A Karon Farko, Shugaba Tinubu Ya Taka Wa Wike Birki a Harkokin Gudanarwa a Abuja
- Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya sa baki kan batun bashin harajin kasa da hukumar gudanarwar Abuja ta ke bin masu kadarori 4,794
- Bola Tinubu ya dakatar da garƙame wurare da jami'an FCTA suka fara yau Litinin, ya bai wa masu kadarorin wa'adin kwanaki 14 su biya bashi da tara
- Wannan dai na zuwa ne bayan FCTA ta fara rufe duk wani wuri da ake bi haraji akalla na shekara 10 a manyan unguwannin Abuja
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya taka wa ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike birki kan kwace filayen da ya fara yi yau Litinin.
Shugaban ƙasar ya bai wa duka masu kadarorin da lamarin ya shafa wa'adin kwanaki 14 su tabbatar da sun biyan bashin da ake binsu sannan su sabunta takardunsu.

Asali: Twitter
Daraktan kula da harkokin filaye na FCTA, Mr. Chijioke Nwankwoeze, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannunsa da aka wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Ya ce:
“A ranar 26 ga Mayu, 2025, muka fara aiwatar da matakin tilasta biyan harajin fili kan kadarori 4,794 saboda gazawa wajen biyan harajin da ya kai tsakanin shekaru 10 zuwa 43.”
Shugaba Tinubu ya sa baki kan matakin FCTA
Ya ce kadarorin da lamarin ya shafa sun hada da na hukumomin gwamnati, kamfanoni masu zaman kansu, da kuma na ɗaiɗaikun mutane.
“Amma sakamakon Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya sa baki, an bai wa duk masu irin wadannan kadarori wa’adin makonni biyu su biya bashin harajin da ake binsu da tara.," in ji shi.

Asali: Facebook
Tarar da kowane mai kadara daga cikin waɗanda aka ambata a baya zai biya bisa tsarin unguwanni:
- Central Area: ₦5,000,000 na tara da yawan bashin haraji
- Maitama, Asokoro, Wuse II, Guzape: ₦3,000,000 na tara + bashin da ake binka
- Wuse I, Garki I, Garki II: ₦2,000,000 na tara + bashin harajin
Wike ya gargaɗi masu sayen filaye a Abuja
Haka kuma, wadanda suka sayi kadarori daga wasu amma ba su yi rajistar saye ba ta hanyar samun amincewar minista da rajistar takardun mallaka, an bukaci su yi hakan cikin kwanaki 14.
Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya kuma shinfida wa’adin kwanaki 14 ga duk masu kadarori a Abuja domin su biya kuɗin haƙƙin mallaka (R-of-O) da shaidar mallaka (C-of-O) ko ya soke takardunsu.
A ƙarshe, Ministan ya ja kunnen masu kadarori da su rika biyan kuɗaɗen da suka rataya a wuyansu domin gwamnatin tarayya ta ci gaba da aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa.
Lamarin Wike a Abuja
Tun bayan da Nyesom Wike ya zama Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), yake fuskantar suka daga al’umma, musamman mazauna Abuja da ‘yan kasuwa.
Daya daga cikin abubuwan da suka janyo masa suka shi ne yadda ya fara aiwatar da matakan tilasta biyan haraji da kuma kwace kadarori ba tare da la'akari da halin da jama'a ke ciki ba.
Wasu na ganin Wike yana tafiyar da FCT kamar yadda ya ke gudanar da Gwamnatin Jihar Ribas, wato da karfi da matsin lamba.
Zargin da ake yiwa Wike
An zargi Wike da rashin tuntubar al'umma kafin daukar wasu muhimman matakai, musamman kan harajin filaye da mallakar kadara.
Har ila yau, matakin da ya dauka na fara rufe gidaje da ofisoshi ya haifar da zaman dar-dar a tsakanin masu kadarori, inda wasu ke ganin hakan zalunci ne da rashin tausayi.
Hakan ya sanya ‘yan adawa da kungiyoyin fararen hula suka fara kiran Gwamnatin Tarayya da ta sa baki.
A karshe, sai ga shi Shugaba Tinubu ya dakatar da matakin Wike, ya bada wa’adin kwanaki 14 kafin a aiwatar da rufe wuraren.
Wannan na nuni da cewa akwai rashin daidaito tsakanin manufofin gwamnatin tarayya da irin tsarin shugabanci da Wike ke kokarin aiwatarwa a Abuja.
Gwamnatin Tinubi ta fara biyan bashi ga ma'aikata
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta fara biyan bashin ƙarin albashi na ₦35,000 ga ma'aikata.
Gwamnatin ta yi wannan ƙarin albashi ne domin rage wa ma'aikatan raɗaɗin ƙuncin rayuwar da suka shiga bayan cire tallafin man fetur.
Watanni bayan gwamnati ta yi alƙawarin ƙarin, a yanzu an fara tura wa ma'aikata kudin kamar yadda wata sanarwa daga ofishin Akanta Janar ta tabbatar.
Asali: Legit.ng