'Ba 'Yan Bauchi ba ne,' Gwamna Ya Gano za a Yiwa Jiharsa Kwangen Daukan Aikin Sojoji
- Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana damuwarsa kan yadda aka saka wadanda ba 'yan asalin jihar ba daukar aikin sojojin sama
- Ya bayyana cewa musanya sunayen yan asalin Bauchi da wadanda ba 'yan jiha ba cin zarafi ne da kuma nuna wariya da kaya dokar kasa
- Sanata Abdul Ningi, mai wakiltar Bauchi ta tsakiya, ne ya mika wa majalisar dattawa koken gwamnan a zaman da aka yi ranar Talata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Bauchi – Majalisar Dattawa ta fara daukar mataki kan zargin da gwamnan Bauchi ya yi na cewa an dauki wasu da ba 'yan asalin jihar ba a matsayin yan Bauchi a aikin sojojin saman Najeriya.
Sanata Abdul Ningi mai wakiltar Bauchi ta tsakiya ne ya gabatar da koke daga Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, a zaman majalisar da ya gudana a ranar Talata.

Asali: Facebook
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa gwamnan ya ce daukar wadan da ba 'yan asalin Bauchi ba a matsayin'yan jihar ya saba da tsarin daukar ma’aikata kuma abin damuwa matuka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Gwamnan Bauchi ya fusata da daukar sojoji
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a cikin kokensa, Gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa saka ba 'yan asalin jihar a matsayin ‘yan asalin Bauchi nuna wariya ne ga jama'arsa.
Ya ce:
"Wannan koke ne domin jawo hankalin majalisar dattawa kan wani lamari mai matukar muhimmanci – wato saka ba 'yan asalin jihar Bauchi ba a matsayin ‘yan asalin jihar a shirin horar da sojojin saman Najeriya.”
"Ya zama dole, Shugaban Majalisa, a lura cewa an tauye jihar Bauchi matuka, an nuna mata wariya."

Asali: Facebook
Gwamna Bala Mohammed na ganin wannan babbar matsala ce da ke bukatar mahukunta su sanya ido, sannan a dauki matakin daina nuna wa jama'ar jiharsa wariya.
Majalisa za ta duba bukatar gwamnan Bauchi
Bayan karanta kokensa, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya mika batun ga kwamitocin da ke kula da kan harkokin sojin sama domin gudanar da cikakken bincike.
Ya ce:
“Za a tattauna wannan koke a matakin kwamitoci.”
Haka kuma, Akpabio ya umarci kwamitocin da su gudanar da bincike cikin gaggawa tare da dawo da rahoto ga zauren majalisa cikin kwanaki bakwai.
Ana sa ran za a bayyana mataki na gaba da za a dauka a kan batun bayan an samu rahoton da kwamitocin za su fitar bayan wa'adin da aka ba su.
Gwamnan Bauchi ya nada hakimai 168
A baya, kun samu labarin cewa gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya janyo ce-ce-ku-ce a fadin jihar bayan da ya amince da nade-naden sababbin hadimai na musamman guda 168.
Mai taimaka masa na musamman kan yada labarai, Mukhtar Gidado, ne ya fitar da sakon sabon nadin wani bangare ne na kokarin Gwamna Bala Mohammed na farfado da harkokin mulki.
Duk da cewa gwamnati na ganin wannan mataki a matsayin ci gaba, wasu daga cikin al’umma da masana harkokin siyasa na bayyana damuwa kan yawan wadanda aka nada.
Asali: Legit.ng