Mutane Sun Fara Fargaba da Rikicin Sarauta Ya Kara Tsananta duk da Kara na gaban Kotu
- Rikicin naɗin sarauta a kauyen Isiagu da ke ƙaramar hukumar Nkanu ta Gabas ya ƙara zafi duk da an kai ƙara gaban kotu
- Rahoto ya nuna cewa mazauna garin sun fusata da ganin wata takarda da ke nuna an naɗa Prince Tony Ike Okoye a matsayin sabon Igwe
- A cewarsu, ba zai yiwu a naɗa Okoye ba tare da bin al'ada da ƙa'idojin zaɓe ba, sun roki gwamnatin Enugu ta bari su yi abin da ya dace
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Enugu - Wani rikicin cikin gida na neman ɓarkewa a ƙauyen Isiagu Akpawfu da ke ƙaramar hukumar Nkanu ta Gabas a Jihar Enugu, kan naɗin sabon basaraken garin.
An ruwaito wasu mutane na neman naɗa sabon Igwe, watau basaraken garin ba tare da ƙa'idoji da shirya zaɓe ba.

Asali: Original
Rikicin sarauta ya ɗauki zafi a Enugu
Leadership ta binciko cewa takaddamar sarautar Igwe tana gaban kotun ɗaukaka ƙara amma kwatsam aka ji labarin an ba wani Prince Tony Ike Okoye takardar shaidar nasara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Sai dai wannan naɗin sarauta ba tare da zaɓe ba kamar yadda aka saba bai yi wa yawancin mazauna ƙauyen dadi ba.
Yayin ganawa da manema labarai a ƙarshen mako, ɗaya daga cikin masu neman sarautar, Cif James Ede Ogbu, ya ce an hana shi shiga zaɓen bisa zargin cewa ba ɗan ƙauyen ba ne, zargin da ya kira abin dariya.
“Ni daga Obodo Onovo Nwowo na ke kuma kowa ya gaskata hakan. Don haka tambayata ita ce, me ya sa za a ce ni ba ɗan gari ba ne?” in ji Ogbu.
Ana neman hana wasu neman sarauta
Ya zargi wasu da ƙoƙarin kawar da sunan danginsa daga jerin sunayen ‘yan ƙauyen da gangan domin hana shi shiga takarar neman sarautar Igwe.
Cif Ogbu ya jaddada cewa kundin tsarin ƙauyen ya tanadi zaɓe a matsayin hanyar naɗa Igwe, ba naɗawa ko ɗora mutum da karfi ba, yana mai cewa babu wani zaɓe da aka gudanar kafin bayyana Okoye.
Ya ce an tantance ‘yan takara uku kafin daga bisani Okoye ya samu hukuncin kotu da ya dakatar da tsarin zaɓen, sannan ya garzaya kotun ɗaukaka ƙara domin tabbatar da cewa shi ɗan kauye ne.
Gwamnatin Enugu ta naɗa sabon Igwe
A cewar Ogbu, abin mamakin shi ne kwatsam kwamishinan harkokin ƙananan hukumomi da harkokin sarauta na Enugu, Okey Ogbodo, ya amince da Okoye a matsayin sabon Igwe a ranar 26 ga Afrilu, 2025, duk da ƙara na gaban kotu.
Ya roƙi Gwamna Peter Mbah da ya shiga tsakani domin ganin an bi doka da adalci wajen naɗa sabon basaraken, rahoton Daily Post.
A nasa bangaren, Ede Stephen, mataimakin sakataren ƙungiyar ƙauyen, ya tabbatar da cewa Ogbu ɗan ƙauyen ne, yana mai cewa:
"Ba ma son gwamnati ta amince da kowa a matsayin Igwe yanzu. Ba mu da Igwe tukuna, muna so mu zaɓi Igwe namu ta hanyar da doka ta tanada.”
Kotu ta kori karar neman sauke sarki a Delta
A wani labarin, kun ji cewa babbar kotun jihar Delta ta kori ƙarar da aka nemi tsige nadin Cif Oma Eyewuoma a matsayin Ologbotsere.
Mai shari’a V.O. Agboje na babbar kotun ya bayyana cewa ba a kawo karar a daidai ba, wanda hakan ya sa kotun ta yi watsi da ita.
Tun farko dai an nada Cif Eyewuoma a matsayin Ologbotsere a shekarar 2023 bayan Olu na Warri ya cire Cif Ayiri Emami daga mukaminsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng