Duk da Ya Haɗa Kai da Su Atiku, Tinubu Ya Aika Saƙon Taya Murna ga Ministan Buhari

Duk da Ya Haɗa Kai da Su Atiku, Tinubu Ya Aika Saƙon Taya Murna ga Ministan Buhari

  • Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya jingine siyasa, ya aika sakon taya murnar cika shekaru 60 ga tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi
  • Tinubu ya tuna da irin gudummuwar da Amaechi ya bayar tun daga matakin jihar Ribas zuwa tarayya, ya yi masa addu'a da fatan alheri
  • Rotimi Amaechi na cikin waɗanda ke shirin haɗa ƙawance domin 'yan adawa su kifar da gwamnatin Shugaba Tinubu a zaɓen 2027

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

State House, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon ministan sufuri kuma tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Chibuike Amaechi, murnar cika shekara 60 a duniya.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar mai dauke da sa hannun Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru.

Rotimi Amaechi da Shugaba Tinubu.
Tinubu ya taya tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, murnar cika shekara 60 Hoto: @FMINONigeria
Asali: Twitter

A sanarwar wacce ma'aikatar yaɗa labarai da wayar da kan jama'a ta wallafa shafin X, Shugaban ya taya Amaechi murna tare da yaba masa bisa hidimar da ya yi wa ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Shugaba Tinubu ya yabawa Rotimi Amaechi

Shugaban kasa Tinubu ya bayyana Amaechi a matsayin ɗan siyasa na kwarai wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa ga ci gaban jihar Rivers da Najeriya gaba ɗaya.

Bola Tinubu ya jaddada cewa Rotimi Amaechi ya taka muhimmiyar rawa a tarihin siyasar Najeriya, inda ya riƙe kujerar shugaban majalisar dokokin jihar Rivers.

Daga nan kuma ya shugabanci jihar a matsayin gwamna har sau biyu, kafin daga bisani ya shugabanci Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF).

Bayan sauka daga kujerar gwamna, Amaechi ya ci gaba da hidimta wa kasa a matsayin ministan sufuri na tarayya a karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari daga 2015 zuwa 2023.

A wannan matsayi, ya jagoranci wasu muhimman ayyuka kamar farfado da layin dogo da bunkasa zirga-zirgar jiragen kasa a sassa daban-daban na kasar nan.

Rotimi Amaechi.
Gwamnatin tarayya ta taya Amaechi murnar ƙarin shekara Hoto: Rotimi Amaechi
Asali: Facebook

Tinubu ya yi wa Amaechi fatan alheri

Shugaba Tinubu ya yi addu’ar, "Allah ya kara wa Rotimi Amaechi lafiya, nisan kwana da hikima, tare da fatan alheri a dukkan harkokinsa na rayuwa da siyasa."

Sanarwar ta kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta yaba da irin jajircewa da sadaukarwar da Amaechi ya nuna wajen ganin Najeriya ta samu ci gaba mai dorewa tun daga matakin jiha har zuwa na kasa.

A ranar Talata, 27 ga watan Mayu, 2025, Amaechi ya cika shekaru 60 a duniya kuma manyan mutane daga sassan daban-daban sun yi masa fatan alheri.

2027: Amaechi ya shiga haɗakar yaƙar APC

A wani rahoton, kun ji cewa haɗakar ƴan adawa da AtikuAbubakar ke jagoranta ta ɗora wa tsohon gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi aikin tsara abin da ya kamata a yi kafin 2027.

Amaechi, wanda ya riƙe kujerar ministan sufuri a gwamnatin Muhammadu Buhari, da tsohon gwamnan Kuros Ribas, Liyel Imoke, su za su jagoranci nazarin matakan da haɗakar adawa za ta ɗauka.

An dora wa tsofaffin gwamnonin biyu alhakin duba yiwuwar a kafa sabuwar jam’iyya ko kuma su hade da wata jam’iyya domin yakar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: [email protected] 07032379262

OSZAR »