Sauƙi Ya Samu: Dangote Ya Sauke Farashin Fetur, Litar Mai Ta Koma Kasa da N835

Sauƙi Ya Samu: Dangote Ya Sauke Farashin Fetur, Litar Mai Ta Koma Kasa da N835

  • Kamfanin Dangote ya sake rage farashin man fetur (PMS) a matatarsa zuwa N825 daga N835, saboda gasa a kasuwar cikin gida
  • Rage farashin zai kara saukaka wa 'yan Najeriya tare da ƙarfafa kasance matatar Dangote a matsayin jagora a kasuwar man Najeriya
  • Duk da sauke farashin da Dangote ke yi akai akai, an ce 'yan kasuwa sun shigo da lita miliyan 156 na fetur don ƙara yawan man a ƙasa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Kamfanin Dangote ta sake rage farashin man fetur (PMS) a matatarsa zuwa N825 a kan kowace lita, daga N835 da take sayarwa a baya.

An rahoto cewa matatar man Dangote ta dauki wannan matakin ne yayin da gasa a kasuwar man fetur ta cikin gida ta ci gaba da ƙaruwa.

Dangote ya rage man fetur a matatar mansa da ke Legas, lita ta koma N825
Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote | Ma'aikaci na sayar da fetur a gidan mai. Hoto: Bloomberg
Asali: Getty Images

Yadda Dangote ya fara rage fetur zuwa N835

A watan da ya gabata, wannan matatar mai sarrafa ganga 650,000 a kowace rana ta rage farashin man fetur zuwa N835 daga N865 a kowace lita, inji rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

A sanarwar da matatar ta fitar a wancan lokaci, ta bayyana cewa sabon farashin ya haɗa da kuɗin hukumar kula da man fetur ta NMDPRA.

Sanarwar da ke ɗauke da sabon tsarin farashin ta nuna cewa za a fara sayar da kowace litar man fetur a matatar a kan N835, wanda ya haɗa da harajin NMDPRA.

Farashin dizal a matatar an saita shi a kan $608 tare da ƙarin $70, wanda za a iya biya da Naira a kan N1,650/$, ko kuma da dalar Amurka.

An tsara sayar da man jirgin sama a kan $664.75 tare da ƙarin $42 a matatar da kuma ƙarin $22 a bakin teku, inda aka dakatar da sayar da gas din girki a matatar da kuma bakin teku.

Tasirin sauke farashin fetur zuwa N825

An ce rage farashin daga N835 zuwa N825 ya kara nuna ƙoƙarin kamfanin Dangote na bai wa masu amfani da man fetur din matatarsa ƙarin darajar kuɗinsu.

Binciken da jaridar ta gudanar ya nuna cewa wannan sabon sauyi na farashi zai ƙarfafa matsayin kamfanin Dangote a matsayin jagora a kasuwar man fetur ta Najeriya.

Da wannan kuma, kamfanin Dangote zai ci gaba da jan ragamar kasuwar mai a kasar, inda sauran 'yan kasuwa za su ci gaba da dogara da man matatarsa.

Wannan mataki na kamfanin Dangote zai iya rage farashin man fetur a gidajen sayar da man a faɗin ƙasar nan, wanda zai sauƙaƙa wa 'yan Najeriya, inji rahoton BusinessDay.

Matatar man Dangote na ci gaba da sauke farashin man fetur daidai da kasuwar duniya
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote. Hoto: Bloomberg
Asali: Getty Images

'Yan kasuwa sun shigo da man fetur

Duk da kokarin matatar Dangote na sauke farashin mai, hakan bai hana 'yan kasuwa shigo da akalla lita miliyan 156 na fetur daga kasashen waje ba.

'Yan kasuwar sun samu izinin hukuma don shigo da tan 117,000 na man fetur, wanda ya yi daidai da lita miliyan 156.897, cikin kwanaki takwas, daga 8 zuwa 16 ga Afrilu 2025, don ƙara yawan man a faɗin ƙasa.

Jaridar Punch ta ce ta samu bayanan ne a cikin wasu takardu daban-daban daga hukumar tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya da kuma kungiyar manyan dillalan mai ta Najeriya.

Dangote ya gana da sabon shugaban NNPCL

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya kai ziyara ga sabon shugaban hukumar NNPCL, Bashir Bayo Ojulari.

Kamfanin man fetur na NNPCL ya bayyana cewa an tattauna hanyoyin da za a ƙarfafa gasa mai kyau da kuma tabbatar da tsaron samar da makamashi a Najeriya.

Yayin da NNPCL ta yabawa Dangote kan nasarorin da ya samu, shugaban rukunin kamfanonin ya nuna gamsuwarsa da ƙwarewar sababbin shugabannin kamfanin man.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

OSZAR »