Jihohi 6 da Ɗalibai Za Su Sake Rubuta Jarabawar UTME 2025 bayan Kuskuren JAMB
- JAMB ta yarda cewa an samu kuskure a jarabawar UTME 2025, inda ɗalibai fiye da miliyan 1.5 suka samu ƙasa da maki 200
- Bayan koke daga ɗalibai, JAMB ta ce ɗalibai 379,997 daga cibiyoyi 157 a Legas da Kudu maso Gabas za su sake rubuta jarabawa.
- Hukumar za ta tuntuɓi waɗanda lamarin ya shafa, kuma WAEC ta ba da damar ɗaliban su rubuta jarabawar da aka sake wa rana.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar shirya jarabawar shiga jami'a ta kasa (JAMB) ta amsa cewa an samu kuskure a sakamakon wasu ɗaliban da suka rubuta jarabawar UTME 2025.
Fiye da ɗalibai miliyan 1.9 ne suka zana jarabawar bana, inda kimanin miliyan 1.5 ko 78% suka samu ƙasa da maki 200 daga cikin 400 da ake iya samu.

Asali: Facebook
Yadda dalibai suka sha kasa daga 2021 zuwa 2025
Sai dai wasu daga cikin ɗaliban da lamarin ya shafa sun yi zanga-zanga, suna mai cewa an tauye masu hakki a jarabawar, inji rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Shugaban JAMB, Farfesa Is-haq Oloyede, ya ce wannan sakamakon da aka samu ya yi daidai da na shekarun da suka gabata. A bara, 76% na ɗaliban da suka rubuta UTME suka samu ƙasa da 200.
A cewar JAMB, a 2022, ɗalibai miliyan 1.3 daga cikin miliyan 1.7, ko a ce 78% da suka zauna jarabawar sun samu ƙasa da maki 200.
A shekarar 2021, ɗalibai 803 kawai daga cikin miliyan 1.3, ko 0.06% ne suka samu sama da maki 300, in ji Oloyede a wancan lokaci.
Jihohi 6 da za a sake jarabawar JAMB
Sai dai, bayan korafe-korafe masu yawa daga jama’a, hukumar ta kira taron masu ruwa da tsaki kuma ta sake duba sakamakon.
Oloyede ya ce an yanke shawarar cewa dukkanin ɗaliban da kuskuren ya shafa a cibiyoyi 157 daga cikin 882 za su sake rubuta jarabawar daga ranar Juma’a, 16 ga Mayu.
Jimillar ɗalibai 379,997 ne daga cikin waɗannan cibiyoyi 157 a Lagos da jihohin Kudu maso Gabas za su sake rubuta jarabawar JAMB din..
Rahoton Premium Times ya nuna cewa cibiyoyin sun haɗa da 65 a yankin Legas da 92 a yankin Owerri.
Jihohin da lamarin ya shafa su ne:
- Legas
- Abia
- Enugu
- Imo
- Ebonyi
- Anambra

Asali: Twitter
JAMB ta nemi taimakon hukumar WAEC
Ɗalibai 206,610 ne aka gano cewa lamarin ya shafa a cibiyoyi 65 da ke yankin Legas, yayin da 173,387 suka fito daga cibiyoyi 92 na yankin Owerri.
JAMB za ta tuntuɓi waɗanda abin ya shafa ta sakonnin waya, imel, shafukan su na hukumar da kuma kiran waya kai tsaye.
Ana kuma sa ran ɗaliban za su sake buga takardun shaidar zaunawa jarabawar da aka sauya wa lokaci.
Oloyede ya ce JAMB ta tuntuɓi hukumar WAEC wacce ke gudanar da jarabawar kammala sakandire (WASSCE) a yanzu, domin a ba su damar yin jarabawar, kuma WAEC ta amince.
Abin da ya sa dalibai suka fadi jarabawar JAMB
A wani labarin, mun ruwaito cewa, fiye da ɗalibai miliyan 1.5 ba su samu maki 200 ba a UTME ta 2025, sakamakon kura-kuran da hukumar JAMB ta amsa cewa ta yi.
Shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya ɗauki alhakin kuskuren, yana mai cewa sakaci daga cikin gida ne ya janyo wannan koma-bayar sakamako.
JAMB ta bayyana cewa fiye da ɗalibai 380,000 za su sake rubuta jarabawar, bayan da ta tattauna da masana domin gano matsalolin da aka fuskanta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng