An Samu Kuskure, Ɗan Sanda Ya Kashe Wani Ɗalibi da ke Rubuta Jarabawar WAEC
- Wani ɗalibi ya mutu a Ibadan yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa zana jarrabawar WAEC, bayan dan sanda ya harbe sa da bindiga
- Fusatattun matasa da ‘yan kasuwa sun dauki gawar ɗalibin zuwa ofishin gwamnatin Oyo, inda suke neman a gaggauta daukar mataki
- Rundunar ‘yan sanda ba ta fitar da jawabi ba, yayin da jama’a ke caccakar rashin daukar mataki da kuma hukunta jami’in da ya harba
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Oyo - Harsashin bindigar wani dan sanda ya hallaka wani ɗalibi mai shirin rubuta jarabawar kammala sakandire ta WAEC a birnin Ibadan, jihar Oyo.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a kan titin kasuwar Gbagi, lokacin da ɗalibin ke kan babur tare da mahaifinsa, suna hanyarsu zuwa cibiyar jarrabawa.

Asali: Twitter
'Dan sanda ya harba bindiga, dalibi ya mutu
Shaidu sun ce wani ɗan sanda da ke bin wasu da ake zargin 'yan damfara ne ya harba bindiga, amma aka samu kuskure ya samu dalibin, inji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Rahoton ya nuna cewa an garzaya da yaron zuwa asibitin Welfare yayin da jini ke zuba daga jikinsa. Likitoci sun tabbatar da mutuwarsa bayan isarsu.
Wasu na zargin cewa ɗalibin na tare da ɗan uwansa, wanda kamar tagwaye ne a lokacin da lamarin ya faru a ranar Talata, 20 ga Mayu, 2025.
Mutane da dama ciki har da matasa da ƴan kasuwar da ke wajen sun fusata matuka, inda suka ɗauki gawar yaron zuwa ofishin gwamnatin jihar Oyo, tare da yin zanga-zangar neman adalci.
Masu zanga-zangar sun bukaci Gwamna Seyi Makinde da yagaggauta daukar mataki, yayin da a hannu daya jami’an tsaro ke ƙoƙarin shawo kan taron jama’ar.
'Yan sanda ba su yi martani kan lamarin ba
Sai dai jaridar Leadership ta rahoto cewa har zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoto, rundunar ƴan sandan jihar Oyo ba ta fitar da wata sanarwa ba.
Kakakin rundunar, SP Adewale Osifeso, bai amsa tambayoyin manema labarai ba, wanda hakan ya kara hura wutar fushin da jama'a ke yi.
Shafukan sada zumunta sun cika da alamar #EndPoliceBrutality, inda mutane ke wallafa bidiyon zanga-zangar da kuma tunatar da irin wannan lamari da ya faru a baya.
A shekarar 2022, wani ɗalibi ya mutu sakamakon kuskuren harbin bindigar 'yan sanda a Eruwa, sai dai har yanzu ba a ga sakamakon binciken da aka yi ba.

Asali: Twitter
Oyo: An dauki gawar dalibin zuwa asibiti
An dauki gawar ɗalibin zuwa dakin ajiye gawa na asibitin Adeoyo, inda jama’ar Ibadan ke ci gaba da jimamin wannan rashi da suka bayyana a matsayin “halin ko-in-kula na jami’an tsaro.”
Gwamna Makinde bai fitar da wata sanarwa ba dangane da lamarin, sai dai masu zanga-zangar na fatan muryarsu za ta kai ga daukar mataki kan jami’in da ya harba bindigar.
Ana cigaba da neman cikakken bayani kan waɗanda ake zargi da damfarar da aka ce ƴan sandan ke binsu, domin har yanzu ba a san ko su wanene ba.
'Dan sanda ya harbe dalibar ajin karshe a jami'a
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani ɗan sanda ya harbe wata ɗalibar jami'a da ke ajin ƙarshe a shingen binciken ababen hawa da ke Makurdi, babban birnin jihar Benue.
Shaidu sun bayyana cewa lamarin ya faru ne yayin da ɗalibar ke cikin wata motar haya, tana hanyarta ta komawa makaranta domin ci gaba da karatu.
Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce daga abokanta da kuma masu rajin kare haƙƙin ɗan adam, inda suka bukaci a hukunta jami’in da ya harba ɗalibar cikin gaggawa.
Asali: Legit.ng