Wata Sabuwa: Majalisa Ta Gayyaci Gwamnonin Arewa 2, An ba Su Wa'adin Mako 1

Wata Sabuwa: Majalisa Ta Gayyaci Gwamnonin Arewa 2, An ba Su Wa'adin Mako 1

  • Majalisar wakilai ta bai wa gwamnonin Benue da Zamfara wa'adin mako guda su bayyana gabanta kan dakatar da 'yan majalisu a jihohinsu
  • Majalisar na binciken ƙarar da lauyoyi suka shigar kan zargin dakatar da 'yan majalisu 13 a Benue da 10 a Zamfara ba bisa ƙa'ida ba
  • Lauyoyin sun ce dakatar da 'yan majalisun ya sa an rasa adadin 'yan majalisun da ake bukata don gudanar da ayyukan majalisun jihohin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Majalisar wakilai ta bai wa gwamnan Benue, Hyacinth Alia, da takwaransa na Zamfara, Dauda Lawal, wa'adin mako guda su gurfana gabanta.

An ce gayyatar da hada da shugabannin majalisun jihohin biyu, kuma za su gurfana ne a gaban kwamitin majalisar da ke sauraron ƙorafe-ƙorafen jama'a game da rikicin siyasa a jihohin.

Majalisar Wakilai ta ba gwamnonin Benue, Zamfara wa'adin mako 1 su gurfana gabanta
Zauren majalisar wakilai, yayin wani zaman majalisar a Abuja. Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Majalisa ta ba gwamnoni 2 wa'adin mako 1

An bai wa gwamnoni da shugabannin majalisun jihohin biyu wa'adin ne biyo bayan kin amsa gayyatar da aka yi musu a ranar Alhamis, inji jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Kwamitin na binciken wata ƙara da ƙungiyar lauyoyi ƙarƙashin tutar Guardians of Democracy suka shigar dangane da zargin dakatar da 'yan majalisu 13 a Benue da 10 a Zamfara ba bisa ƙa'ida ba tun watan Fabrairu 2024.

Kudurin karar, wanda mataimakin mai magana da yawun majalisar, Hon. Philip Agbese, ya ɗauki nauyi, an gabatar da shi a zauren majalisar a ranar 27 ga Maris.

Lauyoyi sun shigar da karar Benue, Zamfara

A zaman farko na kwamitin a ranar Alhamis, Hon. Douglas Akya (Makurdi ta Kudu) ya jagoranci tawagar 'yan majalisun Benue da aka dakatar, yayin da Hon. Aliyu Ango Kagara (Talata Mafara ta Kudu) da shugaban marasa rinjaye na majalisar zamfara suka wakilci takwarorinsu.

Lauyan kare haƙƙin ɗan adam kuma babban lauyan masu ƙara, Barista Ihensekhien Samuel Junior, wanda ya bayyana tare da tawagar lauyoyi 12, ya bukaci kwamitin da ya gaggauta sauraron ƙarar, inji rahoton The Guardian.

Ya fayyace cewa ba a gabatar da ƙarar a gaban kowace kotu ba, kuma ko da tana gaban kotu, majalisar na da ikon ci gaba da sauraron ta ba tare da wata matsala ba.

Majalisa ta nemi ganin gwamnonin Benue, Zamfara kan rikicin siyasa a jihohin
Zauren majalisar wakilai, Abuja. Hoto: @HouseNGR
Asali: UGC

Ana so majalisa ta kwace ikon Benue, Zamfara

A cewar Barista Ihensekhien:

“A Zamfara, ana zargin gwamna ya sa an dakatar da ‘yan majalisu 11 sama da watanni 16. A Benue ma, an dakatar da ‘yan majalisu 13 a wani yanayi mai cike da ayar tambaya.”

Barista Ihensekhien ya ce wannan dakatarwar ta taso da wata gagarumar matsalar tsarin mulki, yana mai tambaya:

"Shin sauran 'yan majalisun za su iya samar da yawan adadin 'yan majalisun da ake bukata domin gudanar da ayyukan majalisa, a bisa ƙa'ida?"

Ya ƙara da cewa:

“Idan har adadin 'yan majalisun bai cika ka'ida ba, to majalisar wakilai, ƙarƙashin ikon tsarin mulkinta, za ta iya shiga tsakani ta hanyar karɓe ayyukan majalisa a irin waɗannan jihohin.”

Lauyoyi sun mamaye ginin majalisar wakilai

A wani labarin, mun ruwaito cewa, fiye da lauyoyi 1000 sun yi tururuwa a harabar majalisar tarayya, suna neman a karɓe ikon majalisun dokokin Benue da Zamfara.

Sun bayyana damuwarsu game da dakatar da 'yan majalisa 23 a Zamfara da Benue saboda sabani da gwamnoni.

Lauyoyin sun yi gargadin cewa gazawar magance matsalar na iya haifar da dokar ta-baci a jihohin biyu, wanda zai shafi majalisar tarayya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

OSZAR »