An Sallami Kansilolin Ganduje, Gwamnatin Abba Ta Fara Biyansu Hakkokinsu
- Gwamnatin Kano ta fara biyan sama da N16bn ga tsofaffin kansilolin APC, shugabannin kananan hukumomi da masu rike da mukaman siyasa
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya kaddamar da fara biyansu hakkokinsu, inda ya zargi gwamnatin Abdullahi Ganduje da watsi da bukatun shugabannin
- Ya kara da cewa gwamnati ta dauki matakin ne domin tabbatar da gaskiya da adalci, yayin da wasu Kansiloli suka fara karbar kudinsu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnatin jihar Kano ta fara biyan bashin fiye da N16n na hakkokin sallama ga tsofaffin kansilolin jam’iyyar APC da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta hana kudinsu.
Wadanda za su amfana sun hada da kansilolin da suka yi wa’adinsu daga shekarar 2014 zuwa 2024, tare da masu rike da mukaman siyasa na yanzu a cikin kananan hukumomi 44 na jihar.

Asali: Facebook
Wannan bayani na kunshe ne a cikin sanarwar da kwamishinan labarai na jihar Kano, Kwamred Ibrahim A Waiya ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Gwamnan Kano ya biya tsofaffin kansiloli
A cikin jerin sakonnin da hadimin gwamna, Ibrahim Adam, ya wallafa a shafinsa na Facebook, an bayyana yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da fara biyan kudin a gidan gwamnati ranar Laraba.
A jawabinsa, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ce biyan hakkokin sallama ga tsofaffin kansilolin APC ba wata alfarma ba ce, illa dai hakkin da ya kamata a biya su.

Asali: Facebook
Da yake bayyana godiya bisa gudummawar da suka bayar wajen hidimtawa jihar Kano, Gwamna Abba ya ce ya dauki wannan mataki ne bisa gaskiya da adalci.
A cewarsa:
"Wannan lokaci ba wani bikin al’ada ba ne kawai; yana wakiltar jajircewarmu wajen mutunta kima, adalci da rikon amana a harkokin gwamnati."
Yadda aka fara biyan tsofaffin kansilolin Kano
Gwamna Abba ya ce lokacin da aka gabatar da batun biyan hakkokin tsofaffin kansiloli a gaban majalisar zartaswa ta jihar, dukan 'yan majalisar sun amince.
Ya ce bai dace a rike hakkokin jama'a ba, musamman bayan sun yi wa al’umma aiki da gaskiya da rikon amana.
Gwamnan ya ce kansiloli daga mazabu 484 da ke kananan hukumomi 44 na jihar, wadanda suka kammala wa’adinsu a lokuta daban-daban, ne gwamnatin APC ta hana su kudinsu.
Wadanda biyan ya shafa sun hada da tsofaffin kansiloli, mataimakan shugabannin kananan hukumomi, shugabannin kananan hukumomi, da masu ba da shawara na musamman.
Gwamnatin Kano ta yi sababbin nadi
A baya, mun wallafa cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya amince da nadin Malam Haladu Mohammed a matsayin Mai Ba da Shawara ta Musamman kan Inganta Ilimi.
Gwamnati ta ce an kirkiri wannan sabon mukami ne domin karfafa ayyukan da gwamnati ke yi na farfado da harkar ilimi, wanda ya yi daidai da manufar gwamnatin Abba Gida-Gida
A cikin sanarwar da Darakta Janar na yada labaran gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, a ce nadin Malam Haladu yana daga cikin tsarin gwamnati na aiki da matasa.
Asali: Legit.ng