Atiku Abubakar Ya Tuna baya, Ya Bayyana Yadda aka Daure Mahaifinsa
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi magana kan wasu darussan da ya koya a rayuwarsa
- Atiku Abubakar ya bayyana cewa saboda ƙin bari a sanya shi a makaranta, an taɓa ɗaure mahaifinsa
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya kuma yi bayani kan yadda ya taɓa tsallake rijiya da baya lokacin da aka yi yunƙurin hallaka shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Adamawa - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya yi magana kan muhimmancin ilmi.
Atiku Abubakar wanda ya kafa jami’ar American University of Nigeria (AUN), jaddada cewa ilimi shi ne mafi tasiri wajen cigaban mutum da ƙasa baki ɗaya.

Asali: Facebook
Ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi ga ɗaliban da za su kammala karatu a ajin shekara ta 2025 na jami’ar AUN, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Meyasa aka taɓa ɗaure mahaifin Atiku?
Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya kuma bayyana yadda aka garƙame mahaifinsa saboda ya ƙi yarda a sanya shi makaranta.
"An ɗaure mahaifina saboda ya ƙi amincewa da a kai ni makaranta."
“Mun fara daga tushe, mu na zaune ne a ƙasa ba tare da kujeru ba, mu na rubutu da yatsunmu. Daga wannan hali na fara."
- Atiku Abubakar
Atiku ya magantu kan haƙuri da jarumta
Atiku ya jaddada muhimmancin haƙuri da jarumta, yayin da ya bayyana wasu darussa daga rayuwarsa.
“Na fuskanci ƙalubale da dama. An nemi hallaka ni, amma ban taɓa ja da baya ba."
“Haƙuri ba rauni ba ne. Wani makami ne na masu hikima. A lokacin da muka bijire wa mulkin soja, sun ba ni gwamna ba tare da zaɓe ba, na ƙi karɓa. Amma a 1999, na ci kujerar bisa ƙa’ida, kuma na zama mataimakin shugaban ƙasa."
- Atiku Abubakar
Ya kuma tuna yadda ya koyi jarumta daga ubangidansa, marigayi Janar Shehu Musa Yar’Adua, wanda ya nuna jarumta a yayin da aka yanke masa hukuncin kisa.
“A ranar da aka shirya kashe shi, jininsa bai hau ba, kamar ba abin da ke faruwa. Wannan shi ne soja, wannan shi ne jarumta."
- Atiku Abubakar

Asali: Facebook
Yadda Atiku ya tsallake rijiya da baya
Atiku ya kuma bayyana yadda ya tsallake yunƙurin kashe shi da aka yi a Kaduna.
“Na ɓoye matata da ƴaƴana a cikin wurin ajiyar kaya, sannan na fito na fuskanci waɗanda suka kawo hari. Sun harbe ni amma ba su same ni ba. Na miƙe na tambaye su, ‘me ya sa kuka buɗe wuta?’ Wannan shi ne ainihin jarumta."
- Atiku Abubakar
Oshiomole ya yi wa Atiku shaguɓe
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ahugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Adams Oshiomole, ya yi shaguɓe ga Atiku Abubakar.
Samata Adams Oshiomole wanda yake wakiltar Edo ta Arewa a majalisar dattawa, ya buƙaci tsohon mataimakin shugaban ƙasan da ya rubuta littafi kan sauya sheƙa.
Adams Oshiomole ya bayyana cewa a tarihin Najeriya ba a samu ɗan siyasar da ya sauya jam'iyya ba kamar Atiku Abubakar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng