FCTA: Jam'iyyar PDP Ta Ƙara Shiga Garari, An Kwace Babbar Hedkwatarta Ta Ƙasa a Abuja

FCTA: Jam'iyyar PDP Ta Ƙara Shiga Garari, An Kwace Babbar Hedkwatarta Ta Ƙasa a Abuja

  • Hukumar gudanarwa ta Abuja watau FCTA ta ƙwace hedkwatar jam'iyyar PDP da wasu kadarori sama da 4,000
  • FCTA ta bayyana cewa daga ranar Litinin mai zuwa, 26 ga watan Mayu, 2025, za ta fara ƙwace kadarorin saboda kin biyan haraji
  • Daga cikin filayen da hukumar FCTA za ta ƙwace har da filin da aka gina Wadata Plaza, wurin da hedkwatar PDP ta ƙasa take a Abuja

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hukumar Gudanarwar Babban Birnin Tarayya (FCTA) ta bayyana cewa daga ranar Litinin, 26 ga Mayu, 2025, za ta fara kwace haƙƙin mallakar kadarori 4,794 a Abuja.

FCTA ta ce za ta ƙwace waɗannan kadarori ciki har da filin da sakatariyar PDP ta ƙasa take da gidaje saboda kin biyan haraji na tsawon lokaci, daga shekara 10 zuwa 43.

Abuja.
Hukumar FCTA ta tabbatar da ƙwace filaye sama da 4,000 saboda gaza biya harajin ƙasa na tsawon shekaru Hoto: @CelebritiesGist1
Asali: Twitter

Leadership ta ruwaito cewa FCTA ta ce kadarorin da abin ya shafa suna cikin manyan unguwannin Abuja kamar su Central Area, Garki I da II, Wuse I da II, Asokoro, Maitama da Guzape.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

FCTA za ta ƙwace gidaje da kadarori 4,793

Mai magana da yawun ministan Abuja, Lere Olayinka, daraktan kula da filaye, Chijioke Nwankwoeze da daraktan gine-gine na FCTA, Mukhtar Galadima ne suka sanar da hakan a wata hira da ƴan jarida yau Juma'a.

Sun tabbatar da cewa hukumar FCTA za ta fara ƙwace kadarorin daga ranar Litinin mai zuwa ba tare da la'akaro da waye mai su ba.

A cewarsu:

“Wannan mataki ya yi daidai da dokokin da suka shafi mallakar fili a Abuja. Za a kulle kadarorin da abin ya shafa kuma za a hana kowa shiga ciki.”

PDP na dab da rasa hedkwatarta a Abuja

Daga cikin kadarorin da za a karɓe har da filin Wadata Plaza, inda hedkwatar PDP ta ƙasa take, wanda tun watan Maris, 2025, aka soke haƙƙin mallakarsa saboda ƙin biyan haraji.

Daraktan Kula da Gina-gine, Mukhtar Galadima, ya kara da cewa gwamnati za ta yanke hukunci kan yadda za a sake amfani da wadannan filaye nan gaba.

Ya kuma tabbatar cewa kotu ba ta dakatar da shirinsu ba, don haka babu wata shari’a da ke hana hukumar FCTA ƙwace filayen da suka rasa ingancin takardunsu.

Wike.
Hukumar FCTA za ta fara ƙwace kadarori da suka kunshi filaye da gidaje a Abuja Hoto: @GovWike
Asali: Twitter

FCTA ta fara zaƙulo wasu abubuwan a Abuja

A nasa jawabin, darakta kulanl da filaye na FCTA, Nwankwoeze ya ce ana ci gaba da tattara bayanan masu kadarorin da suka gaza biyan harajin kasa na shekara 1 zuwa 10, su ma an ba su kwanaki 21 domin su biya.

Daga karshe, ya ce gwamnati za ta dauki matakin da ya dace da zarar an kammala tantance bayanan, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Hukumar FCTA ta lalata babura 601

A wani rahoton, kun ji cewa Hukumar DRTS ta FCTA ta lalata babura 601 da aka kama da laifin zirga-zirga a wuraren da aka haramta a Abuja.

Sakataren ma’aikatar sufuri ta FCTA, Elechi Chinedum, ya jagoranci jami’an gwamnati wajen ruƙurƙushe baburan wanda galibinsu na ƴan acaɓa ne.

Elechi Chinedum ya ce doka ce ta haramta hawa babura a wasu yankuna na Abuja, kuma akwai hukuncin da aka tanada ga masu kunnen ƙashi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: [email protected] 07032379262

OSZAR »