An Kama Ɗan Tsohon Shugaban PDP da Laifi Dumu Dumu, Kotu Ta Ɗaure Shi Shekaru 14

An Kama Ɗan Tsohon Shugaban PDP da Laifi Dumu Dumu, Kotu Ta Ɗaure Shi Shekaru 14

  • Kotun laifuffuka ta musamman da ke zama a Legas ta kama ɗan tsohon shugaban PDP na ƙasa da laifin zambar kuɗi N2.2bn na tallafin fetur
  • A zaman yau Talata, kotun ta yanke wa ɗan tsohon shugaban PDP, Mamman Ali hukuncin ɗaurin shekaru 14 a gidan gyaran hali
  • EFCC ta gurfanar da shi tare da wani Christian Taylor bisa zargin haɗa baki da karɓar kudin tallafin mai daga gwamnatin tarayya ta hanyar ƙarya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Wata kotun laifuffuka ta musamman da ke Ikeja, jihar Legas, ta ɗaure Mamman Ali, ɗan tsohon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Ahmadu Ali, a gidan yari na tsawon shekaru 14.

Kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 14 a gidan gyaran hali ne bisa samunsa da laifin zambar Naira biliyan 2.2 daga cikin kudin tallafin man fetur.

Mamman Ali.
Kotu ta ɗaure ɗan tsohon shugaban PDP kan laifin zambar kudin tallafin mai N2.2bn Hoto: @Nairametrics
Asali: Twitter

Rahoton The Cable ya nuna cewa kotun ta kuma yanke wa Christian Taylor, wani ɗan kasuwar mai, hukuncin zaman gidan yari na shekaru 14 tare da Mamman Ali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

EFCC ta gurfanar da ɗan tsohon shugaban PDP

Hukumar EFCC ce ta gurfanar da su a kotu bisa tuhume-tuhume guda 49, wanda ya ƙunshi haɗa baki domin karɓar kudi ta hanyar yaudara, jabun takardu da amfani da takardun ƙarya.

Waɗannan laifuffuka dai sun ci karo da dokar Advance Fee Fraud Act na 2006 da kuma dokar laifuka ta jihar Legas ta 2011.

EFCC ta tuhume su da karɓar Naira biliyan 1.48 daga gwamnatin tarayya da sunan kudin tallafin mai ne ga kamfaninsu, Nasaman Oil Services Ltd, domin shigo da lita 20,492,982.50 na fetur.

Sai dai duka waɗannan bayanai da suka miƙa ga gwamnati na kamfaninsu ƙarya ne, kamar yadda kotu ta tabbatar a hukuncin da ta yanke.

Yadda zaman shari'ar ta kaya a kotun

Mai shari'a Adeniyi Onigbanjo ya fara sauraron karar, amma daga bisani ya ajiye ta, daga nan aka ɗora wa mai shari'a Mojisola Dada alhakin ci gaba da sauraron karar a kotun.

Bayan haka EFCC ta sake gurfanar da su a gaban kotu a bisa tuhume-tuhume 57 da aka gyara, kuma dukkan su sun musanta laifin, rahoton Sahara Reporters.

A yayin shari’ar, lauyan EFCC, Seiduh Atteh, ya gabatar da shaidu da kuma takardu waɗanda kotu ta karɓa a matsayin hujjoji.

Kotu.
Kotu ta umarci a ƙwace duka kuɗin da ke asusun ajiyar waɗanda ake zargi masu alaƙa da laifin Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Kotu ta ɗaure waɗanda ake zargi shekaru 14

Da take yanke hukunci a ranar Talata, Mai shari'a Dada ta ce EFCC ta gabatar da hujjoji masu ƙarfi, kuma ta gamsu laifin da suka aikata sun cutar da gwamnatin tarayya.

Kotun ta yanke wa kowane daga cikin waɗanda ake zargi, Mamman Ali da Christian Taylor, hukuncin shekaru 14, sannan ta bayar da umarnin kwace duka dukiyoyinsu da asusun ajiyar kudi da ke da alaƙa da laifin.

Haka kuma, alkalin ta bayar da sammacin kama wasu mutane biyu da ake nema ruwa a jallo, Oluwaseun Ogunbambo da Olabisi Abdul Afeez, waɗanda suka tsere.

Kotu ta yi zama kan shari'ar Hadi Sirika

A wani labarin, kun ji cewa babbar kotun tarayya ta amince da wasu takardu a matsayin hujjoji a shari’ar tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika.

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ce ke gurfanar da Sirika tare da ’yarsa Fatima Sirika da surukinsa Jalal Sule Hamma.

EFCC ta bayyana cewa tana gurfanar da su ne bisa tuhume-tuhume guda shida da suka shafi almundahanar kudi N2.7bn.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: [email protected] 07032379262

OSZAR »