Sojoji, 'Yan Sanda sama da 30 aka Damke Suna Sayar da Makamai ga 'Yan Ta'adda
- Rundunar sojojin ta kama jami’an tsaro bisa zargin safarar makaman gwamnati ga ’yan bindiga a Arewa maso Gabas
- An gano N135m a asusun wani dan sanda da ake zargi da safarar makamai, wanda ke nuna kazamar riba da suke samu
- Duk da haka, ana samun nasara yayin da sojoji suka cafke masu kai wa ’yan ta’adda kayan aiki da leken asiri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Dakarun Operation Hadin Kai (OPHK) sun kama sojoji 18 da ‘yan sanda 15 da ake zargi da laifin sayar da makamai ga ’yan bindiga a yankin Arewa maso Gabas.
Babban jami’in tsare-tsare na OPHK, Manjo Ademola Owolana, ne ya bayyana hakan yayin bayani ga manema labarai a kan ayyukan Rundunar Hadin Gwiwa daga 2024 zuwa 2025 a Maiduguri.

Asali: Facebook
Leadership News ta wallafa cewa Manjo Owolana ya ce an samu nasarori a yaki da safarar makamai a karkashin Operation Snowball da aka kaddamar a watan Agustan 2024 domin dakile safarar makamai a yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Ta'addanci: Ana yaki da safarar makamai
Daily Trust ta ruwaito Manjo Owolana ya bayyana cewa an kaddamar da yaki da safarar makamai a jihohi 11 ciki har da Bauchi, Benue, Borno, da Ebonyi.
Sauran jihohin da ake wannan aiki sun hada da Enugu, Legas, Filato, Kaduna, Ribas, Taraba da babban birnin tarayya Abuja. Ya ce:
“Ya zuwa yanzu, an kama sojoji 18, ‘yan sanda 15 da kuma fararen hula takwas ciki har da wani basarake.”
Dalilin wasu na sayar da makaman gwamnati
Ya ce binciken farko ya nuna cewa matsin lamba daga al’ummomi, musamman inda ake samun rikice-rikice na tilasta wa jami’an tsaro su rika sayar masu da makamai. Ya kara da cewa:
"Yadda ake samun riba mai yawa daga safarar makamai na daga cikin dalilan da ke kara karfafa wannan aiki.”
Manjo Owolana ya bayyana cewa wani Sajo Ameh Raphael, jami’in ajiyar makamai na rundunar Garrison ta Divisionta 7, na cikin harkar tun 2018.
Sai kuma Sajo Seidi Adamu na, wanda ya fara harkar tun 2022, kowannensu yana da kudi har Naira miliyan 45 da miliyan 34 a asusun bankinsu.

Asali: Facebook
Ya kuma bayyana cewa bincike ya gano cewa Naira miliyan 135 ta ratsa ta asusun wani dan sanda mai suna Sufeto Enoch Ngwa, wanda aka kama bisa zargin safarar makamai.
Manjo Owolana ya kafa da cewa dole ne a rika daukar tsauraran matakan da hukunci a kan duk wanda aka kama da laifin sayar da makamai ga yan ta'adda.
A bangare guda, rundunar ta bayyana damuwa kan yawaitar shan miyagun kwayoyi da sauran abubuwan maye da ke kara wa ‘yan ta’adda karfin kai hare-hare.
Manjo Owolana ya ce daga Janairun 2025 zuwa yanzu, an kama masu leken asiri da mika kayan aiki ga yan ta'addan sama da 186 a jihohin da ake aikin.
'Yan kasashen waje na horar da 'yan ta'adda
A wani labarin, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa wasu 'yan ƙasashen waje na baiwa kungiyoyin Boko Haram da ISWAP horo a kan dabarun yaki.
Daga cikin abubuwan da ake koyar dasu har da amfani da fasahohin zamani kamar jirage marasa matuka da kuma ƙera abubuwan fashewa da suke amfani da su a kan bayin Allah.
Kwamandan Operation Hadin Kai, Laftanar Janar Abdulsalam Abubakar, ya bayyana cewa an kama wasu 'yan Pakistan hudu da ake zargi da safarar makamai ga 'yan ta'adda.
Asali: Legit.ng