An Samu Sauki: Dangote Ya Fadi Gidajen Mai 6 da Za a Sayi Litar Fetur a kan N875

An Samu Sauki: Dangote Ya Fadi Gidajen Mai 6 da Za a Sayi Litar Fetur a kan N875

  • Matatar Dangote ta rage farashin man fetur daga ₦835 zuwa ₦825, domin taimakawa wajen daidaita farashi da wadatar mai a Najeriya
  • Kamfanin Dangote ya bayyana cewa akwai gidajen mai mallakin abokan huldarsa shida da suke sayar da fetur a farashin matatar da ke Legas
  • Ya shawarci 'yan Najeriya da su rika siyan man fetur daga waɗannan gidajen domin cin moriyar sabon farashin da mamatar ke bayar wa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Matatar Dangote ta sanar da sauke farashin man fetur daga ₦835 zuwa ₦825 a kan kowace lita ga masu sayen man kai tsaye daga wajenta.

Sabon farashin, wanda ya fara aiki tun a ranar 12 ga Mayu 2025, na zuwa a daidai lokacin da Najeriya ke ƙoƙarin daidaita wadatar man fetur da rage dogaro da shigo da shi daga waje.

Kamfanin Dangote ya fadi gidajen mai 6 da 'yan Najeriya za su sayi feturinsa a farashi mai rahusa
Alhaji Aliko Dangote | Ma'aikacin gidan mai na sayar da fetur. Hoto: Dangote Group|Getty Images
Asali: Getty Images

Dangote ya rage farashin fetur zuwa ₦825

Masana harkar mai sun ce wannan rangwame na iya haifar da sauƙin farashin sayarwa a gidajen mai a fadin ƙasar, kamar yadda rahoton Business Day ya nuna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Majiyoyi sun tabbatar da cewa matatar Dangote ta saukar da farashinta zuwa ₦825 a kan kowace lita, ta hanyar rage ₦10 ga abokan huldarta bayan sun kammala ɗaukar man.

Majiyoyin sun bayyana cewa ‘yan kasuwa a lokacin na biyan ₦835 ka kowace lita, amma suna karɓar ragin ₦10 daga matatar domin saukaka masu jigilar man zuwa sassan kasar.

Wannan sauyin farashi ya bai wa abokan huldar Dangote damar sayar da lita ɗaya a tsakanin ₦830 zuwa ₦835, wanda ke sa su fi dillalan da ke shigo da mai daga waje samun riba.

Gidajen man da ke sayar da fetur da araha

A safiyar Alhamis, 22 ga Mayun 2025, Dangote ya bayyana cewa an sabunta farashin man fetur a gidajen saida mai na abokan hulɗarsa shida, kuma farashin zai bambanta kadan daga yanki zuwa yanki.

A cikin sanarwar da kamfanin Dangote ya wallafa a shafinsa na X, an bayyana abokan huldar matatar da ke sayar da litar fetur a kan N875 zuwa 905:

  1. MRS Oil
  2. AP (Ardova)
  3. Heyden Petroleum
  4. Optima Energy
  5. Hyde Energy
  6. Tecno Oil

Farashin da ake sayar da feturin Dangote

Ga farashin da gidajen man ke sayar da fetur, kamar yadda matatar Dangote ke sayarwa:

Gidajen MaiJihar LegasKudu maso YammaArewa maso GabasArewa maso Yamma/TsakiyaKudu maso Kudu/Gabas
MRS ₦875₦885₦905₦895₦905
Ardova (AP) ₦875₦885₦905₦895₦905
Heyden ₦875₦885₦905₦895₦905
Optima Energy ₦875₦885₦905₦895₦905
Technoil ₦875₦885₦905₦895₦905
Hyde ₦875₦885₦905₦895₦905

Dangote ya bayyana cewa zai ci gaba da rage farashin man fetur domin saukaka wa 'yan Najeriya
Alhaji Aliko Dangote, shugaban rukunonin kamfanin Dangote. Hoto: Getty Images
Asali: Facebook

Dangote ya ba 'yan Najeriya shawara

Dangote ya shawarci 'yan Najeriya da su rika siyan man fetur daga waɗannan gidajen domin cin moriyar sabon farashin da aka kayyade.

Matatar Dangote ta kuma fitar da wata sanarwar jan kunne, inda ta nemi jama’a su rika ba da rahoto idan wani gidan mai bai bi sabon farashi ba.

Matatar ta ce man da suka tace yana da inganci, yana kuma taimakawa wajen kyautata aikin inji da kare muhalli, bisa kudirin kamfanin na samar da ingantaccen mai.

Dangote zai ci gaba da rage farashin fetur

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Matatar Dangote da ke Legas ta bayyana cewa za ta ci gaba da rage farashin fetur duk da ƙarin farashin danyen mai a kasuwannin duniya.

Kamfanin ya ce wannan mataki na nuna jajircewarsa wajen tallafa wa tattalin arzikin ƙasa da rage wa 'yan Najeriya radadin tsadar rayuwa.

Dangote ya kuma gode wa Shugaba Bola Tinubu bisa shirin sayar da danyen mai cikin Naira, wanda ya ba kamfanin damar saukaka farashin fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

OSZAR »