Uba Sani Ya Faɗi Bangaren da Tinubu Ya Kece Sauran Tsofaffin Shugabannin Najeriya

Uba Sani Ya Faɗi Bangaren da Tinubu Ya Kece Sauran Tsofaffin Shugabannin Najeriya

  • Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya yabawa salon mulkin Bola Ahmed Tinubu musamman a wasu ɓangarori a Najeriya
  • Gwamnan ya ce babu wani shugaban kasa da ya zuba jari a harkar noma kamar Bola Tinubu cikin shekaru biyu da suka wuce
  • Ya ce tallafin da Tinubu ke bayarwa ba kawai na lokaci kadan ba ne, suna da tsari mai zurfi da ke rage talauci da rashin ayyuka

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya kwarara yabo ga shugaban kasa, Bola Tinubu.

Uba Sani ya fadi ɓangare daya da Tinubu ya kece dukan sauran tsofaffin shugabannin Najeriya gaba daya.

Uba Sani ya yabawa ƙoƙarin Tinubu
Uba Sani ya yaba Tinubu a bangaren noma. Hoto: Uba Sani, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Noma: Uba Sani ya yabawa ƙoƙarin Tinubu

Gwamnan ya bayyana haka ne a wajen rabon kayan tallafin Shugaban kasa da aka yi a Cibiyar Taro ta Umaru Musa Yar'Adua, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Uba Sani ya ce babu wata gwamnati da ta zuba jari a harkar noma kamar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu cikin shekaru biyu.

Ya kara da cewa shugaba Tinubu ya dauki matakan da suka rage matakin talauci musamman a Arewacin Najeriya cikin shekaru biyu da suka gabata.

Ya ce:

“Matsalar talauci a Arewa, musamman Arewa maso Yamma, na kusa da kashi 65 zuwa 70, amma cikin shekaru biyu Tinubu ya dauki matakai.
“Ba kawai tallafi ba ne, muna magana ne kan matakai masu zurfi. Shugaban kasa ya bayar da takin zamani da kudade ga manoma ƙanana.
“Babu wani shugaban kasa da ya tallafa wa harkar noma kamar Tinubu. Tallafin ya wuce batun jam’iyya, an bai wa kowa dama."
Uba Sani ya jinjinawa salon mulkin Tinubu
Uba Sani ce Tinubu ya kafa tarihi a bangaren noma. Hoto: Uba Sani.
Asali: Twitter

'Yadda Tinubu ya taimaki Arewa' - Uba Sani

Uba Sani ya ce shirye-shiryen Tinubu sun shafi gina ababen more rayuwa, samar da ayyuka da rage talauci a matakin ƙasa baki ɗaya.

A cewarsa, fahimtar Shugaban kasa kan matsalolin jihohi ne ya sa aka samar da muhimman tsare-tsare da ke taimaka wa talakawa, musamman a Arewa.

Gwamna Uba Sani ya kara da cewa:

“Ba tare da ’yancin ƙananan hukumomi ba, ba za mu iya yaki da talauci da rashin aiki ba a Najeriya.
“Dukkan shugabannin ƙananan hukumomi 23 na Kaduna sun halarta yau. Ku ne masu tafiyar da wannan aiki kai tsaye."

Ya bayyana cewa noma na da rawar gani a tattalin arzikin Najeriya, inda ya ke da kaso 43 na GDP da kuma daukar ma’aikata 60%, The Nation ta ruwaito.

“A Jihar Kaduna, mu na amfani da noma wajen yakar talauci. Muna son ci gaba da zama cibiyar noma a Najeriya."

- Cewar Uba Sani

Uba Sani ya koka kan matsalolin Arewa

Kun ji cewa Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya nuna damuwarsa kan yadda matasan Arewacin Najeriya suke ta'ammali da kayan maye.

Uba ya koka kan yadda matasan musamman na Arewa maso Yamma suka rungumi ɗabi'ar amfani da magungunan kayan maye.

Gwamnan ya nuna cewa hakan babbar barazana ce ga lafiyar jama'a, zaman lafiya da tsaron yankin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a [email protected].

OSZAR »