Bayan Ƴan Daba Sun Kashe DPO a Kano, An Sake Hallaka Ɗan Sanda da Mutane 3 a Benue
- Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da cewa 'yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kashe jami’inta da mutane uku a Benue
- Mazauna yankin sun ce an kai hare-hare a kauyuka hudu, inda fiye da mutane 30 suka mutu, sannan wasu bakwai suka jikkata
- Fargaba ta mamaye jama’a, inda suka fara tserewa daga kauyukansu yayin da rundunar ‘yan sanda ta tsananta bincike a kan lamarin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Benue - Rundunar ‘yan sanda ta jihar Benue ta tabbatar da kisan wani jami’inta tare da wasu mutane uku a karamar hukumar Gwer ta Yamma da ke jihar.
An rahoto cewa wasu Fulani Makiyaya dauke da miyagun makamai ne suka farmaki karamar hukumar Gwer, inda suka kashe dan sandan da mutane uku.

Asali: Twitter
An kashe dan sanda a Gwer, Benue
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Sewuese Anene, ta bayyana hakan ga manema labarai a Makurdi a ranar Litinin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
SP Sewuese Anene ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a kauyen Aondona da ke karamar hukumar Gwer ta Yamma.
Ta bayyana cewa jami’in ‘yan sandan ya rasa ransa ne yayin da yake kokarin kare al’ummar kauyen daga harin 'yan bindigar.
SP Anene ta ce:
“Rundunar 'yan sanda ta hanzarta kai dauki a kauyen Aondona yayin da ta samu kiran gaggawa kan bullar 'yan bindiga. Mun samu gawarwaki uku, kuma bincike yana ci gaba.
"A wani hari na daban da ya faru ‘yan sa’o’i kafin wannan, wani jami’in ‘yan sanda ya mutu yayin da yake kare wani ƙauye a cikin Gwer West.”
An kashe sama da mutane 30 a Benue
Sai dai mazauna yankin sun bayyana cewa harin bai tsaya a kauyen Aondona kawai ba, domin an kai harin a kauyuka hudu a yankin.
Mazauna yankin sun kara da cewa fiye da mutane 30 ne suka mutu a hare-haren, yayin da wasu bakwai suka jikkata, sannan aka sace mutane biyu.
Sun ce 'yan bindiga sun tsananta hare-hare a yankunan ne tun daga ranar Asabar da yamma, inda aka fara kai hari a kauyen Aondona, sai kuma aka ci gaba da farmakin wasu kauyuka a ranar Litinin.
Wasu da suka tsira daga hare-haren sun ce an kashe fiye da mutane 15 a kauyen Aondona, an kashe mutane bakwai a kauyen Ahume, inji rahoton Punch.
A kauyen Tyolaha kuwa, an ce an kashe mutum biyar, yayin da aka kashe mutane shida a kauyen Orbiam, sannan aka sace wasu mutum biyu.

Asali: Original
Mutane sun fara tserewa daga gidajensu
Harin da aka kai ya jefa al’ummar yankin cikin halin fargaba da tashin hankali, inda mafi yawan mazauna kauyukan suka tsere daga gidajensu.
Al’ummar Mablim da ke karamar hukumar Gwer ta Gabas, wanda ke makwabtaka da Aondona, suma sun bar gidajensu, sun tsere zuwa garin Taraku domin neman mafaka.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar ‘yan sanda ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin harin da kuma gano wadanda suka aikata wannan mummunan ta’asa.
An kashe DPO a jihar Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu matasa sun kai hari ofishin ‘yan sanda a Rano, Kano, bayan mutuwar wani da aka kama bisa zargin amfani da miyagun ƙwayoyi.
An rahoto cewa matasan sun hallaka DPO na Rano bayan sun ji masa munana raunuka, sannan sun kona motoci 12 ciki har da guda biyu na sintiri.
Rundunar ‘yan sanda ta kama mutum 27 da ake zargi, yayin da kwamishina ya umurci a gudanar da bincike domin gano musabbabin rikicin da aka yi.
Asali: Legit.ng