Abin da Gwamna Zulum Ya Ce kan Sababbin Hare Haren 'Yan Boko Haram a Borno
- Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya nuna kaɗuwarsa kan sababbin hare-haren da ƴan ta'addan Boko Haram suka kai a jihar
- Zulum ya yi Allah wadai kan kisan gillar da ƴan ta'addan suke yi wa sojoji da fararen hula a hare-haren da suke kai wa
- Ya nuna cewa gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa wajen ci gaba da ƙoƙarin ganin an shawo kan matsalar ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya yi alhini kan sababbin hare-haren da ƴan ta'addan Boko Haram/ISWAP suka kai.
Gwamna Zulum ya yi Allah-wadai da jerin hare-haren da ƴan ta’addan Boko Haram da ISWAP suka kai a sassa daban-daban na jihar.

Asali: Facebook
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Dauda Iliya, ya fitar a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Ƴan Boko Haram sun yi ta'asa a Borno
Idan ba a manta ba miyagun ƴan ta’addan sun kai hare-hare a hanyar Maiduguri zuwa Damboa, da garuruwan Marte, Chibok, Gwoza, Kala Balge, da wasu ƙauyuka.
Gwamna Zulum ya kuma nuna tausayinsa da alhini ga iyalan waɗanda abin ya rutsa da su, musamman waɗanda fashewar bam ɗin da aka binne ya shafa a hanyar Maiduguri-Damboa.
Wannan fashewar da ta auku a ranar 12 ga watan Mayu, ta hallaka ma’aikata biyu na hukumar ilmi ta ƙaramar hukumar Damboa da suke kan hanyarsu zuwa Maiduguri domin rubuta jarabawar Hukumar TRCN.
Haka kuma, sojoji da dama da fararen hula sun rasa rayukansu sakamakon jerin hare-haren da aka kai kwanan nan.
Gwamna Zulum ya sha alwashi
Gwamna Zulum ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da yin aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin tarayya, sojoji da sauran hukumomin tsaro don shawo kan matsalolin tsaro.

Asali: Facebook
“Waɗannan ayyukan ta’addanci abin Allah-wadai ne matuƙa. Rasa rayukan ma’aikatan ilimi, jaruman sojojinmu da fararen hula na tunatar da mu ƙalubalen da muke fuskanta."
"A shirye na ke wajen ci gaba da tallafawa rundunar sojoji, jami’an tsaro, da ƙungiyoyin sa-kai wajen kawo ƙarshen ta’addanci da fitina a jiharmu.”
"Yawaitar hare-haren da aka samu kwanan nan ba zai hana mu ci gaba da jajircewa wajen yaƙar wannan fitinar da ta ɗauki shekaru 16 ba."
"Ina kira ga al’ummar jihar Borno da su ci gaba da zama masu juriya da addu’a. Wannan ɗan koma baya ne, kuma za mu shawo kansa, Insha Allah."
- Farfesa Babagana Umara Zulum
Zulum ya kuma yi addu’o’i da ta’aziyya ga iyalan jaruman sojoji, fararen hula da sauran al’ummar jihar Borno da wannan lokaci mai wuya ya shafa.
Ƴan Boko Haram sun farmaki sansanin sojoji
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan ta'addan Boko Haram sun kai farmaki a wani sansanin sojojin Najeriya da ke jihar Borno.
Ƴan ta'addan sun kai harin ne a sansanin sojojin da ke Marte cikin ƙaramar hukumar Damboa da tsakar dare.
Miyagun sun hallaka sojojin da ba a san adadinsu ba yayin da suka kwashe makaman yaƙi masu tarin yawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng