Ana tsaka da Shari'arta da Gwamnati, an Nemi Hamdiyya an Rasa a Birnin Sokoto
- Majiyoyi sun ce ana neman Hamdiyya Sidi Shareef a Sokoto tun jiya da safe bayan ta fita siyan kayan abinci har yanzu ba a san inda take ba
- Daya daga cikin lauyoyinta, Abba Hikima ya tabbatar da hakan a rubutunsa na Facebook, yana cewa sun riga sun sanar da ‘yan sanda a Sokoto
- Hamdiyya na shari’a da gwamnatin jihar bisa sukar matsalar tsaro da fuskantar barazanar dauri saboda zargin cin mutuncin Gwamna Ahmad Aliyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Sokoto - Rahotanni sun tabbatar da cewa ana neman Hamdiyya Sidi Shareef bayan ta bata a birnin Sokoto da ke Arewacin Najeriya.
An ce Hamdiyya ta fita tun jiya da safe domin sayan kayen abinci, amma har zuwa yanzu da ake hada wannan rahoto babu labarin ta.

Asali: Facebook
Daya daga cikin lauyoyinta, Abba Hikima shi ya tabbatar da haka a yau Laraba 21 ga watan Mayun 2025 a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
An taso gwamnatin Sokoto kan lamarin Hamdiyya
Idan ba ku manta ba, matashiyar ce Gwamnatin Sokoto take Shari'a da ita kan rashin tsaro da take magana a kai wanda shi ne silar jefa ta a wannan matsala.
A baya, Hamdiyya Sidi ta bayyanawa duniya irin halin da talakawan Sokoto suke ciki na rashin tsaro wanda ya daidaita ƙauyukan jihar Sokoto.
Hakan ya jawo mata matsaloli a rayuwarta wanda ya sa aka kama ta tare da gurfanar da ita a gaban kotu.
Daga cikin zarge-zargen da ake yi mata akwai cin mutuncin Gwamna Ahmad Aliyu na jihar Sokoto da rashin mutunta hukumomi game da yadda ta yi kakamanta.
Sai dai mutane da dama sun caccaki gwamnan saboda matakin da ya dauka duk da abin da ta fadi gaskiya ne kan rashin tsaro da ya addabi mutane a jihar.

Asali: Facebook
Hamdiyya: Amnesty Int'l ta soki gwamnatin Sokoto
Har ila yau, Kungiyar Amnesty International ma ta zargi gwamnatin Sokoto da kokarin dakile gwagwarmaya a fadin jihar musamman kan matsalolin tsaro.
Kungiyar ta ce babu yadda za a yi kokarin rufewa mutane baki yayin da 'yan bindiga ke cin karensu babu babbaka a fadin jihar da yankin Arewa maso Yamma.
Abin da Abba Hikima ya ce game da Hamdiyya
Abba Hikima ya ce tuni suka sanar da rundunar yan sanda kan lamarin Hamdiyya domin daukar matakin da ya dace.
A cikin rubutunsa, Abba Hikima ya ce:
"Tun jiya da karfe 10:00 na safe ba a ga Hamdiyya ba.
"Ta fita siyan kayan abinci a cikin garin Sokoto har yanzu ba duriyar ta.
"Mun sanar da ‘yan sandan Sokoto tun tuni."
Wasu mutane sun yi martani game da rubutun Abba Hikima inda suke zargin gwamnatin jihar kan batan Hamdiyya.
Wasu ko sukar masu kula da ita suke yi saboda barin ta a Sokoto duk da hatsarin da ke tattare da ita.
Hamdiyya: Bulama Bukarti ya kalubalanci gwamnan Sokoto
A baya, kun ji cewa fitaccen lauya, Barista Bulama Bukarti ya soki gwamnatin Ahmed Aliyu a jihar Sokoto a kan cin zarafin Hamdiyya Sidi Shareef.
Ɗan gwagwarmayar ya ce babu wani kuskure ko laifi a cikin kalamanta na neman a tabbatar da tsaro wanda ya addabi al'ummar yankin gaba daya.
Bulama ya yi mamakin yadda gwamnan ke ganin mai dakinsa da yaransa da ke gidan gwamnati sun fi na jama'a daraja duk da cewa hakkinsa ne ya kula da lamuransu.
Asali: Legit.ng