Mutane na Tserewa daga Gidajensu saboda Zafafa Hare Haren 'Yan Bindiga a Zamfara

Mutane na Tserewa daga Gidajensu saboda Zafafa Hare Haren 'Yan Bindiga a Zamfara

  • Al’ummar wasu kauyuka a Kauran Namoda a Zamfara na guduwa daga gidajensu da daddare saboda yawaitar harin ‘yan bindiga
  • Akalla mutum hudu sun mutu yayin da aka sace wasu 26 a sababbin hare-haren da aka kai tsakanin Alhamis zuwa Asabar
  • Gwamna jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ba da tabbacin ƙara taimaka wa hukumomin tsaro don kawo ƙarshen matsalar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Sababbin rahotanni daga Kaura Namoda a jihar Zamfara na nuna yadda jama’a ke shiga mummunan hali sakamakon tsanantar hare-haren ‘yan bindiga a yankin.

Rahotanni na nuni da cewa wasu al’ummomi sun fara barin gidajensu da daddare, suna dawowa da safe.

Zamfara
Mutane na guduwa a gidajensu saboda hare hare a Zamfara. Hoto: Legit
Asali: Original

A cewar Daily Trust, hare-haren da aka kai tsakanin Alhamis da Asabar ya yi sanadin mutuwar mutum hudu tare da sace wasu 26, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin tsananin fargaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Wani ganau ya bayyana cewa kauyen Sabon Gari ne ya fi shan wahala, inda wata mata ta rasa ranta, sannan aka yi garkuwa da kimanin mutum 20.

Hare haren 'yan bindiga ya karu a Zamfara

Rahotanni sun nuna cewa an kai hare-haren ne a tsakanin ƙarfe 1:00 na dare zuwa 2:30 na safiyar Asabar, duk da kasancewar jami’an tsaro a garin Kaura Namoda.

Rahoton Trust Radio ya ce an zargi wani shahararren ɗan bindiga, Bello Kaura, wanda aka fi sani da Dan Sade, da jagorantar hare-haren.

An ce yana da sansani a bayan Bakalori, kuma yana amfani da sanin da ya yi wa yankin domin kai farmaki.

Wani mazaunin yankin ya ce:

“Dan Sade yana da dangantaka da yankin. Mahaifinsa ma sarki ne a kauyen Kaura Namoda. Har masallaci da shaguna ya gina a wasu kauyuka.”

Mutane na tserewa daga gidajensu a Zamfara

An bayyana cewa mazauna kauyuka irin su Unguwan Sarkin Musulmi, Unguwan Rogo da Yamitsawa sun daina zama a gidajensu da daddare.

Rahoto ya ce mutanen yankunan na barin gida da yamma, sai su koma da safe saboda tsoron hare-hare.

Wani da ya tsallake rijiya da baya ya ce:

“Muna roƙon gwamnati ta kafa sansanin sojoji a Kungurki domin hana shigowar ‘yan bindiga.”

A cewarsa, Sabon Gari da Kungurki sun fi fuskantar barazanar hare haren 'yan bindiga a baya-bayan nan.

A wani hari daban da ya faru a kauyen Kungurki, an kashe mutum hudu yayin da aka sace mutum daya.

Bayan kwana daya, ‘yan bindigar sun nemi fansa na Naira miliyan 3, amma sun hana kowa jin halin lafiyar wanda suka kama.

Matakin da gwamnati ke dauka a Zamfara

Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya ce gwamnatinsa na aiki tukuru don kawo ƙarshen matsalar tsaron.

Dauda Lawal ya bayyana cewa an bai wa hukumomin tsaro motocin aiki 140 domin ƙarfafa ayyukansu.

Dauda Lawal
Gwamnan Zamfara ya ce suna kokarin magance matsalar tsaro. Hoto: Dauda Lawal
Asali: UGC

An kama iyalan dan bindiga a Saudiyya

A wani rahoton, kun ji cewa ana rade radin cewa an kama wasu mata biyu a kasar Saudiyya bisa alaka da dan bindiga, Ado Aliero.

Duk da ba a bayyana sunansu ba, hukumomin tsaro na cigaba da bincike domin tabbatarwa ko kore alakar matan da dan bindigan.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa ana zargin daya daga cikin matan mahaifiyar dan ta'addan ce, dayar kuma matarsa ta aure.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. [email protected]

OSZAR »