Fada Ya Barke tsakanin Fulani Makiyaya da Manoma a Jihar Yobe, An Samu Asarar Rai
- Rikici ya barke a Nangere, Yobe tsakanin manoma da makiyaya bayan wani bafullatani ya shiga gona da dabbobinsa ya lalata amfanin noma
- An harbi Babayo Maina da kibiya a goshinsa, sannan aka kashe Usman Mohammed, dan shekara 35, daga kauyen Chikuriwa a rikicin
- Jami'an tsaro sun kwato shanu da awaki da raguna, sannan suka kira shugabannin manoma da makiyaya domin warware rikicin cikin zaman lafiya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Yobe - Rahotanni da muke samu na nuni cewa wani mummunan rikici ya barke tsakanin manoma da Fulani makiyaya a karamar hukumar Nangere ta jihar Yobe.
An rahoto cewa rikicin wanda ya fara daga cacar baki, ya rikide zuwa harbi da kibiya, wanda a karshe ya yi sanadin mutuwar mutum daya tare da jikkatar wasu.

Asali: Twitter
Fada ya barke tsakanin makiyaya da manoma
Majiyoyin tsaro sun shaida wa Zagazola Makama cewa rikicin ya samo asali ne daga sabani da aka samu tsakanin wani manomi da makiyayi kan lalata amfanin gona.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
An ce da yammacin ranar Litinin, 13 ga Mayu, rikicin ya barke bayan wani bafullatani ya shiga gonar wani manomi da dabbobinsa a Nangere.
An ce manomin, mai suna Babayo Maina, ya tunkari makiyayin domin jin dalilin da ya sa ya sanya masa dabbobi a cikin gona har suka lalata amfanin gonarsa.
An kashe mutum 1, an raunata da dama
Sai dai an rahoto cewa a yayin da manomi da makiyayan suka fara sa-in-sa, sai aka harbi Babayo Maina Osi da kibiya a goshinsa, lamarin da ya raunata shi sosai.
Rikicin ya rikide zuwa tashin hankali mai tsanani lokacin da manoman yankin da ke kusa suka yo kan makiyayan tare da 'yan uwansa.
A yayin artabu, an harbe wani matashi mai suna Usman Mohammed, dan shekara 35 daga kauyen Chikuriwa da kibiya, lamarin da ya yi ajalinsa a asibitin gwamnati da ke Nangere.

Asali: UGC
An tattauna tsakanin makiyaya da manoman Yobe
An rahoto cewa jami’an tsaro sun hanzarta kai dauki, inda aka tura ‘yan sanda zuwa wurin da lamarin ya faru domin dawo da zaman lafiya.
Hukumomin tsaro sun kwato shanu biyu da awaki da raguna 29 da ake zargin manoma sun kwace daga hannun makiyaya yayin wannan rikicin.
An ce an gayyaci shugabannin garuruwan manoma da makiyaya domin tattaunawa kan rikicin yayin da bincike ke ci gaba da gudana don hana sake barkewar tashin hankalin.
An kashe Bafullatani da shanu 100 a Filato
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani sabon hari da aka kai wa makiyaya Fulani a jihar Filato ya yi sanadiyyar mutuwar mutum daya da shanu fiye da 100.
Kungiyar Fulani ta MACBAN ta yi ikirarin cewa wasu matasan kabilar Berom daga kauyukan jihar ne suka kai wannan harin, inda suka harbe dabbobi, tare da yanka wasu.
A yayin da kungiyar Fulani ke kira ga gwamnati da masu ruwa da tsaki da su kawo karshen hare-haren da ake musu na ba gaira babu dalili, matasan Berom sun fito sun musanta zargin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng