Koriya Ta Tunkaro Najeriya da Sababbin Bukatu 4, Karon Farko bayan Shekaru 15

Koriya Ta Tunkaro Najeriya da Sababbin Bukatu 4, Karon Farko bayan Shekaru 15

  • Cibiyar al’adun Koriya ta cika shekaru 15 da kafuwa a Najeriya, yanzu tana neman sabuwar huldar al’adu da kasar a wasu fannoni hudu
  • An gudanar da shirye-shirye sama da 650 tun kafuwar cibiyar, ciki har da karatun Hangeul, K-Pop, Taekwondo da gasar girki na Hansik
  • Cibiyar na fatan hada gwiwa da masana’antar Nollywood da ’yan Najeriya a harkar fim da adabi don zurfafa hulda tsakanin kasashen

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shekaru 15 bayan bude cibiyar al’adun Koriya a Najeriya, yanzu ta gabatar da bukatar kulla sababbin huldodin al’adu da Najeriya.

Kasar Koriya ta nemi Najeriya ta amince su kulla hulda a fannoni hudu, da suka hada da fim, adabi, ilimi da kuma abinci.

Cibiyar al'adun Koriya ta gabatar da bukatar hadin gwiwa da Najeriya kan fannonin fim, waka, abinci da ilimi
Kim Changki, daraktan cibiyar al’adun Koriya a Najeriya. Hoto: @KCCNigeria_/X
Asali: Twitter

Koriya na son hadin gwiwa da Najeriya

Tun daga ranar 24 ga Mayun 2010 da aka kafa cibiyar, tana aiki tukuru wajen gina alaka tsakanin Koriya da Najeriya ta hanyar al’adu, ilimi, hadin gwiwa da shirye-shiryen al’umma, inji rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Cibiyar ta kaddamar da shirye-shiryen koyon wakoki da rawa na Koriya (K-Pop), karatun harshen Koriya (Hangeul), atisayen Taekwondo da yawon shakatawa a cibiyar ga dalibai.

Ta kuma hada hakan da bukukuwan shekara-shekara irin su bikin baje kolin fina-finan Koriya, na na wakokin K-Pop da ma gasar girkin abincin Hansik da ake gudanarwa a Najeriya.

Ayyukan da cibiyar Koriya ta yi a Najeriya

Wadannan shirye-shirye na samun goyon baya ne daga hadin gwiwa da kungiyoyi a Najeriya da kasashen waje, ciki har da hukumomin Koriya da wakilan diflomasiyya.

Har ila yau, ana samun karin tasiri ta hanyar hadin gwiwa da masu sha’awar al’adun Koriya, da suka hada da tsofaffin daliban GKS, masu kirkira na Hallyu da ma wakilan jaridu.

Cibiyar ta karbi sama da mutane 300,000 cikin shekaru 15, da baƙi na musamman 16,000 a shekara, tare da gudanar da shirye-shirye sama da 650 a sassa daban-daban na kasar.

Yanzu da cibiyar ke tunkarar karin wasu shekaru a kasar, tana kokarin zurfafa huldar al’adu a sababbin fannonin fim, adabi da ilimi, don kara karfafa dangantaka da Najeriya.

Kasar Koriya na son kulla hulda da Najeriya a fim, waka, abinci da ilimi
Mambobin ƙungiyar The Billers Group Abuja sun kai ziyara zuwa cibiyar al’adun Koriya a Najeriya (KCCNigeria). Hoto: @KCCNigeria_/X
Asali: Twitter

Koriya ta fadi tasirin kulla hulda da Najeriya

Yujin Lee, manajan shirye-shiryen cibiyar, ta ce dalilan wannan sabon yunƙuri sun hada da martabar Nollywood a matsayin masana’antar fim ta uku mafi girma a duniya.

Ta kara da cewa wani dan Najeriya mai suna JJC Skillz ne ya samar da fim din da ake magana da Turanci da Koriya na farko, mai taken 'My Sunshine'.

Yujin Lee ta bayyana irin nasabar da ke tsakanin Najeriya da Koriya ta fannin adabi inda Wole Soyinka da Han Kang suka lashe kambunan karramawa ta Nobel Laureates a nahiyoyinsu.

A cewarta, cibiyar tana da burin yada al’adun Koriya zuwa jihohin Najeriya, ba wai a iya Legas, Abuja, Ibadan, Abeokuta da Fatakwal ba.

'Yan Koriya za su gina matatun mai a Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, karamin ministan albarkatun man fetur, Heineken Lokpobiri, ya ce Najeriya ta samu sahalewar wasu masu zuba jari daga Koriya ta Kudu.

Ya ce waɗannan masu zuba jarin sun nuna kwadayin gina matatun man fetur guda huɗu a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Ministan ya ƙara da cewa gwamnati ta riga ta tura musu gayyata tare da tabbatar da cikakken tallafi da sauƙaƙe musu hanyoyin gudanar da kasuwanci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

OSZAR »