A Karshe, JAMB Ta Fadi Abin da Ya Jawo Dalibai Suka Fadi Jarabawar UTME 2025
- Sama da dalibai miliyan ɗaya da rabi sun kasa samun maki 200 a jarabawar UTME 2025 sakamakon kura-kuran da JAMB ta samu
- Farfesa Ishaq Oloyede ya ɗauki alhakin matsalar, yana mai cewa sakaci daga hukumar JAMB ne ya haddasa wannan mummunan sakamako
- JAMB ta sanar da cewa sama da dalibai 380,000 za su sake zana jarabawar, ta haɗu da ƙwararru don duba matsalolin da aka fuskanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta kasa (JAMB) ta amince da cewa wasu manyan kura-kurai sun shafi yadda dalibai suka zana jarabawar UTME ta 2025.
A wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Laraba, shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya nemi afuwar iyaye kan abin da ya jawo rashin nasarar 'ya 'yansu.

Asali: Twitter
JAMB ta gano kuskure a jarabawar UTME 2025
JAMB ta amince da kuskurenta ne yayin da aka samu ƙaraɗewar korafe-korafe daga daliban da abin ya shafa, har wasu na barazanar kai ƙara kotu, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
“Jarabawar da ya kamata ta kasance ta farin ciki, yanzu ta koma ta bakin ciki saboda kuskure guda ɗaya ko biyu,”
- Inji Farfesa Oloyede, yayin da yake matse kwalla.
Farfesa Ishaq Oloyede, ya ɗauki alhakin kuskuren da aka samu gaba ɗaya, yana mai cewa sakaci daga hukumar ne ya haifar da faduwar dalibai.
Daga cikin dalibai miliyan 1.9 da suka rubuta UTME ta 2025, sama da miliyan 1.5 ne suka gaza samun maki 200 daga cikin 400, lamarin da ya tayar da jijiyoyin wuya.
Kididdigar makin JAMB da dalibai suka samu
JAMB ta tantance sakamakon jarabawar dalibai 1,955,069, amma 4,756 (0.24%) ne kawai suka samu maki 320 ko fiye; 7,658 (0.39%) sun samu tsakanin maki 300 zuwa 319, jimillar 12,414 (0.63%) ke da maki sama da 300.
Haka nan, dalibai 73,441 (3.76%) sun samu tsakanin maki 250 zuwa 299, yayin da 334,560 (17.11%) suka samu tsakanin maki 200 zuwa 249.
Adadin ya nuna cewa an samu raguwar cin jarabawar sosai idan aka kwatanta da shekarun baya, yayin da a 2025 dalibai 983,187 (50.29%) suka samu tsakanin maki 160 zuwa 199.
Sakamakon waɗannan kura-kuran da aka samu, wasu dalibai sun fito fili suna shirin maka JAMB kotu, inda suke zargin an ci fuskarsu tare da gaza bin tsarin da ya kamata.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa hukumar JAMB na fuskantar matsin lamba daga jama'a domin gyara kura-kuran da aka samu cikin gaggawa.

Asali: Facebook
Dalibai za su sake zana jarabawar UTME 2025
Farfesa Oloyede, wanda ya nuna damuwa matuka, har da hawaye, ya sanar da cewa dalibai 379,997 za su sake rubuta jarabawar, ciki har da waɗanda suka rubuta a cibiyoyi 65 a Legas da 92 a yankin Owerri ta Kudu maso Gabas.
JAMB ta haɗu da ƙwararru daga kungiyar masanan kwamfuta ta Najeriya da shugabannin jami’o’i don binciko matsalolin fasahar da aka samu tare da samar da mafita.
Matakin sake jarabawa ya nuna cewa JAMB na ƙoƙarin tabbatar da adalci, sai dai yawan kura-kuran da suka faru ya haifar da kira na a sake duba tsarin jarabawar gaba ɗaya.
JAMB ta fitar da sakamakon UTME 2025
A wani labarin, mun ruwaito cewa, JAMB ta saki sakamakon jarabawar UTME na shekarar 2025, amma ta dakatar da na dalibai 39,834 saboda kura-kuran da aka samu.
JAMB ta bayyana cewa tana gudanar da bincike kan mutane 80 da ake zargin sun tafka maguɗi, inda jihar Anambra ta fi ko’ina yawan waɗanda ake tuhuma.
Shugaban hukumar, Farfesa Is-haq Oloyede, ya ce dalibai 467 da ba su kai shekara 18 ba sun samu maki ƙasa, inda 50 daga cikinsu suka yi damfara.
Asali: Legit.ng