Dangote zai Yi Hadakar Kafa Kamfanin Shinkafa a Neja, Matasa za Su Samu Ayyuka

Dangote zai Yi Hadakar Kafa Kamfanin Shinkafa a Neja, Matasa za Su Samu Ayyuka

  • Kamfanin Dangote da Gwamnatin Neja sun kulla yarjejeniya don gina kamfanin sarrafa shinkafa mai iya sarrafa ton 500,000
  • An ware filin noma mai girman hekta 50 don aikin, tare da biyan diyyar Naira miliyan 36 ga mazauna yankin
  • Aikin zai ƙarfafa shirin wadatar da abinci da samar da ayyukan yi ga matasa a jihar Neja da ma Najeriya baki daya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Niger - Gwamnatin Neja da haɗin gwiwar Dangote sun sanar da shirin gina kamfanin sarrafa shinkafa a jihar, wanda zai zamo ɗaya daga cikin manyan kamfanoni a Najeriya.

Kamfanin Dangote ne ya bayyana hakan a wani taron da aka yi a jihar, inda ya ce an kammala shirye-shiryen fara aikin a tsakanin ƙananan hukumomin Wushishi da Bida.

Dangote
Dangote zai yi hada kai da Neja wajen kafa kamfanin shinkafa. Hoto: Dangote Industries
Asali: Getty Images

Rahoton Punch ya nuna cewa aikin zai samu goyon baya daga gwamnatin Neja da kamfanin Dangote.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

An ware hekta 50 don yin kamfanin shinkafa

Rahoto ya nuna cewa gwamnati ta ware filin noma mai girman hekta 50 a Wushishi da Bida don gina kamfanin.

An ruwaito cewa an biya diyyar Naira miliyan 36 ga gidaje 37 da abin ya shafa, domin tabbatar da adalci da gaskiya a tsarin.

Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa an bi dukkan matakan doka wajen mallakar filin, kuma za a mika shi ga kamfanin Dangote domin fara aikin.

Aikin zai ƙarfafa noman shinkafa a Neja

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa kamfanin sarrafa shinkafar zai taimaka wajen bunkasa noman shinkafa a jihar, tare da samar da ayyukan yi ga matasa da kuma ƙarfafa tattali.

Kwaminshinan kasuwnci na jihar, Aminu Takuma ya ce aikin zai kuma haɗa da samar da gidajen gona na zamani, inda za a yi amfani da sababbin fasahohi wajen noman shinkafa.

Dangote zai taimaka wajen habaka tattali

Kamfanin Dangote ya bayyana cewa wannan aikin wani ɓangare ne na shirin kamfanin na zuba jari a fannin noma da sarrafa abinci a Najeriya.

Ya ce kamfanin zai ci gaba da haɗin gwiwa da gwamnatocin jihohi domin ƙarfafa tattalin arziki da kuma samar da abinci mai yawa ga 'yan Najeriya.

Gwamnatin Neja za ta tallafa wa aikin kamfanin

Aminu Takuma ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafa wa aikin ta hanyar samar da abubuwan more rayuwa kamar hanyoyi, wutar lantarki da kuma ruwa.

Gwamnatin Neja ta kuma yaba wa kamfanin Dangote bisa wannan gagarumin zuba jari da zai taimaka wajen ciyar da jihar gaba.

Umaru Bago
Gwamnatin Neja ta yaba wa Dangote kan kafa kamfanin shinkafa. Hoto: Balogi Ibrahim
Asali: Facebook

Dangote zai zuba jari a Taraba

A wani rahoton, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya yi alkawarin zubar jari a jihar Taraba da ke Arewa maso Gabas.

Alhaji Aliko Dangote ya yi alkawarin ne jim kaɗan bayan kammala taron tattalin arziki da aka yi a jihar Taraba.

Gwamnatin Taraba ta shirya taron ne domin jawo hankalin ƴan kasuwa a ciki da wajen Najeriya domin saka hannu wajen haɓaka tattalin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. [email protected]

OSZAR »