Kaduna: Uba Sani Ya Naɗa Sababbin Kwamishinoni bayan Sauyi a Ma'aikata

Kaduna: Uba Sani Ya Naɗa Sababbin Kwamishinoni bayan Sauyi a Ma'aikata

  • Mai girma Gwamna Uba Sani ya yi nadin sababbin kwamishinoni domin inganta shugabanci a jihar Kaduna
  • Uba Sani ya nada Farfesa Abubakar Sambo a matsayin Kwamishinan Ilimi, aka sauyawa Farfesa Sani Bello ma’aikata
  • Gwamnan ya ce yana sa ran sabbin kwamishinonin za su kawo sauyi a ma’aikatunsu tare da samar da hanyoyin magance matsalolin jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya yi nadin sababbin kwamishinoni a jihar Kaduna.

Gwamna Uba Sani ya nada Farfesa Abubakar Sani Sambo a matsayin sabon Kwamishinan Ilimi a jihar.

Uba Sani ya nada sababbin kwamishinoni
Uba Sani ya yi nade-naden kwamishinoni a jihar Kaduna. Hoto: Uba Sani.
Asali: Facebook

Uba Sani ya yi sauyin muƙami a ma'aikata

Hakan na cikin wata sanarwa da sakatarensa, Ibraheem Musa ya fitar wanda a Abdallah Yunus Abdallah ya wallafa a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Haka kuma, gwamnan ya mayar da tsohon Kwamishinan Ilimi, Farfesa Sani Bello (Mainan Zazzau) zuwa sabuwar Ma’aikatar Yada Labarai.

Barrista Gloria Ibrahim ita ce ta zama sabuwar Kwamishinar ci gaban matasa da aka nada bisa manufar sauya fasalin matasa.

Nadin kwamishinonin da sauya wurin aiki sun fara aiki nan take, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Tarihin Farfesa Abubakar Sani Sambo

Sabon Kwamishinan Ilimi kwararren malami ne kuma masani, wanda ya taba lashe kyaututtuka, an kuma ba shi lambar yabo ta OON a shekarar 2000 saboda gagarumin gudunmawarsa.

Farfesan makamashi ne wanda ya taba rike mukamin Shugaban jami’ar ATBU, Bauchi da kuma jami’ar Kaduna.

Ya kuma rike mukamin mataimakin shugaban jami’a (Bangaren Ilimi) a Usmanu Danfodiyo, Sokoto, daga 1990 zuwa 1994.

Daga 2005 zuwa 2012, ya jagoranci Hukumar Makamashi ta Najeriya (Energy Commission of Nigeria) a matsayin Darakta-Janar.

A shekarar 2011, an nada shi a matsayin mashawarci na musamman ga shugaban kasa kan harkokin makamashi.

Ya kasance mamba ko shugaba a kwamitoci da dama a Najeriya da matakin duniya, musamman kan makamashi da bincike.

Ya taba zama shugaban kwamitin haɗin gwiwa da Brazil kan makamashi a 2007 zuwa 2008 da mamba a wasu manyan kwamiti.

Uba Sani ya kawo sababbin jini a gwamnatinsa
Uba Sani ya nada sababbin kwamishinoni a Kaduna. Hoto: Uba Sani.
Asali: Twitter

Addu'o'in da Uba Sani ya yi ga kwamishinonin

Gwamna Uba Sani yana fatan Farfesa Sambo zai gyara bangaren ilimi domin cimma burin gwamnati na inganta tsarin karatu.

Gwamnan ya ce burinsa shi ne a gina makarantun zamani, horas da malamai, da kuma tabbatar da tsaro a cibiyoyin ilimi.

A bangaren matasa, gwamnan ya bukaci Barista Gloria ta kirkiri tsare-tsaren zamani don amfani da fasaha da basira wajen ciyar da matasa gaba.

Yayin da yake taya su murna, Gwamna Uba Sani ya roki Allah ya ba su jagora da kariya a sababbin aikace-aikensu.

Uba Sani ya magantu kan matsalar tsaro

Kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani na ya fadi abubuwan da ke kara rura wutar rashin tsaro.

Gwamna Uba Sani ya lissafo talauci da rashin aikin yi a matsayin silar matsalolin tsaron da ake fama da su.

Ya yi gargadi ga shugabannin Arewa da cewa dole a hada ƙarfi da karfe domin ceto yankin daga matsaloli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a [email protected].

OSZAR »