Boko Haram Sun Hadu da Fushin Sojoji yayin da Suke Shirin Satar Abinci a Borno

Boko Haram Sun Hadu da Fushin Sojoji yayin da Suke Shirin Satar Abinci a Borno

  • Dakarun Operation Hadin Kai sun kashe mayakan Boko Haram da ISWAP guda bakwai a farmakin da suka kai a yankunan Rann da Damboa na jihar Borno
  • An kai farmakin ne bayan bayanan sirri game da yunƙurin ‘yan ta’addan na satar kayan abinci a motar da ta lalace a hanyar zuwa garin Gamboru–Ngala
  • A wani samame, dakarun sun yi kwanton-bauna a hanyar Maiduguri–Damboa, suka halaka wani dan ta’adda kuma suka kwato babura da kayan hada bam

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar hallaka wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne na kungiyoyin Boko Haram da ISWAP guda bakwai a cikin makon nan.

Lamarin ya auku ne a wasu yankuna biyu daban-daban na jihar Borno, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Boko Haram
Sojoji sun hallaka Boko Haram a Borno. Hoto: Zagazola Makama
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da mai sharhi kan tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Wannan samame na cikin jerin matakan kakkabe ‘yan ta’adda da dakarun Operation Hadin Kai ke ci gaba da gudanarwa domin hana su yawo da kai hare-hare a cikin al’umma.

Rahoton ya ce dakarun sun haɗu da mayakan ne a lokacin da suke yunƙurin kwasar kayan abinci daga wata mota da ta lalace a hanya kusa da Rann.

Sojoji sun kashe Boko Haram na shirin sata

Rahotanni sun nuna cewa an kai farmaki na farko ne ranar Laraba, inda dakarun bataliya ta 3 tare da haɗin gwiwar CJTF suka yi arangama da ‘yan ta’adda a hanyar Gamboru–Ngala.

Sojojin sun bude wuta, inda suka kashe ‘yan ta’adda shida tare da kwato bindigu AK-47 guda biyu da harsashi da dama.

Daya daga cikin manyan bindigogin na dauke da harsashi guda hudu, yayin da dayan ke dauke da guda shida.

Sojoji sun kashe dan Boko Haram a Borno

A wani farmaki na daban, dakarun FOB Molai sun yi kwanton bauna a kusa da Komala bayan samun bayanan sirri a hanyar Maiduguri–Damboa da ke karamar hukumar Damboa.

A nan ne sojojin suka kashe wani dan ta’adda daya da ke kan hanyarsa zuwa dajin Sambisa tare da kwato babura da kayan hada bom da ake zargin za a dasa su a hanya.

Janar Musa
Sojoji za su cigaba da kai farmaki kan 'yan ta'adda. Hoto: Defence Headquaters
Asali: Facebook

Sojoji na ci gaba da kakkabe Boko Haram

Wata majiya daga soji ta bayyana cewa waɗannan hare-haren sun kasance wani bangare na yunkurin sojojin Najeriya na kakkabe 'yan ta’adda daga wuraren da suke kai hare-hare.

An bayyana cewa matakin zai taimaka wajen hana ‘yan ta’adda motsi da yin munanan ta'asa a yankunan Najeriya.

Zamfara: 'Yan ta'adda na korar mutane a gidajensu

A wani rahoton, kun ji cewa hare haren 'yan bindiga a jihar Zamfara ya fara sanya mutane guduwa a gidajensu.

Rahotanni daga wasu yankunan Kaura Namoda a jihar Zamfara sun nuna cewa 'yan ta'adda sun zafafa kai hare hare a yankin.

Wani mazaunin karamar hukumar Kaura Namoda ya yi kira ga gwamnati kan kara daukan matakan da suka dace don magance matsalar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. [email protected]

OSZAR »