Zargin Cin Hanci: Ganduje Ya Samu Koma baya Shari'arsa da Gwamnatin Kano

Zargin Cin Hanci: Ganduje Ya Samu Koma baya Shari'arsa da Gwamnatin Kano

  • Buƙatar da Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar a gaban wata babbar kotun jihar Kano ba ta samu ƙarɓuwa ba
  • Mai shari'a Amina Adamu Aliyu ta yi watsi da buƙatar tsohon gwamnan Kano kan ƙalubalantar hurumin kotun na sauraron shari'ar
  • Ta bayyana cewa kotun na da hurumin sauraron ƙarar kuma za a yi hakan ko da Ganduje da sauran waɗanda ake tuhuma ba su halarta ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Wata babbar kotun jihar Kano ta yi watsi da buƙatar da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya shigar a gabanta.

Ganduje ya ƙalubalanci hurumin kotun na sauraron ƙarar mai ɗauke da tuhuma 11 da ake yi masa da wasu mutane bakwai.

Kotu ta yi watsi da bukatar Ganduje
Kotu ta ki karbar bukatar Abdullahi Umar Ganduje Hoto: @Abdullahiumargandujee
Asali: Twitter

Tashar Channels tv ta ce mai shari’a Amina Adamu Aliyu, wacce ke jagorantar sauraron karar, ta yanke wannan hukuncin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Kotu ta yi watsi da buƙatar Ganduje

Mai shari'a Amina Adamu Aliyu ta ce ƙorafin farko wanda Ganduje da sauran waɗanda ake tuhuma suka gabatar bai da inganci kuma bai cancanci sauraro ba.

Ta tabbatar da cewa kotun na da ikon sauraron ƙarar, wadda ke ɗauke da zarge-zargen cin hanci, haɗin baki, almundahana da karkatar da kudaden jama’a da yawansu ya kai biliyoyin Naira.

“Ƙararrakin da ke gaban wannan kotu suna da inganci. Ikon binciken laifuffuka ba yana hannun ƴan sanda ne kaɗai ba. Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafen jama'a da yaƙi da cin hanci ta jihar Kano tana da ikon yin hakan bisa doka."

- Mai shari’a Amina Adamu Aliyu

Alƙalin kotun ta jaddada cewa za a ci gaba da shari’ar ko da Ganduje da sauran waɗanda ake tuhuma shida ba su halarta ba, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Haka kuma ta umarci kamfanin Lamash Properties Limited, wanda shi ne na shida a jerin waɗanda ake tuhuma, da ya bayyana a gaban kotu.

An ɗage zaman kotun gwamnati da Ganduje

Hakazalika ta ɗage zaman kotun kan ƙarar har zuwa ranakun 30 da 31 ga watan Yuli domin cigaba da sauraron shari'ar.

Kotu ta yi hukunci a shari'ar Ganduje
Kotu ta dage.sauraron shari'ar Ganduje da gwamnatin Kano Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Wadanda ake tuhuma sun haɗa da matar Ganduje, Farfesa Hafsat Umar, da wasu mutane da kamfanoni; Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Safari Textiles Limited, Lasage General Enterprises Limited da Lamash Properties Limited.

Lauyan gwamnati, Adeola Adedipe, SAN, a martaninsa kan korafin farko da aka gabatar, ya roƙi kotu da ta yi watsi da dukkan buƙatun, yana mai bayyana su a matsayin ƙoƙari na da gangan don hana shari’ar tafiya yadda ya kamata.

Gwamna Sule ya buƙaci a daina takurawa Ganduje

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Nasararwa, Abdullahi Sule ya buƙaci ƴaƴan jam'iyyar APC su bar shugaban jam'iyyar ya sakata ya wala.

Gwamna Sule ya bayyana cewa bai kamata ƴaƴan jam'iyyar APC suna raba hankalin Abdullahi Umar Ganduje ba.

Ya nuna cewa ya kamata a bar Ganduje ya yi aikinsa domin samun nasarar jam'iyyar a zaɓuɓɓukan da za a yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta [email protected]

OSZAR »