Rashin Tsaro: Sanata Ya Fallasa Makarkashiyar da Ake Kullawa Tinubu

Rashin Tsaro: Sanata Ya Fallasa Makarkashiyar da Ake Kullawa Tinubu

  • Sanata Sunday Karimi ya nuna damuwa a game da ƙaruwar matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a ƙasar nan
  • Sunday Karimi ya nunaakwai masu mugun nufi da ke ƙoƙarin ɓata nasarorin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta samu
  • 'Dan majalisar na jihar Kogi ya buƙaci hukumomin tsaro da su yi azama wajen gudanar da bincike domin gano tushen matsalar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban kwamitin ayyukan majalisar dattawa, Sanata Sunday Karimi, ya bayyana damuwa kan yadda matsalar rashin tsaro ke ƙaruwa a ƙasar nan.

Sanata Sunday Karimi ya ce ƙaruwar matsalar rashin tsaron na barazana ga kyakkyawan aikin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Sunday Karimi ya tabo batun rashin tsaro
Sunday Karimi ya ce ana kokarin bata Tinubu da rashin tsaro Hoto: Daniel Bwala, Senator Sunday Karimi
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta rahoto cewa Sunday Karimi ya ambato dawowar kashe-kashe da ke faruwa a sassa daban-daban na ƙasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Sanata Sunday Karimi ya koka da rashin tsaro

Sanatan ya nuna damuwa kan kashe-kashen musamman a jihohin Benue, Plateau, Kogi, hare-haren 'yan bindiga a Arewaci maso Yamma, da kuma sababbin hare-haren Boko Haram a Arewa maso Gabas.

Ya nuna cewa ya kamata a binciki waɗannan abubuwa cikin gaggawa, rahoton jsridar The Nation ya tabbatar.

“Yawaitar rashin tsaro ya bazu a faɗin ƙasa, a Arewa maso Gabas akwai dawowar Boko Haram. A wani lokaci komai ya lafa, amma yanzu sun fara dawowa."
“Duba sauran yankuna na ƙasar nan, sace mutane yana ƙaruwa sosai, ko a Kudu maso Yamma, Kudu maso Kudu, Kudu maso Gabas, haka abin ke faruwa a ko’ina."
"Kusan kullum sai an samu wani rahoton hare-haren ƴan bindiga a Arewa maso Yamma."
“Ina ganin wannan dawowar wani yunƙuri ne daga wasu ƙungiyoyi ko mutane masu mugun nufi da ke ƙoƙarin ɓata aikin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta gudanar a cikin shekaru biyu da suka gabata, musamman ganin yadda maganar zaɓen 2027 ke ta ƙarfi."

- Sanata Sunday Karimi

Sanata Sunday Karimi, wanda ke wakiltar Yankin Sanatan Kogi ta Yamma, ya yaba wa hukumomin tsaro bisa ƙoƙarinsu da sadaukarwar da suke yi wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ƴan ƙasa a faɗin Najeriya.

Sai dai, ya buƙaci shugabannin hukumomin tsaro su fuskanci sabon ƙalubalen da ke tunkarowa ta hanyar gudanar da cikakken bincike kan dalilan da ke haddasa hakan, tare da ɗaukar matakan gaggawa.

Sunday Karimi
Sanata Sunday Karimi ya yabawa hukumomin tsaro Hoto: Senator Sunday Karimi
Asali: Facebook

'Ana ƙoƙarin ɓata Bola Tinubu' - Karimi

“Wannan gwamnati ta yi aiki tuƙuru a cikin shekaru biyu da suka gabata domin magance matsalolin tsaron da ta gada, ciki har da ƙara kasafin kuɗin tsaro sosai."
"A majalisar tarayya, akwai haɗin gwiwa domin tabbatar da cewa an cimma manufofin gwamnati ta hanyar daidaiton hulɗa tsakanin ɓangaren zartarwa da na dokoki, wanda ke tabbatar da tsaro ga ƴan Najeriya gaba ɗaya.”
“An sami wannan nasarar a wani lokaci. Abin takaici, yanzu ga wannan dawowar ta rashin tsaro wadda ke barazana ga nasarorin shugaban ƙasa. Ina zargin akwai hannun masu cin amana wanda hakan ke buƙatar yin bincike cikin gaggawa."

- Sanata Sunday Karimi

Naja'atu ta zargi Tinubu da nuna ƙabilanci

A wani labarin kuma, kun ji cewa Hajiya Naja'atu Mohammed wacce fitacciyar ƴar siyasa ce ta nuna rashin gamsuwa da kamun ludayin mulkin Shugaba Bola Tinubu.

Naja'atu Mohammed ta zargi mai girma Bola Tinubu da fifita yankinsa fiye da sauran sassan Najeriya.

Ta bayyana cewa shugaban ƙasan ya fi fifita yankin Yarbawa wato Kudu maso Yamma inda nan ne ya fito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta [email protected]

OSZAR »