Sojojin Najeriya Sun Yi wa Boko Haram Kaca Kaca a Dajin Sambisa
- Rundunar Operation Hadin Kai tare da CJTF sun kai farmaki kan maboyar 'yan ta’adda a dajin Sambisa, suka kori mayakan Boko Haram daga matsugunansu
- An kwato makamai da kayan hada bama-bamai daga Garin Malam Ali da kuma yankin Ukuba, yayin da ‘yan ta’addan suka tsere suka bar kayan yakin nasu
- Rundunar ta kuma kai samame ta sama a Garin Baaba a ranar 13 ga Mayu, aka hallaka ‘yan Boko Haram da dama tare da lalata makaman da suke aiki da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Sojojin Najeriya a karkashin Operation Hadin Kai tare da hadin guiwar 'yan sa-kai na CJTF sun yi wani kwanton bauna mai karfi a dajin Sambisa da ke jihar Borno.
Sojoji sun kai farmakin ne domin korar ‘yan Boko Haram da suka dade suna amfani da yankin a matsayin mafaka.

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan harin ne a cikin wani sako da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Sojoji sun kwato makaman Boko Haram
Sojoji da jami’an CJTF sun yi nasarar karbe matsugunan ‘yan ta’addan, suka kwato makamai da kuma kayan hada bama-bamai da ake aiki da su wajen kai hare-hare a Arewa maso Gabas.
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan ta’addan sun tsere daga matsugunansu bayan da suka fuskanci karfin sojoji, inda suka bar bindigogi, harsasai da wasu kayayyaki.
Rundunar ta ce ana cigaba da bincike da zurfafa kai hare-hare a cikin dajin Sambisa domin kakkabe sauran maboyar ‘yan ta’addan da suka rage.
Ana sa ran sojojin Najeriya za su cigaba da zafafa hare hare kan 'yan ta'addan ISWAP da Boko Haram da sauran 'yan bindiga a fadin kasa baki daya.
Jami'an Sojoji sun hallaka Boko Haram a Borno
Kafin wannan farmaki na ranar 15 ga Mayu, sojojin Operation Hadin Kai sun gudanar da wani samame ta sama a ranar 13 ga Mayu a Garin Baaba.
A yayin farmakin, sojoji sun gano maboyar mayakan Boko Haram ta hanyar leken asiri daga jiragen yaki.

Asali: Facebook
Rundunar ta ce tawagar masu tarwatsa bama-bamai (EOD) sun lalata kayan fashewar da aka samu a wajen, yayin da ake ci gaba da kai samame a yankin don tabbatar da zaman lafiya.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun sababbin hare haren 'yan Boko Harama a Arewa maso Gabas, musamman a jihohin Borno da Yobe.
Sai dai duk da sabuwar barazanar kungiyar, gwamnatin Najeriya ta sha alwashin gamawa da su tare da sauran 'yan ta'adda a fadin kasar.
Kokarin da gwamnati ke ikrarin yi kan Boko Haram
Gwamnatin Najeriya ta sha alwashin kawo ƙarshen matsalar 'yan ta'adda, musamman Boko Haram, tun daga shekarar 2015 lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya hau mulki.
A lokacin, ya yi alkawarin "ƙarƙashin mulkinsa, Boko Haram za ta zama tarihi." Sai dai, bayan shekaru da dama, har yanzu ana fama da hare-haren 'yan ta'adda a yankunan Arewa maso Gabas, musamman a jihohin Borno da Yobe.
A cikin watan Janairu 2024, Shugaba Bola Tinubu ya sake yin alkawarin "kawo ƙarshen ragowar Boko Haram, ISWAP, da sauran 'yan ta'adda," yana mai cewa "ba za mu huta ba har sai mun kakkabe su gaba ɗaya."
Amma, a cikin watan Afrilu 2025, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya bayyana damuwarsa cewa "Borno na rasa ƙarfi," yana mai cewa hare-haren 'yan ta'adda sun ƙaru "kusan kullum ba tare da wani ƙoƙari ba."
Har yanzu akwai Boko Haram
Wannan ya nuna cewa, duk da ƙoƙarin gwamnati, har yanzu matsalar tana ci gaba da tasiri, rahoton Vanguard.
A gefe guda, gwamnatin ta kafa shirin "Operation Safe Corridor" don deradikalizawa da maido da 'yan ta'adda da suka miƙa wuya.
Sai dai, wannan shiri ya fuskanci suka daga jama'a saboda rashin cikakken bayani da kuma damuwar cewa yana iya ƙarfafa masu laifi.
Bugu da ƙari, rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin waɗanda suka kammala shirin sun fuskanci ƙalubale wajen komawa al'umma saboda tsoron ramuwar gayya.
Tinubu zai dauki jami'an tsaron daji aiki
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta fito da wata sabuwar hanyar yaki da 'yan ta'adda a fadin kasar nan.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da daukar jami'an tsaron dazuka a dukkan jihohi domin magance matsalar tsaro.
Bola Tinubu ya ce za a ba jami'an tsaron horo na musamman domin yaki da dukkan 'yan ta'addan da suka fake a dazukan Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng