'Yan Sanda Sun Magantu kan Bidiyon Jirgi da Ake Zargi Ya Saukewa Ƴan Bindiga Makamai

'Yan Sanda Sun Magantu kan Bidiyon Jirgi da Ake Zargi Ya Saukewa Ƴan Bindiga Makamai

  • Rundunar 'yan sanda ta musanta rade-radin cewa jirgin sama ya kai kayan abinci ko makamai ga 'yan bindiga a jihar Kogi
  • Ta bayyana cewa jirgin ya shiga aikin yaki da 'yan bindiga tare da hadin gwiwar jami’an tsaro da yan banga a Obajana
  • Rundunar ta bukaci jama’a da su daina yarda labaran karya, su rika sauraron bayanai daga hukumomin tsaro tukuna a ko da yaushe

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lokoja, Kogi - An yi ta yada wani faifan bidiyo da ake zargin jirgi mai saukar ungulu na raba makamai ga yan bindiga a wani daji da ke jihar Kogi.

An gano jirgin a cikin daji cike da wasu mutane dauke da mugayen makamai kafin daga bisani jirgin ya tashi sama wanda ya jawo ka-ce-na-ce a kafofin sadarwa.

Yan sanda sun ƙaryata taimakawa yan bindiga
Yan sanda sun ƙaryata ba yan bindiga abinci a Daji. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Facebook

Rundunar yan sandan Najeriya ta ƙaryata zargin alaƙar jami'anta da yan bindiga a cikin sanarwa da ta wallafa a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

'Yan bindiga: Faifan bidiyon ya tayar da kura

An yada faifan bidiyon inda aka gano jirgin a tsaye a cikin daji yayin da zagaye da shi ga wasu mutane dauke da makamai masu hatsari.

Mutanen da ke dajin sun fi kama da yan bindiga saboda babu kayan jami'an tsaro a jikinsu sai dai akwai mutum biyu da ke sanye da kaki.

A martanin 'yan sanda, rundunar ta ce jirgin yana taimakawa hadin guiwar jami'an tsaro ne da yan sa kai domin kawo karshen ta'addanci a jihar Kogi.

Martanin yan sanda kan ba yan bindiga makamai
Yan sanda sun ƙaryata ba yan bindiga makamai a Kogi. Hoto: Legit.
Asali: Original

Abin da yan sanda suka ce kan bidiyon

Rundunar ta ce akasin jita-jitar da ke cewa an kai kayan abinci ga ‘yan bindiga, ta ce bidiyon na nuna sahihin aikin tsaro ne na hukuma.

Ta ce lamarin ya gudana ne ranar Asabar, 10 ga Mayu, 2025, tare da hadin gwiwar jami’an tsaro, yan banga, da masu farauta a Obajana da ke Kogi.

Ta kara da cewa ce an tura jirgin sama domin tallafa wa dakarun kasa ta sama, da kuma yin sintiri yayin wannan aikin yaki da masu garkuwa da mutane.

Rundunar na bukatar jama’a su yi watsi da jita-jita marasa tushe, su kuma dogara da bayanan hukumomin tsaro na gaskiya kadai.

Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya.

Ta kuma bukaci hadin kai da sauran hukumomi da al'umma don tsaron kasa tare da kawo karshen ta'addanci a jihar da ma Arewacin Najeriya baki daya.

'Yan bindiga sun kai hari a jihar Kogi

A baya, mun ba ku labarin cewa yan bindiga sun kai hari kusa da wani tsauni a jihar Kogi, sun yi awon gaba da mutane suna tsakiyar ibadar dare.

An ruwaito cewa maharan sun kutsa wurin ibadar babu zato babu tsammani, suka fara harbe-harbe kafin daga bisani su sace mutanen.

Ƴan sa-kai sun yi kokarin daƙile harin amma maharan suka ci ƙarfinsu, suka tafi da masu ibadar da ba a tantance yawansu ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a [email protected].

OSZAR »