'Yan Ta'adda Sun Kai Sababbin Hare Hare, an Kashe Bayin Allah Masu Yawa

'Yan Ta'adda Sun Kai Sababbin Hare Hare, an Kashe Bayin Allah Masu Yawa

  • Ƴan ta'adda ɗauke da makamai sun kai sababbin hare-hare a wasu ƙauyuka na jihar Benue da ke yankin Arewa ta Tsakiya
  • Miyagun sun hallaka sun hallaka mutane da dama a hare-haren da suka kai daga Juma'a zuwa Asabar a ƙananan hukumomi huɗu na jihar
  • Adadin mutanen da ƴan ta'addan suka hallaka ya haura mutane 20 bayan sun buɗe musu wuta a lokuta daban-daban

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Aƙalla mutane 23 ne suka rasa rayukansu tsakanin ranar Juma’a da Asabar sakamakon sababbin hare-hare a wasu ƙauyuka da ke cikin ƙananan hukumomi huɗu na jihar Benue.

Ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Logo, Kwande, Ukum da Guma.

'Yan ta'add sun kai hari a Benue
'Yan ta'adda sun kashe mutane a Benue Hoto: Fr. Hyacinth Iormem Alia
Asali: Twitter

Rahoton jaridar The Punch ya nuna cewa, an kashe manoma takwas da safiyar ranar Asabar a ƙauyen Jootar da ke ƙaramar hukumar Ukum.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Ƴan ta'adda sun yi ta'asa a Benue

Waɗanda lamarin ya rutsa da su sun kwana ne a yankin, inda aka kai musu hari da safe yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa gona.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa:

"Manoman suna kan hanyarsu ta zuwa gona ne aka kashe su. Amma ba za mu iya tabbatar da ko makiyaya ɗauke da makamai ne suka kai harin ko kuma ƴan bindigan ƙabilar Jukun ba."

Jootar dai ƙauye ne da ke da iyaka tsakanin jihohin Taraba da Benue, kuma yana daga cikin wuraren da ke fama da rikici tsakanin ƙabilun Tiv da Jukun.

A wani harin na daban da aka kai ranar Juma’a, wasu da ake zargin makiyaya dauke da makamai ne, sun afkawa ƙauyen Ayilamo da ke ƙaramar hukumar Logo, inda suka kashe mutane tara.

Hakazalika, makamancin waɗannan hare-hare da aka kai a ƙananan hukumomin Kwande da Guma sun hallaka mutane uku-uku, wanda hakan ya kai jimillar adadin waɗanda aka kashe zuwa 23.

Me hukumomi suka ce kan hare-haren?

Kwamishinan yada labarai na jihar Benue, Mathew Abo, ya tabbatar da aukuwar harin da aka kai a ƙauyen Jootar.

"Rahoton da na samu shi ne, an kashe manoma takwas a Jootar da safiyar ranae Asabar yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa gona."
"Yankin dai na kan iyaka ne tsakanin kabilun Tiv da Jukun, kuma rikici na ci gaba da faruwa a tsakaninsu. Ba za mu iya tabbatar da su waye suka kai harin ba."

- Matthew Abo

'Yan ta'adda sun kai hare-hare a Benue
'Yan ta'adda sun yi kashe-kashe a Benue Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Matthew Abo ya ƙara da cewa bai samu tabbacin hare-haren da aka kai a Guma, Logo da Kwande ba.

Kokarin da aka yi na tuntubar kakakin rundunar ƴan sandan jihar Benue, Catherine Anene, ya ci tura domin ba ta amsa kira ko saƙon tes da aka aike mata ba.

Sojoji sun hallaka hatsabibin ɗan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka wani hatsabin ɗan ta'adda a jihar Katsina.

Dakarun sojojin sun hallaka tantirin ɗan ta'addan ne mai suna Mallam a ranar, 5 ga watan Mayun 2025 da daddare.

Nasarar hallaƙa ɗan ta'addan na zuwa ne yayin da sojoji suke ƙara ci gaba da matsa lamba wajen fatattakar migagu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta [email protected]

OSZAR »