Yadda Abacha Ya Zama Silar Mutuwar Yar'adua, Abiola, Ya Yi Kokarin Kashe Ni - Obasanjo

Yadda Abacha Ya Zama Silar Mutuwar Yar'adua, Abiola, Ya Yi Kokarin Kashe Ni - Obasanjo

  • Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana yadda Janar Sani Abacha ya kitsa kashe shi tare da MKO Abiola da Shehu Yar’Adua
  • Obasanjo ya ce Abacha ya yi alkawarin cewa su ukun ba za su fito daga gidan yari da rai ba, kuma ya yi nasara kan Abiola da Yar'Adua
  • Tsohon shugaban ya ce ya tsira daga makircin Abacha a lokacin ne kawai saboda rahamar Allah, ba wai saboda ƙarfinsa ko kwarewarsa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Imo - Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana yadda ya tsira daga mummunan shirin da tsohon shugaban mulkin soja, Janar Sani Abacha, ya tsara domin hallaka shi.

Obasanjo ya bayyana cewa bayan kama shi tare da Janar Shehu Musa Yar’Adua da dan kasuwa kuma wanda ya lashe zaben ranar 12 ga Yunin 1993, Chief MKO Abiola, Abacha ya kitsa wani makirci na kawar da su daga doron kasa.

Olusegun Obasanjo ya tuno da yadda Janar Abacha ya hallaka su Yar'Adua, Abiola don ya yi mulki na har abada
Marigayi Janar Sani Abacha | Olusegun Obasanjo. Hoto: @Oolusegun_obj
Asali: Twitter

Obasanjo ya tuno makircin da Abacha ya kulla masu

Tsohon shugaban ya bayyana hakan ne a Ogbor Uvuru da ke Aboh Mbaise a jihar Imo, yayin bude cocin zamani na Assemblies of God da aka rada mata suna “The Noah’s Ark”, inji rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Obasanjo ya ce Abacha ya sha alwashin cewa su ukun ba za su fita daga gidan yari da rai ba, domin ya samu damar ci gaba da mulki har abada.

A cewarsa tsohon shugaban kasar:

“Lokacin da aka kama ni, na fara tunanin ko kuskure aka yi. Amma daga baya na gane cewa mutumin da ya kama ni ya riga ya yanke shawarar cewa dole sai an hallaka mu idan har zai cigaba da mulki na har abada.
“Na shiga cikin rudani a farko domin ban aikata wani laifi ba. Amma daga bisani na koma ga addu’a, har ma da irin addu’ar da Stifan ya yi. Na ce, ko da gangan suke yi, ko ma ba da gangan ba, Allah ka gafarta musu.”

"Allah ya kare ni da ikonsa" - Obasanjo

Jaridar The Sun ta rahoto Obasanjo ya kara da cewa:

“Na mika lamura na ga Allah. Mutumin da ya kama mu ya shaida cewa mu uku ba za mu fito daga kurkuku da rai ba; cewa MKO Abiola ba zai fito da rai ba, Shehu Yar’Adua ba zai fito da rai ba, Obasanjo ma ba zai fito da rai ba.”
“Biyu daga cikinmu da aka kitsa kashe su,, ba su fito ba. Amma ni na fito da rai na ba don saboda karfi na ba, sai domin wata babbar ni’ima ta Allah.”
Obasanjo ya ce Allah ne ya tsare shi, da tuntuni Abacha ya hallaka shi
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo. Hoto: @Oolusegun_obj
Asali: Getty Images

Yayin da yake jaddada cewa ya rayu ne bisa ga hukuncin Ubangiji, Obasanjo ya ce:

“Idan akwai wani da zai iya cewa ya ci gajiyar alherin Allah, to ni ne. Na shaida cewa Allah yana so na sosai, domin ya kare ni fiye da tunanin mai tunani.”

'Yadda Abacha ya kashe Abiola da Yar'adua'

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa Janar Sani Abacha, ne ke da alhakin kisan Janar Shehu Musa Yar’Adua, da Chief MKO Abiola.

Obasanjo ya ce Abacha ya yi shirin hallaka su uku ne ta hanyar allurar guba, amma Allah ya tsare shi daga wannan mummunan makirci da aka kitsa masa.

Ya kara da cewa, an killace shi a wani gida da ke Legas na tsawon watanni uku, kafin daga bisani a mayar da shi kurkukun Jos inda aka kai shi Yola bayan samu ziyara daga manyan kasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

OSZAR »