Zaɓen 1993: Sule Lamido Ya Yiwa IBB Gyara kan Dalilin Soke Nasarar Abiola
- Tsohon Gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya ce hujjar da Janar Ibrahim Babangida (mai ritaya) ya bayar kan soke zaɓen 12 ga Yuni ba gaskiya ba ce
- Sule ya bayyana cewa Babangida ya gaya masa cewa Moshood Abiola yana bin Najeriya bashin N45bn, kuma hakan ne ya hana shi mika masa mulki
- Wannan bayani ya kara jefa shakku a cikin abubuwan da suka wakana a lokacin da 'yan kasar nan suka hau layi domin kada kuri'arsu a zaben a 1993
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon Gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana cewa dalilin da tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (rtd), ya bayar na soke zaɓen 12 ga Yuni.
Sule Lamido, wanda kuma tsohon Ministan Harkokin Wajen Najeriya, ya bayyana cewa babu gaskiya a cikin dalilin da aka bayar da soke zaben 1993.

Asali: Getty Images
Jaridar Aminya ta wallafa cewa Lamido ya bayyana hakan ne a cikin littafinsa na tarihin rayuwa mai suna “Being True to Myself”, wanda aka ƙaddamar ranar Talata a birnin Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Sule Lamido ya yi magana kan zaben 1993
Daily Post ta wallafa cewa Sule Lamido, maganar da Janar Babangida ya yi cewa Moshood Abiola ne ya yi nasara a zaben 1993, gaskiya ne.
Ya kara da cewa:
“A littafin Babangida ya ce Abiola shi ya ci zaɓe. A gaskiya shi ne ya ci zaɓen. Yanzu hujjar soke zaben kuma wani abu ne daban.”
“Amma ni abin da ya gaya min cewa shi ne dalilin da ya sa ya soke zaɓen shi ne saboda Abiola yana bin Najeriya bashin kuɗi naira biliyan 45 saboda haka idan ya ba shi wannan mulki to zai yi amfani da mulkin ya biya kansa, kuma a lokacin nan ƙasar ba ta da wannan kuɗin da za ta biya shi, shi ya sa ya soke zaɓen."
Ya bukaci shugaban kasa, Bola Tinubu da ya gaggauta biyan iyalan Abiola kudin da mahaifinsu ke bin Najeriya, a rufe shafin zaben 1993.
Abin da littafin Sule Lamido ya kunsa
Littafin Sule Lamido mai shafi sama da 500 ya tabo muhimman abubuwan da suka faru tun daga ƙuruciyarsa har zuwa fitowarsa cikin manyan sahun siyasa a Najeriya.
Fitattun mutane kamar su Olusegun Obasanjo, Atiku Abubakar, Peter Obi, Aminu Waziri Tambuwal da Gwamna Inuwa Yahaya sun halarci ƙaddamarwar.

Asali: Twitter
Tare da sababbin bayanan da Sule Lamido ya fitar, rikicin tarihin zaɓen 1993 ya sake ɗaukar sabon salo, tare da ƙara tayar da tambayoyi kan gaskiyar abubuwan da suka faru a wancan lokaci.
Sule Lamido ya aika sako ga Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya roƙi Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da ya biya bashin naira biliyan 45 da ake zargin MKO Abiola na bin gwamnati.
A cewar Sule Lamido, wannan bashi da ake zargin MKO Abiola na bi ya samo asali ne daga wasu kwangiloli da kamfaninsa ya kulla da ma’aikatar sadarwa a zamanin mulkin soja.
Ya ƙara da cewa lokacin da ya ziyarci Janar Ibrahim Babangida, tsohon shugaban mulkin soja ya amince cewa MKO Abiola ne ya lashe zaɓen, kuma ya tabbatar masa cewa yana bin bashin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng