Ribadu Ya Fadi Dabarar da Suka Yi wajen Kashe 'Yan Ta'adda 13,500 a Shekara 2

Ribadu Ya Fadi Dabarar da Suka Yi wajen Kashe 'Yan Ta'adda 13,500 a Shekara 2

  • Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya ce sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda da masu laifi sama da 13,500
  • Ribadu ya bayyana cewa an samu nasarar ne sakamakon hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da kuma ƙarfafa leƙen asiri da aka yi
  • Ya ƙara da cewa mayakan Boko Haram da ISWAP da suka mika wuya da iyalansu sun kai sama da 124,000 tun bayan zuwan Bola Tinubu mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa dakarun Najeriya sun kashe 'yan ta'adda da wasu masu aikata laifuffuka akalla 13,543 a fadin kasar cikin shekara biyu da suka gabata.

Mai bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin tsaro (NSA), Mallam Nuhu Ribadu, ne ya bayyana hakan a wani taro na jam’iyyar APC da aka gudanar a Abuja.

Ribadu
Ribadu ya fadi nasarorin da aka samu kan tsaro karkashin Tinubu. Hoto: Nuhu Ribadu
Asali: Facebook

Punch ta rahoto cewa Ribadu ya ce nasarar ta samu ne bayan aiwatar da dabarun tsaro, hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da kuma jajircewa wajen dakile ‘yan ta’adda a sassan Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

'Yan Boko Haram da ISWAP sun mika wuya

Ribadu ya ce sojoji sun samu gagarumar nasara wajen fatattakar Boko Haram da ISWAP musamman a Arewa maso Gabas, inda mayaka 124,408 da iyalansu suka sallama.

Ya ce wadanda suka mika wuya yanzu haka suna cikin shirin sake fasalin tunani da sake haɗa su da al’umma domin hana su komawa ta’addanci.

Ribadu ya bayyana cewa an kwato da lalata harsasai guda 252,596 nau’uka daban-daban a kokari da ake na wanzar da zaman lafiya a fadin kasar.

Harin 'yan ta’adda na ci gaba da tayar da kura

Duk da wadannan nasarori, Ribadu ya ce akwai sauran aiki domin hare-haren 'yan ta’adda da na ‘yan bindiga da masu rajin ballewa na cigaba da tayar da hankula a wasu yankuna.

Ribadu ya ce lamarin Boko Haram da ya fara tun 2009 ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 350,000 tare da raba fiye da mutum miliyan 2 da muhallansu.

Rahoton Arise News ya nuna cewa ya ce harin da aka kai a baya-bayan nan a Plateau, Benue da Borno yana nuna bukatar ci gaba da sa ido da ƙara karfafa tsaro a wadannan yankuna.

Tinubu
Ribadu ya ce Tinubu na kokari kan tsaro. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Ribadu: 'Tinubu ya gaji matsalolin tsaro'

Ribadu ya ce gwamnatin Tinubu ta karfafa gwiwa wajen tunkarar matsalolin tsaro da ta gada, ciki har da Boko Haram, ‘yan bindiga a Arewa maso Yamma da Tsakiya, da 'yan a-ware a Kudu.

Ya ce haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro da saka jari a fannin leƙen asiri ne ke taimakawa wajen rage barazanar tsaro.

Legit ta tattauna da Sulaiman Adam

Wani mazaunin jihar Borno, Sulaiman Adam ya zantawa Legit cewa sun fi gamsuwa da matakan da gwamnatin Buhari ta dauka game da tsaro.

Sulaiman ya ce:

"Duk da cewa ana ikirarin tsaro ya inganta, amma maganar gaskiya koma baya muka gani mu kam.
"Boko Haram na shirin dawowa kai hare hare bayan an ci karfinsu a baya. Muna fatan za a kawo karshensu."

Sojoji sun kashe Boko Haram a Borno

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojin Najeriya sun kai wasu hare hare kan Boko Haram a Borno.

A wani farmaki da suka kai, sojojin Najeriya sun kashe Boko Haram shida suna kokarin satar kayan abinci.

Haka zalika, sojojin sun hallaka wani dan Boko Haram yana kokarin shiga dajin Sambisa da babur dauke a kayan hada bom.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. [email protected]

OSZAR »