'Gwamnan Adamawa Zai Fice daga PDP,' Malamin Addini Ya Hango Matsaloli a Jihohi 6
- Primate Elijah Ayodele ya bayyana cewa gwamnonin Neja, Abia, Imo, Adamawa da Delta za su fuskanci rikicin siyasa, tsaro, da zarge-zarge
- Malamin addinin ya shawarci Gwamna Alex Otti da ya kauce wa manufofin da za su jawo masa suka, tare da gaggauta magance matsalar tsaro
- Ayodele ya ce Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa zai bar PDP yayin da Gwamna Sheriff Oborevwori zai samu sabani da Shugaba Bola Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Babban limamin cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya fitar da sabon hasashe game da makomar wasu gwamnonin Najeriya shida.
A wata sanarwa da mai taimaka masa kan kafafen yada labarai, Osho Oluwatosin ya fitar, limamin ya bayyana matsalolin da gwamnoni za su fuskanta nan gaba.

Asali: Facebook
Ayodele ya hango rikicin siyasa a Neja
A jihar Neja, limamin ya gargadi Gwamna Umaru Bago kan rikicin siyasa da na tsaro, inda ya yi hasashen cewa sabani zai barke tsakaninsa da wasu kusoshin jihar, inji rahoton The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Primate Ayodele ya ce gwamnan Neja ba zai samu yabon da ya dace duk da kokarin da yake yi, saboda rikice-rikicen siyasa da tsaro da za su dabaibaye mulkinsa.
Ya kuma yi hasashen rikici tsakanin gwamnan Neja da mataimakinsa da kuma wasu fitattun shugabannin siyasa na jihar.
"Gwamna Otti zai fuskanci zarge-zarge" - Ayodele
A jihar Abia kuwa, ya ja kunnen Gwamna Alex Otti da kada ya lalata ayyukan alherin da ya fara da manufofin da za su jawo masa suka.
Limamin ya ce gwamnatin Otti za ta fuskanci zarge-zargen karya, kuma wasu daga cikin ‘yan majalisar zartarwarsa za su sauya sheka zuwa wasu jam'iyyu.
Ya bukaci Gwamna Otti da ya gaggauta magance matsalolin tsaro da ke kara yawaita a jihar don kaucewa matsaloli masu muni a nan gaba.
Malami addinin ya ba gwamnan Imo shawara
A Imo, Primate Elijah Ayodele ya bukaci Gwamna Hope Uzodinma da ya yi hattara wajen zaben wanda zai gaje shi, yana mai cewa kuskurensa zai iya haifar da matsala babba.
Malamin addinin ya gargadi gwamnan da ya ya bar fitattun ‘yan takara su tsaya, tare da yin zabe na gaskiya, idan ba haka ba jam’iyyarsa za ta sha kaye a zabe mai zuwa.
Ya ce dan takarar Uzodinma zai doke Emeka Ihedioha, amma gwamnan zai fuskanci barazana daga matsalar tsaro da kuma ta talakawa, inda ya nemi ya kaddamar da shirin yaki da talauci.
Limamin ya kara da cewa Uzodinma zai iya samun ci gaba a siyasa idan ya kaucewa duk wani kage daga fadar shugaban kasa da kuma kulawa da lafiyarsa.
"Fintiri zai bar jam'iyyar PDP" - Ayodele
A jihar Adamawa kuwa, Primate Ayodele ya bayyana cewa Gwamna Ahmadu Fintiri zai bar PDP nan gaba kadan kuma zai samu rikici da Atiku Abubakar.
Ya ce Fintiri zai bata wa magoya bayansa rai, inda zai janyo rikici wa kansa kuma ya yi amfani da addini ta hanyar da ba ta dace ba.
Limamin ya shawarci Gwamna Fintiri da ya tsara sababbin dabarun siyasa domin kaucewa faduwar jam'iyyarsa a zabe mai zuwa.
Ya kara da cewa Fintiri da Nuhu Ribadu za su fada cikin rikici mai muni, wanda zai bar baya da kura a siyasance, musamman ga jihar Adamawa.
Ayodele ya kuma yi gargadi ga jihar Adamawa da su dauki mataki tun wuri, kan yiwuwar hare-haren ta’addanci, bullar cutar kwalara da kuma sankarau.

Asali: Twitter
"Gwamna Sheriff zai samu sabani da Aso Villa" - Ayodele
A Delta, limamin ya ce Gwamna Sheriff Oborevwori ba zai samu karbuwa a jam’iyyar APC ba, kuma zai samu matsala da fadar shugaban kasa.
Faston ya bayyana cewa Sheriff zai rikita jam’iyyar APC a jihar Delta, inda wasu mambobi za su yi murabus saboda yadda ake tafiyar da jam’iyyar.
Ya kara da cewa Gwamna Sheriff zai sake samun sabani da wanda ya gaji mulki a hannunsa, lamarin da zai kara rikita siyasar jam’iyyar a jihar.
An ji ya yi gargadi ga jihar Delta kan yiwuwar harin bam, yana mai kira ga jami’an tsaro da su kara sa ido don kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Wasu hasashen Fasto Elijah a baya
Primate Elijah Ayodele ya shahara wajen fitowa da hasashen abubuwan siyasa, tsaro da al’amuran rayuwa a Najeriya.
Yana amfani da irin wannan dama don jan hankalin gwamnati da jama’a game da hadurran dake tattare da rashin tsaro, rikice-rikicen siyasa, da kuma matsalolin shugabanci.
A cikin ‘yan watannin nan, Ayodele ya yi hasashen rikicin siyasa a jihohi daban-daban kamar Neja, Abia da Delta, inda ya ja hankalin gwamnonin kan barazanar rikice-rikice da zarge-zarge masu tsanani.
Misali, rahoton The Guardian ya nuna yadda Ayodele ya gargadi Gwamnan Neja, Umaru Bago, kan rikice-rikicen siyasa da tsaro da za su iya dabaibaye mulkinsa.
Haka kuma, a jihar Abia, ya shawarci Gwamna Alex Otti da ya guji ayyukan da za su jawo masa suka daga jama’a, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Bugu da kari, ya hango rikici tsakanin Gwamna Sheriff Oborevwori na Delta da fadar shugaban kasa, tare da yiwuwar wasu hare-haren ta’addanci, rahoton Premium Times ya tabo wannan batu.
Primate Ayodele na amfani da waɗannan hasashen ne don zama faɗakarwa ga gwamnati da masu ruwa da tsaki, domin kaucewa tabarbarewar al’amura da kiyaye zaman lafiya.
Primate Ayodele ya hango abin da zai faru a 2027
A wani labarin, mun ruwaito cewa, malamin addinin kirista, Primate Elijah Babatunde Ayodele, ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya ɗauki matakai masu ƙarfi don dakile rikicin siyasa.
Primate Elijah Ayodele ya yi wannan gargaɗin ne a cikin hasashensa game da abubuwan da za su iya faruwa a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
A wani faifan bidiyo, Ayodele ya bayyana cewa, idan Tinubu da mutanen da ke kusa da shi suka gaza ɗaukar matakan da suka dace, za su fuskanci ƙalubale masu yawa a zaɓen.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng