Cin Hanci: Yadda EFCC Ta Yi Amfani da Hadisin Manzon Allah domin Jan Hankalin Mutane

Cin Hanci: Yadda EFCC Ta Yi Amfani da Hadisin Manzon Allah domin Jan Hankalin Mutane

  • Hukumar EFCC ta ci gaba da fadakar da al'umma kan illar cin hanci da rashawa da kuma barnar da ake yiwa dukiyar kasa
  • A wata sanarwa a Facebook, EFCC ta ja hankali game da wadaka da dukiyar al'umma ta hanyar amfani da hadisin Manzon Allah (SAW)
  • Hadisin Sahih Muslim ya gargadi shugabanni da su guji boye ko satar dukiyar jama'a, yana cewa za su zo da ita a ranar lahira

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT , Abuja - Yayin da cin hanci ke kara ƙamari a Najeriya, hukumar yaki da cin hanci ta ci gaba da wayar da kan al'umma.

Hukumar ta EFCC ita ke yaki da cin hanci da karbar rashawa da kuma yiwa tattalin arziki ta'annati.

EFCC ta ja hankalin mutane kan cin hanci
Hukumar EFCC ta gargadi mutane kan cin hanci. Hoto: Economic and Financial Crimes Commission.
Asali: Facebook

Cin hanci: Salon EFCC na jan hankulan mutane

A cikin wata sanarwa a shafin Facebook a yau Juma'a, hukumar ta ja hankulan al'umma kan wadaka da dukiyar jama'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

A cikin sanarwar, hukumar ta yi amfani da hadisin Manzon Allah (SAW) domin tsoratar da mutane hakkin al'umma a lahira.

EFCC ta yi amfani da hadisin Sahih Muslim wanda ya yi gargadi kan almundahana da kuma abin da zai biyo baya.

Hadisin yana magana ne kan boyewa ko take hakkin al'umma da shugabanni ko wadanda aka naɗa shugabanci ke yi.

A cikin sanarwar, hukumar ta ce:

"Wadaka da dukiyar al'umma cin amana ne.
"Manzon Allah (SAW) ya ce: 'duk wanda aka naɗa shugabanci kan wani lamari kuma ya boye ko da allura ne, ya yi wadaka da dukiya.
"Haka zai zo da ita a ranar tashin lahira - Sahih Muslim 1933a."
EFCC ta yi gargadi kan cin hanci
EFCC ta ja hankulan mutane kan almundahana da cin hanci. Hoto: Economic and Financial Crimes Commission.
Asali: Facebook

Martanin 'yan Najeriya kan sakon EFCC

'Yan Najeriya da dama sun tofa albarkacin bakinsu game da wannan salo na hukumar a kokarin yaƙi da cin hanci a kasa.

Mafi yawan wadanda suka yi magana sun soki hukumar ne ganin yadda take cafke masu kananan karfi amma yan siyasa na fantamawa.

Abdullahi Mohammed:

"Ban da yan siyasar Najeriya, su ne kadai ba ku isa ku taba su ba."

Tpl Sunnex Blaq:

"Tsuntsunwarku yanzu ba ta da fiffike, ba ku yi komai kan Yahaya Bello da Tompolo ba."

Christopher Orji:

"EFCC kamar burodin Agege ne, an ajiye wa talakawa ne kawai."

Hot Point Media:

"Ina Gandollar? yana yawo kai tsaye babu fargaba a kasa, kawai tambaya na ke yi."

Alhassan Abdulrahman:

"Yan siyasa barayi nawa kuka kama a mulkin Buhari da na Tinubu, hakan na nufin babu dan siyasa da ya sace kudinmu?"

EFCC ta yi wa'azi da ayar Kur'ani

Mun ba ku labarin cewa hukumar EFCC ta yi amfani da darajar Juma’a a cikin watan Ramadan domin fadakar da jama'a kan yaki da cin hanci.

Hukumar ta ambaci wata aya daga Alkur’ani mai girma domin yin kashedi ga mutane game da wawure dukiyar haram.

Al’ummar Najeriya sun yi mamakin wannan sabon salo da EFCC ta dauka wajen fadakarwa game da cin amanar dukiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a [email protected].

OSZAR »