'Yan Sanda Sun Kama Wanda Ya Jagoranci Kashe DPO a Kano da Wasu Mutane 40

'Yan Sanda Sun Kama Wanda Ya Jagoranci Kashe DPO a Kano da Wasu Mutane 40

  • Rundunar ‘yan sandan Kano ta tabbatar da kisan DPO na Rano, CSP Baba Ali, a yayin da yake bakin aikinsa a yankin
  • Bayan binciken gaggawa, an cafke mutane 41 da ake zargi da hannu a kisan, ciki har da wanda ake zargi ya jagoranci aikata laifin
  • Kwamishinan ‘yan sanda ya tabbatar da cewa za a tabbatar da hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aikin a kan lokaci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta bayyana kisan CSP Baba Ali, DPO na Rano, a matsayin wani mummunan al'amari da ya girgiza jami'an tsaro da al'umma baki ɗaya.

Rundunar ta ce wannan kisa ba wai kawai hari ne ga jami’in ba, har ma barazana ce ga kokarin kare rayuka da dukiyoyin jama’a da 'yan sanda ke yi kullum.

Baba Ali
An kama mutane 41 kan kisan DPO a Kano. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da rundunar ta yi ne a cikin wani sako da SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce rundunar ta fara bincike mai zurfi cikin gaggawa dangane da kisan gillan da aka yi wa dan sandan.

An cafke wadanda ake zargi da kisan DPO

Bayan faruwar lamarin, rundunar ‘yan sanda ta tura jami’anta na musamman domin gudanar da bincike mai zurfi, wanda ya kai ga kama wasu daga cikin mutanen da ake zargi da hannu a kisan.

A cewar SP Kiyawa, binciken ya kai ga cafke mutum 41 da ake zargi da hannu a cikin lamarin, ciki har da wanda ake zargi ya jagoranci kisan.

Rundunar ta bayyana cewa tana aiki tuƙuru don tabbatar da cewa babu wani wanda ya tsira daga hukunci, kuma za a kamo sauran da ke da hannu a lamarin.

Kwamishina ya yi alkawarin hukunta masu laifi

CP Ibrahim Bakori ya bayyana cewa rundunar ba za ta yarda da irin wannan ta'asa ba, kuma za ta tabbatar da an gurfanar da duk wanda aka samu da laifi.

Kwamishinan ya kuma jaddada kudirin rundunar na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.

Ya yaba da goyon bayan jama’a da suka nuna da kuma hadin kai a yayin da rundunar ke gudanar da bincike, yana mai rokon su da su kwantar da hankali kuma su ci gaba da ba da hadin kai.

An karrama marigayi CSP Baba Ali a Kano

Rundunar ta bayyana cewa za ta ci gaba da girmama sunan CSP Baba Ali bisa sadaukarwa da jarumtar da ya nuna wajen gudanar da aikinsa.

Haka kuma ta yaba da kokarin sauran jami’ai da ke fuskantar haduran rayuwa a kowace rana domin kare al’umma.

Kano CP
'Yan sandan Kano sun nemi karin hadin kan al'umma. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Rundunar ta sha alwashin ci gaba da aiki tare da jama’a wajen samar da tsaro da zaman lafiya a jihar Kano.

An cafke bokan da ake nema ido rufe a Legas

A wani rahoton, kun ji cewa jami'an shige da ficen Najeriya sun cafke bokan da ake zargi da garkuwa da yarinya a Enugu.

Hukumar shige da ficen Najeriya da tabbatar da cewa da cafke shi ne a jihar Legas a lokacin da yake kokarin arcewa daga Najeriya.

Rundunar 'yan sanda ta sanar da cewa tana neman mutumin ruwa a jallo bayan da ta kai farmaki gidan da yake tsafi a jihar Enugu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. [email protected]

OSZAR »