115 aka gano zuwa yanzu.
Rahoto ya nuna cewa ambaliyar ruwan ta tafka ɓarna a ƙaramar hukumar Mokwa, inda ta rusa gidaje tare ɓarnata dukiyoyi masu ɗumbin yawa.

Asali: Facebook
Daraktan Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta jihar Neja (NSEMA), Abdullahi Baba Arah, ne ya tabbatar da hakan ga jaridar Leadership ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Ibrahim Hussain.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Ambaliya: Mutane sama da 100 sun rasu a Neja
A cewarsa:
“Sabanin rahoton da ke yawo a wasu kafafen yaɗa labarai, hakikanin lamarin shi ne an ciro gawarwaki 115 zuwa yanzu. Muna ci gaba bincike.”
Abdullahi Arah ya ƙara da cewa, fiye da gidaje 300 ne suka lalace sakamakon ambaliyar da ta faru a ranar Alhamis a Mokwa, hedikwatar karamar hukumar Mokwa.
A baya, rahotanni sun nuna cewa mutane kusan 20 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka ɓata.
Ambaliya ta rutsa da matafiya a Mokwa
Sai dai, ya bayyana cewa a yanzu adadin waɗanda aka tabbatar sun mutu bayan ciro gawarwakinsu sun kai 115 daga bayanan da aka tattara zuwa ƙarfe 5:00 na yammacin ranar Juma’a.
Wasu mazauna yankin sun shaida wa Daily Trust cewa al’umma na cikin zullumi da kaduwa, inda wasu iyalai suka rasa kusan dukkan ‘yan gidansu.
Har ila yau, matafiya da dama da suka tsaya a Mokwa domin yin salla ko kwana, kamar yadda aka saba, ambaliyar ta rutsa da su.

Asali: Facebook
Mokwa: Babban masallaci ya rufta kan musulmi
Makarantun yara da wuraren ibada sun nutse cikin ruwa, lamarin da ya kara tsananta halin da jama’a ke ciki. Wasu mazauna sun ce adadin waɗanda suka mutu na ƙaruwa kowace rana.
Wani babban masallaci da mutane suka fake a ciki ya rufta kan musulmi masu dumbin yawa, shaidu sun ce har waɗanda suka hau kan rufin masallacin ba su tsira ba.
Duk da cewa ba a gama tantance adadin mutanen da suka mutu ba, an yi imanin da dama daga cikinsu ruwa ya wuce da su zuwa kogin Neja ta magudanan ruwa daga Kwarin Rabba da Koshaba.
Gwamnoni 36 sun yi alhinin ambaliyar Neja
A wani labarin, kun ji cewa gwamnonin jihohi 36 a Najeriya sun nuna damuwa da ambaliyar ruwan da ta ruguza gidaje da laƙume rayuka a jihar Neja.
Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta bayyana alhini kan ambaliyar da ta kashe mutane da dama a Mokwa, jihar Neja.
Kungiyar ta ce tana tare da gwamna Umaru Bago da al’ummar jihar Neja a wannan lokaci mai cike da kunci da baƙin ciki.
Asali: Legit.ng