Tsautsayi: Matasa Sun Gamu da Ajalinsu a wajen Karbo Bashi a Kano
- Matasa biyu daga unguwar Gwammaja sun gamu da ajalinsu a lokacin da suke kokarin karbo bashi daga hannun wani matashi a Kano
- Hukumar kashe gobara ta Kano bayyana cewa lamarin ya afku ne a lokacin da mutumin da ake bi domin karbar kudin ya shiga wani rafi
- Mai magana da yawun hukumar, Saminu Yusuf Abdullahi ya ce matasan biyu sun makale a cikin ramin har lokacin da jami'ansu suka isa wurin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da rasuwar wasu matasa biyu bayan da suka fada rafi a gefen hanyar Ring Road, a gaban unguwar Dorayi Babba.
Mai magana da yawun hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ya bayyana cewa daraktan hukumar, Sani Anas, ya ce sun samu kiran gaggawa da misalin karfe 9:36 na safe kan batun.

Asali: Original
Daily Trust ta wallafa cewa wadanda lamarin ya rutsa da su sune Saifullahi Muhammad mai shekaru 27 da Halifa Abdullahi mai shekaru 29, dukkansu mazauna unguwar Gwammaja ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Abin da ya hallaka matasa 2 a Kano
Trust Radio ta ruwaito cewa matasan biyu suna bin wani daga kasuwar Kofar Ruwa ne domin karbar bashin da ake binsa, inda mutumin ya fada cikin rafi a lokacin da suke bibiyarsa.
Hukumar kashe gobara ta ce a kokarinsu na kamashi, matasan biyu su ma suka fada cikin ramin, inda suka makale har ta kai ga rasa rai.
A cewar Saminu Yusuf Abdullahi:
“Tawagar ceto daga hedikwatar hukumar ta isa wajen cikin gaggawa, inda suka fito da mutanen biyu daga cikin ramin magashiyyan. Daga nan aka garzaya da su asibitin kwararru na Murtala Muhammad, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsu.”

Asali: Facebook
An mika gawarwakin ga Sufeto Halifa Muhammad na ofishin ‘yan sanda na Kuntau a Kano domin ci gaba da bincike.
Kano: An yi aikin ceton masu hakar rijiya
A wani lamari daban, hukumar ta samu kiran gaggawa dangane da wasu ma’aikatan hakar rijiya biyu da suka makale a cikin rijiyar da suke aiki a cikinta a kauyen Danmaliki.
An bayyana cewa ma’aikatan sun makale ne sakamakon zafi da rashin iskar a rijiyar. Sai dai, tawagar ceto ta samu nasarar fitar da su da rai.
Hukumar ta ce:
“An ceto su cikin nasara, kuma suna cikin hayyacinsu. Daga bisani likitoci sun tabbatar da cewa suna cikin koshin lafiya.”
Hukumar kashe gobara ta shawarci jama'a da su rika yin taka-tsantsan a wuraren da ke da ruwa ko rijiyoyi, musamman a lokacin damuna mai kamawa.
Yan sandan Kano sun gwabza da yan ta'adda
A baya, mun wallafa cewa rundunar ’yan sandan jihar Kano ta tabbatar da ceto wata mata da aka yi garkuwa da ita daga garin Minjibir, inda aka kaita dajin Garki da ke jihar Jigawa.
Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an yi garkuwa da matar ne daga Minjibir, sannan aka tafi da ita zuwa cikin dajin Garki da ke jihar Jigawa.
Rundunar ’yan sandan ta Kano ta gode wa al’umma bisa hadin kai, tare da jan hankalin jama’a da su ci gaba da bayar da bayanai masu amfani domin ci gaba da yakar aikata laifuffuka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng