Ranar Yara: Tinubu Ya Kaddamar da Shirin Yaki da Cutar da Yara a Najeriya
- Shugaba Bola Tinubu ya mika sakon taya murna ga yaran Najeriya a Ranar Yara ta 2025 tare da jaddada ƙudurinsa na inganta rayuwar su
- Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kuduri aniyar kawar da cin zarafi da danniya ga yara, tare da kafa tsarin kariya mai ƙarfi ga kowane yaro
- Shugaban ya ƙaddamar da yaƙi da cin zarafin yara don karfafa juna wajen kare yara daga cin zarafi da cutarwa da kuma inganta lafiyarsu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa yara sune ginshikin makomar Najeriya.
Bola Tinubu ya bayyana haka ne wani sako na musamman da ya fitar a ranar Talata, 27 ga Mayu, 2025 domin bikin ranar yara.

Asali: Twitter
Legit ta tattaro bayanan da Bola Tinubu ya yi ne a cikin wani sako da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki tuƙuru don ganin an kare haƙƙin yara, an basu ingantacciyar rayuwa da kuma tabbatar da cewa kowanne yaro ya samu ilimi da walwala.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa taken bana na ranar yara ya dace da abin da ake bukata yanzu, domin ya nuna aniyar gwamnati wajen gina al’umma mai adalci da ba yara kariya.
Bola Tinubu zai inganta dokokin kariyar yara
Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa ta fara duba dokar haƙƙin yara ta 2003 da kuma dokar hana cin zarafin mutane ta 2015 domin faɗaɗa kariya da inganta yadda ake aiwatar da su.
Ya bayyana cewa ana amfani da Dokar Cybercrime don kare yara daga cin zarafi a kafafen sadarwa, musamman yadda ake yawaita cin mutuncin yara a dandalin intanet.
Ya ce dukkan jihohi 36 sun rungumi dokar kare haƙƙin yara, amma doka kaɗai ba za ta wadatar ba, sai iyaye, malamai, shugabannin addini da al’umma sun tashi tsaye wajen kare yara.
Tsare-tsaren Tinubu don taimakon yara
A cewar Tinubu, an kafa sababbin tsare-tsare kamar CPIMS domin bin diddigin duk wani rahoto na cin zarafin yaro a kan lokaci.
Ya ce an inganta ayyukan ma’aikatar harkokin mata don tabbatar da kula da yara a matakin ƙasa da ƙananan hukumomi, ciki har da wayar da kai da horar da masu kare yara.
Shugaban ya bayyana cewa gwamnati ta ƙaddamar da wani tsarin NGAC don kula da yaran da ba su da damar rayuwa tare da iyayensu.

Asali: Facebook
Tinubu zai tabbatar da yara suna koshi
Tinubu ya ce don ƙarfafa matsayi da amincin yara a cikin al’umma, ya ƙaddamar da wani shiri domin karfafa gwiwar jama’a su rika bayar da rahoton duk wani cin zarafin yara.
Ya ce gwamnati na aiwatar da tsarin ciyar da yara a makarantu da shirin Nutrition 774 domin tabbatar da cewa babu yaron da ke fama da yunwa a Najeriya.
Shugaba Tinubu ya ƙare da cewa:
“Yara ku na da muhimmanci. Kada wani ya cutar da ku ko ya hana ku furta damuwarku. Idan wani ya cutar da ku, ku yi magana – za a saurare ku kuma a kare ku.”
Legit ta tattauna da malamin makaranta
Wani malamin makaranta a jihar Gombe, Hamza Adamu Abdullahi ya zantawa Legit cewa yana da kyau a farfado da murnar ranar yara kamar yadda ake a baya.
Malam Hamza ya ce:
"A shekarun bayan ana bikin ranar yara a filin wasan Pantami, amma yanzu abin ya ja baya sosai.
"Ni malamin makaranta ne amma babu abin da muka shirya domin murnar wannar rana mai cike da tarihi a rayuwar yara."
An nemi Tinubu ya shiga lamarin Hamdiyya
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyoyn fararen hula sama da 30 sun yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu ya shiga lamarin Hamdiyya Sidi Sharif.
Kungiyoyin sun ce bai kamata a tsare matashiyar ba bisa ka'ida ba saboda rikicin da ta ke da gwamnatin Sokoto.
A makon da ya wuce aka samu Hamdiyya Sidi a jihar Zamfara bayan lauyanta, Abba Hikima ya sanar da cewa ta yi batan dabo a Sokoto.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng