ASUU Ta Taso da Muhimman Batutuwa 9, Ta Yi Barazanar Rufe Jami'o'in Najeriya

ASUU Ta Taso da Muhimman Batutuwa 9, Ta Yi Barazanar Rufe Jami'o'in Najeriya

  • Ƙungiyar ASUU ta bukaci gwamnatin tarayya ta cika alkawurran da ta ɗaukar mata kan yarjajeniyar 2009 ko ta tsunduma yajin aiki
  • Malaman jami'o'in sun bayyana cewa babu wata alama da ke nuna gwamnati na da niyyar cika waɗannan alƙawura har yanzu
  • Shugaban ASUU na ƙasa ya bukaci gwamnatin Najeriya ta shirya taro kan ilimi domin tattauna muhimman batutuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya, (ASUU) ta sake tado da batun alƙawurran da aka ɗaukar mata a yarjejeniyar 2009.

Ƙungiyar ASUU ta roki Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta cika yarjejeniyar 2009 da aka kulla tsakaninsu ko kuma ta fuskanci sabon yajin aiki a faɗin ƙasa.

Kungiyar ASUU.
Kungiyar ASUU ta yi barazanar shiga yajin aiki kan yarjejeniyar 2009 Hoto: @ASUU
Asali: Twitter

Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudanar a Abuja ranar Juma’a, kamar yadda Punch ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Kungiyar ASUU ta taso da batutuwa 9

Farfesa Piwuna ya jaddada cewa akwai batutuwa tara masu muhimmanci da har yanzu gwamnati ta kasa magance su, ciki har da:

  • Sake duba yarjejeniyar 2009 da aka dakatar tun 2017.
  • Batun biyan albashin da aka riƙe masu saboda yajin aikin 2022.
  • Alawus-alawus na malaman jami'o'i da aka rike sakamakon amfani da tsarin IPPIS.

Shugaban ASUU ya kuma ce akwai kudin farfaɗo da jami’o’i da hakkokin malamai da gwamnati ta yi alkawarin biya duk sun makale, har yanzu ba a biya ba.

Duk da an yi alƙawarin ware ₦150bn ga jami'o'i da gyara wasu alawus kafin 2026, shugaban ASUU ya ce babu wanda aka yi har yanzu.

Chris Piwuna ya bayyana cewa mambobin ASUU a wasu jami’o’in jihohi irin su Jami’ar Kogi da ta Legas na fuskantar, tsangwama, hana albashi da barazanar kora.

Wannan, a cewarsa, yana karya gwiwar malamai kuma yana haifar da rashin kwanciyar hankali a fannin ilimi, rahoton Vanguard.

ASUU ta koka kan sa siyasa wajen zaɓen VCs

Shugaban ASUU ya koka da yadda siyasa ke shiga tsarin nada shugabannin jami’o’i, yana cewa hakan ya keta ikon cin gashin kai na jami’o’in.

Ya bada misali da abin da ya faru wajen zaɓen shugabanni a jami’ar Nnamdi Azikiwe da ta Abuja.

Bola Tinubu da shugaban ASUU.
ASUU ta bukaci a shirya taron ilimi na ƙasa Hoto: @Nentawe1
Asali: Twitter

Ƙungiyar ASUU ta bukaci a shirya taron kasa kan makomar ilimi wanda zai tattauna kan kudin shigar jami’o’i, ƴancin gudanarwa da walwalar malamai.

“Ilimi shi ne ginshiƙin ci gaba. Ba za a iya gina ƙasa ba sai an farfaɗo da ilimi,” inji Piwuna.

Ya jaddada cewa ASUU za ta ci gaba da gwagwarmaya domin gyaran jami’o’in Najeriya tare da gayyatar ‘yan ƙasa masu kishi da ƙungiyoyi na duniya su mara musu baya.

ASUU ta fara yajin aiki a Sakkwato

A wani labarin, kun ji cewa kungiyar malamai watau ASUU ta jami’ar jihar Sokoto ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani saboda rashin biya mata buƙatunta.

Ƙungiyar ta ce ta yanke shawarar fara yajin aikin ne sakamakon gazawar jami'ar da gwamnatin Sakkwato wajen magance matsalolin malamai.

Ta ce za ta tabbatar da cewa mambobinta na bin umarnin yajin aikin yadda ya kamata, wanda zai dakile duk wasu harkokin ilimi a jami'ar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: [email protected] 07032379262

OSZAR »