Ma'aikatan Wike Sun Dura Hedikwatar PDP, Sun Garkame Ofishin Jam'iyyar da Kwado
- Jami’an FCTA sun rufe hedikwatar PDP da ke Wuse, Abuja, da misalin karfe 2:05 na ranar Litinin, bisa umarnin gwamnatin tarayya
- An ba ma’aikatan da ke aiki a hedikwatar damar fitar da motoci da kayansu, kafin a rurfe wurin, lamarin da ya janyo cece-kuce
- Ma'aikatar FCTA karkashin Nyesom Wike ta ce za ta rufe dukkanin filaye 4,794 da ba a biya wa harajin fili ba tsawon shekaru 10 zuwa 43
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Da misalin karfe 2:05 na ranar Litinin ne jami’an hukumar birnin tarayya (FCTA) sun rufe hedikwatar jam’iyyar PDP da ke unguwar Wuse a Abuja.
Rahotanni sun ce jami’an FCTA sun iso wurin ne suka bukaci ganawa da masu kula da ginin, amma kafin masu tsaron su tuntubi shugabannin, aka garkame harabar gaba daya.

Asali: Twitter
An garkame hedikwatar PDP a Abuja
Lamarin ya janyo cece-kuce daga ma’aikata, inda aka bude kofar na dan lokaci domin su fitar da motoci da kayayyakinsu, sannan aka sake kulle wurin, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
A makon da ya gabata, FCTA ta sanar da shirin karbe kadarorin da suka kai 4,794, da aka soke lasisinsu saboda kin biyan harajin fili har na tsawon shekara 10 zuwa 43.
Jami’an FCTA da suka aiwatar da umarnin sun hada da hadimin ministan Abuja, Lere Olayinka, daraktan kula da filaye, Chijioke Nwankwoeze, da daraktan hukumar kula da gine-gine, Mukhtar Galadima.
Sun bayyana cewa gundumomi da abin ya shafa sun hada da Central Area, Garki I da II, Wuse I da II, Asokoro, Maitama da Guzape, kuma daga ranar Litinin, gwamnati ta fara karbe ikon wadannan kadarori.
Za a rufe wuraren da ba su biya haraji ba
Punch ta rahoto cewa jagororin sun ce za a aiwatar da wannan matakin ne kan duk wani mai kadara ba tare da la’akari da matsayinsa ba, domin bin doka da tsarin kasa.
Mukhtar Galadima ya ce, za a tabbatar an garkame duk filaye ko kadarorin da aka soke mallakarsu, har zuwa lokacin da gwamnati za ta yanke hukunci kan makomar su.
Da aka tambaye shi kan karar gwamnati da wasu ke ikirarin kaiwa kotu, Chijioke Nwankwoeze ya ce babu wani hukuncin kotu da ke hana aiwatar da wannan mataki.

Asali: Facebook
Gwamnati za ta zama mai mallakin kadarori
Ya kara da cewa an fara tattara bayanai kan wadanda suka biya haraji da wadanda ba su biya ba daga shekara daya zuwa 10, kuma an basu kwanaki 21 su cika ka'idojin.
A karshe, ya tuna cewa tun ranar 18 ga Maris, 2025 aka sanar da soke filaye 4,794 daga cikin jimillar 8,375 da ba a biya haraji ba tsawon shekara 1 zuwa 43.
FCTA za ta kasance mamallakin dukkanin kadarorin da aka kwace daga yau Litinin, 26 ga Mayu, 2025 ta hanyar amfani da hukumomin gwamnati.
FCTA ta garkame ofishin FIRS da banki
A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar FCTA ta rufe ofishin hukumar FIRS, bankin Access da wani gidan mai a Abuja saboda kin biyan harajin fili.
Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaron FIRS sun yi kokarin hana jami’an FCTA aiwatar da aikin, amma daga baya suka yarda aka kulle ofishin.
An ce wannan matakin yana cikin kokarin tilastawa masu kadarori biyan harajin filayen da suka ki biya na tsawon shekaru 10 zuwa 20.
Asali: Legit.ng