Sule Lamido Ya Bukaci Tinubu Ya Biya Bashin da MKO Abiola Ya Biyo Gwamnati
- Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya tunatar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan bashin da MKO Abiola ya biyo gwamnati
- Sule Lamido wanda ya taka rawar gani a SDP ya buƙaci Shugaba Tinubu ya biya iyalan MKO Abiola bashin da ya biyo gwamnatin tarayya
- Tsohon gwamnan ya ce biyan bashin zai taimaka a rufe babin zaɓen 12 ga watan Yunin 1993 wanda soke shi ya jawo tashin hankali a kasar nan
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya miƙa buƙatarsa a gaban shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan Chief MKO Abiola.
Sule Lamido ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya biya bashin Naira biliyan 45 da ake zargin MKO Abiola na bin gwamnatin tarayya.

Asali: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce Sule Lamido ya yi wannan kiran ne a Abuja a ranar Talata, yayin da ake ƙaddamar da littafin tarihin rayuwarsa mai suna 'Being True to Myself.'
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Taron ya samu halartar manyan jami’ai da fitattun mutane ciki har da tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, Atiku Abubakar, Peter Obi, gwamnan jihar Gombe Inuwa Yahaya, tsohon gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal da wasu sanannun mutane.
Sule Lamido ya faɗi bashin da MKO Abiola yake bi
Sule Lamido ya ce biyan bashin zai taimaka wajen rufe cece-kuce da rikicin da ke tattare da zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga watan Yuni, 1993, wanda Abiola ya ci, amma aka hana shi ɗarewa kan mulki, rahoton The Punch ya tabbatar.
“Lokacin da (Janar) Murtala (Muhammed) ya rasu, Abiola ya fito da iƙirarin cewa yana bin bashi, ina tsammani, kimanin Naira biliyan 45 dangane da wasu kwangiloli da kamfaninsa na International Telephone and Telecommunication ya yi wa ma’aikatar sadarwa."
"Shugabannin sojoji a lokacin suka ce a’a. Sai ya zagaya wurin sarakunan Arewa yana kamun ƙafa, kuma sarakunan suka buƙaci a biya shi kuɗin."
“Sai dai su (sojoji) suka ce sun soke zaɓen 12 ga watan Yuni ne saboda idan har aka ba shi mulki, zai karɓi kuɗinsa kuma ƙasar za ta ɗurkushe."
"Waɗanda suka kasance kusa da Abacha ya kamata su san wannan, domin Abacha a wancan lokacin yana cikin manyan masu fada a ji, kuma dukkansu sun san da lamarin."
"Kafin na kammala jawabi na, ina so na roƙi Shugaba Tinubu da ya rufe wannan babi na 12 ga watan Yuni.”
“A cikin littafinsa, Janar Ibrahim Babangida ya amince da cewa Abiola ne ya lashe zaɓen. Lokacin da na ziyarce shi, ya kuma tabbatar cewa Abiola na bin Naira biliyan 45. Ya sha wahala sau biyu: na farko, an hana shi shugabanci, na biyu, an hana shi kuɗinsa."
- Sule Lamido

Asali: Twitter
Sule Lamido ya miƙa buƙatarsa ga Tinubu
Yayin da yake magana da ministan yaɗa labarai, wanda ya wakilci shugaban ƙasa a wajen taron, Sule Lamido ya ƙara da cewa:
"Don Allah ka gaya masa ya biya iyalan Abiola wannan Naira biliyan 45 ɗin. Idan aka biya kuɗin nan, za a gama da shafin 12 ga watan Yuni. Yana da matuƙar muhimmanci."
Tinubu ya magantu kan masu sukarsa
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan masu sukar manufofin gwamnatinsa.
Mai girma Bola Tinubu ya bayyana cewa ba zai bari masu sukarsa su karkatar masa da hankali ba wajen yin abin da ya dace ga Najeriya.
Sai dai, shugaban ƙasan ya bayyana cewa yana maraba da suka mai ma'ana domin ya inganta mulkinsa.
Asali: Legit.ng