Tinubu Ya Yi Murnar Cika Shekara 2 da Raba Mukamai 61 a Manyan Makarantu

Tinubu Ya Yi Murnar Cika Shekara 2 da Raba Mukamai 61 a Manyan Makarantu

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana karin nade-nade a majalisun gudanarwa na jami’o’i, kwalejojin ilimi da kuma kwalejojin fasaha na tarayya
  • Nadin ya shafi jami’o’i da cibiyoyin ilimi da dama a fadin Najeriya, kuma ya ƙunshi mutane daga jihohi daban-daban na Arewa da Kudu
  • Nadin mukaman na zuwa ne yayin da fadar shugaban kasa ta fara shirye shiryen murnar cika shekara biyu a kan mulkin Najeriya da Bola Tinubu ya yi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin sababbin mambobi a majalisun gudanarwa na jami’o’i, kwalejojin ilimi da kuma kwalejojin fasaha.

Wannan na daga cikin yunkurin da gwamnati ke yi na farfado da ingancin shugabanci da gudanarwa a cibiyoyin ilimi domin dorewar ci gaban su.

Bola Tinubu
Tinubu ya nada mukamai 61 a manyan makarantun tarayya. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Ma'aikatar yada labarai ne ta fitar da sanarwar nade-naden a sakon da ta wallafa a shafinta na X a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Jerin wadanda aka nada a manyan makarantu

1. Jami’o’in tarayya

  • Jami’ar Kimiya da Fasahar Jiragen Sama ta Afirka, Abuja – Hon. Chidi Nwogu (Imo)
  • Jami’ar Jos – Dr. Folashade Mulikat Kareem (Kwara)
  • Jami’ar Fasaha ta Ikot-Abasi – Dipe Olusina Adeniyi (Lagos)
  • Jami’ar Fasaha ta Babura – Akanimo Umoh (Akwa Ibom)
  • Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi – Mr. Babatunde Usman Jinadu (Lagos)
  • Jami’ar Tarayya, Dutse – Chijioke Paul Okeifufe (Enugu)
  • Jami’ar Tarayya, Kashere – Hon. Babatunde Olokun (Ogun), Hon. Isah Ambaka (Nasarawa)
  • Jami’ar Tarayya, Wukari – Dr. Olusegun Ategbole (Ondo)
  • Jami’ar Tarayya, Gashua – Hon. Isa Song (Adamawa), Hon. Bernard Miko (Rivers)
  • Jami’ar Kimiyyar Lafiya ta Ila-Orangun – Mr. Muyideen Balogun (Ogun)
  • Jami’ar Noma ta Zuru – Hon. Mayegun Yomi (Lagos)
  • Jami’ar Tarayya, Gusau – Hon. Abbas Braimah (Edo)
  • Jami’ar Tarayya, Lafia – Dr. Adebimpe Adebajo (Ondo)
  • Cibiyar Koyar da Harshen Larabci ta Najeriya, Borno – Hon. Bawa Bwari (Niger)
  • Jami’ar Kimiyyar Lafiya ta Katsina – Hon. Bello Bagudu (Kebbi), Hon. Nasarawa Mani (Katsina)

2. Kwalejojin fasaha na tarayya

  • Kwalejin Fasaha ta Isuochi, Abia – Hon. Shehu Kagara (Kaduna)
  • Kwalejin Fasaha ta Oko, Anambra – Dr. Francis Ogbise (Bayelsa)
  • Kwalejin Fasaha ta Monguno, Borno – Hon. Almajiri Geidam (Yobe)
  • Kwalejin Fasaha ta Orogun, Delta – Rahila Ilegbodu (Taraba)
  • Cibiyar Fasahar Gini ta Kasa, Uromi – Hon. Shehu Lambu (Kano)
  • Kwalejin Fasaha ta Kaltungo, Gombe – Hon. Yusuf Bello Mai Adua (Sokoto)
  • Kwalejin Fasaha ta Hussaini Adamu, Kazaure – Saleh Mohammed (Jigawa)
  • Kwalejin Fasaha ta Daura, Katsina – Hon. Adekola Aliu (Osun)
  • Kwalejin Fasaha ta Offa, Kwara – Waidi Olajire Ayinla (Osun)
  • Kwalejin Fasaha ta N’yak, Filato – Hon. Hashimu Abdullahi (Sokoto)
  • Kwalejin Fasaha ta Bali, Taraba – Hon. Abdullahi Abubakar (Bauchi)

3. Kwalejojin ilimi na tarayya

  • Kwalejin Ilimi ta Gwoza, Borno – Ibrahim Abba Geidam (Yobe)
  • Kwalejin Ilimi ta Pankshin, Filato – Mohammed Nura (Kebbi)
  • Kwalejin Ilimi (Fasaha) ta Isu, Ebonyi – Hon. Abdulkadir Usman Global (Kaduna)
  • Kwalejin Ilimi (Fasaha) ta Ekiadolor, Edo – Hon. Usman Balkore (Sokoto)
  • Kwalejin Ilimi ta Odugbo, Benue – Hon. Goodluck Opiah (Imo)
  • Kwalejin Ilimi ta Omoku, Ribas – Hon. Bassey Etim (Akwa Ibom), Hon. Chris Eta (Cross River), Hon. Shuaib Yahaya (Katsina)
  • Kwalejin Ilimi (Na Musamman) ta Oyo – Hon. Sani M. Anka (Zamfara)
  • Kwalejin Ilimi (Fasaha) ta Keana, Nasarawa – Hon. Yusuf Dikko (Jigawa)
  • Kwalejin Ilimi ta Ilawe, Ekiti – Hon. Deacon Taiye (Kwara)
  • Kwalejin Ilimi (Fasaha) ta Asaba, Delta – Hon. Isa Lawal Doro (Katsina)

Tinubu
Tinubu ya cike guraben da aka samu a majalisun gudanarwar manyan makarantun tarayya. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

A bisa jerin da aka bayar, adadin mutanen da Shugaba Bola Tinubu ya nada a manyan makaratu 36 sun kai 61.

Tinubu zai kaddamar da ayyuka a jihohi

A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya isa jihar Legas domin kaddamar da wasu ayyuka na musamman.

A ranar 31 ga Mayu Bola Tinubu zai kaddamar da ayyukan da ake gani za su kawo cigaba sosai musamman a harkokin sufuri.

Baya ga jihar Legas, shugaban kasar zai kaddamar da wasu ayyukan a jihar Kano da wani jihar Katsina ta yanar gizo.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. [email protected]

OSZAR »