Tura Ta kai Bango: Shugaban Sojoji Ya ba da Sabon Umarni kan Yaki da 'Yan Ta'adda
- Babban hafsan Sojojin ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya buƙaci a fatattaki ƴan ta'addan da suka takurawa ƙasar nan
- Laftanar Janar Olufemi ya umurci dakarun sojoji n kasada su nuna rashin tausayi wajen fatattakar miyagun ƴan ta'adda
- Babban hafsan sojojin ya nuna cewa ba za su lamunci abin da ya kira ƙoƙarin ƴan ta'adda na tarwatsa rayuwar ƴan Najeriya ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Babban hafsan sojojin ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya ba da sabon umarni ga dakarunsa kan yaƙi da ƴan ta'adda.
Laftanar Janar Olufemi Oluyede ya umurci kwamandoji da sojoji su fatattaki ƴan ta’adda gaba ɗaya daga ƙasar nan ba tare da nuna wani tausayi ba.

Asali: Facebook
Oluyede ya bayar da wannan umarni ne yayin da yake rufe taron shekara-shekara na COAS a Maiduguri, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Shugaban sojoji ya umarci a murkushe ƴan ta'adda
A wajen taron manyan janar-janar na rundunar sojojin ƙasa sun shafe kwanaki uku suna tattaunawa kan hanyoyin tabbatar da zaman lafiya da tsaron ƙasa, shafin Zagazola Makama ya tabbatar da zancen.
"Ku saurara mata da maza, babu wata jayayya game da ƙudirinmu na kawar da duk wani mai hana zaman lafiya gaba ɗaya."
“Saboda haka, ina kira ga kowane jami’i da soja kan kada su bari ko guda daga cikin ƴan ta’adda da masu aikata laifi su tsira, sai sun mutu ko an kama su."
"Su (ƴan ta’adda) na ƙoƙarin tarwatsa rayuwarmu da rushe al’ummar da kakanninmu suka gina. Ba za mu bari hakan ta faru ba."
- Laftanar Janar Olufemi Oluyede
Sojoji za su kawo sababbin dabaru
Babban hafsan sojojin ya jaddada cewa dole ne a aiwatar da duk wata dabara ko shawara da aka cimma a taron domin cimma burin da aka sa a gaba tun daga farko.

Asali: Facebook
“A sakamakon muhawara da muka yi, a cikin makonni masu zuwa za mu ƙara haɗa wasu kayan yaƙi da za su ƙarfafa rundunoninmu wajen ayyukansu."
“Duk da haka, ya kamata mu fahimci cewa ƙarfafa sojojin Najeriya ba wai kawai yana cikin makaman da muke dasu a fagen daga bane, amma yana cikin ƙwazon sojojin da ke amfani da su."
“Saboda haka, ya rataya a wuyan kowa da ke nan ya zama abin koyi na shugabanci, ya horar da sojoji, ya kuma shiryar da matasa zuwa hanya madaidaiciya."
"A yau, muna fuskantar maƙiya da ke barazana ga ginshikin al’adunmu da ɗabi’unmu na ƙasa."
- Laftanar Janar Olufemi Oluyede
Kayan aiki ya kamata a ba su
Abubakar Ishaq ya shaidawa Legit Hausa ba umarci sojoji suka fi buƙata ba, kayan aiki na zamani ya kamata a ba su don murƙushe ƴan ta'adda.
Ya bayyana cewa sojoji na buƙatar makamai masu kyau don kawo ƙarshen ƴan ta'adda.
"Dakarun sojojin Najeriga sun fi buƙatar samun kayan aiki don tunkarar ƴan ta'adda. Muna da haziƙan jami'an tsaro amma rashin makamai na daƙile su."
- Abubakar Ishaq
Dakarun sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara mayaƙan ƙungiyar ta'addanci ta Boko Haram.
Dakarun sojojin sun hallaka ƴan ta'adda 16 bayan sun yi yunƙurin kai hari a garin Damboa na jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Bayan ragargazar ƴan ta'addan, dakarun sojojin sun kuma ƙwato tarin makamai a hannun tsagerun masu tayar da ƙayar bayan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng