Wata Sabuwa: Gwamna Ya Fallasa Shirin Kawo Hargitsi, Raba Shi da Kujerarsa

Wata Sabuwa: Gwamna Ya Fallasa Shirin Kawo Hargitsi, Raba Shi da Kujerarsa

  • Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya koka kan wata maƙarƙashiya da ake shiryawa gwamnatinsa da kuma karan kansa
  • Hyacinth Alia ya bayyana cewa ya gano shirin wasu masu tayar da hargitsi tare da ɓata sunan gwamnatinsa domin a ayyana dokar ta ɓaci
  • Gwamnan ya nuna cewa daga cikin abin da masu mugun nufin suke so shi ne su ga an raba shi da kujerarsa ta mulkin jihar Benue

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya bayyana wata maƙarƙashiya da ake ƙulla masa.

Gwamna Hyacinth Alia ya bayyana cewa akwai wani yunƙuri mai hatsari da ake ƙoƙarin aiwatarwa domin tayar da zaune tsaye a jihar da nufin cire shi daga kan kujerarsa.

Gwamna Hyacinth Alia
Gwamna Alia ya ce akwai masu shirin raba shi da kujerarsa Hoto: Rev. Fr. Hyacinth Iormem Alia (Facebook)
Asali: Twitter

Gwamnan ya bayyana hakan ne ta bakin sakataren yaɗa labaransa, Tersoo Kula, a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Laraba a Makurdi, babban birnin jihar, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Wane makirci ake shiryawa gwamnan Benue

Ya ce wani ɓangare na wannan makirci shi ne yaɗa jita-jita da ƙarya ta hanyar kamfen ɗin yaudara da kuma shirya zanga-zangar bogi domin ɓata sunan gwamnatinsa.

Sakataren yaɗa labaran ya ƙara da cewa ana ɗaukar nauyin zanga-zanga domin yi wa gwamnatin Gwamna Hyacinth Alia baƙin fenti.

"Waɗannan zanga-zangar ba su samo asali daga ra’ayoyin jama’a ba, sai dai shiri ne na wasu ƴan siyasa masu baƙin jini da ke son ɗaukar fansa don cimma mummunan buri."
“Waɗannan mutane, da ke fama da son ganin jihar Benue cikin mawuyacin hali, na ganin cewa idan suka ɓata sunan jihar, za su iya tilastawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci."
“Wannan tunani nasu ya samo asali ne daga ƙin jinin cigaba da kuma burin komawa tsohuwar gwamnati wadda aka riga aka fatattaka saboda gazawarta."
“Babban burinsu shi ne su haifar da rikici da rashin tabbas domin su ci moriyar wannan rikici don amfanin kansu."

"Bari mu bayyana a fili, mun san waɗanda ke ɗaukar nauyin waɗannan zanga-zanga kuma mun fahimci dalilansu. Burinsu kawai shi ne su tumɓuke Gwamna Alia daga kan mulki, amma ba za su yi nasara ba.”
“Mutanen jihar Benue sun haɗa kai wajen goyon bayan gwamnansu, kuma ba za su bari waɗannan miyagun mutane su hana ci gaban da ake samu a ƙarƙashin jagorancinsa ba."

- Tersoo Kula

Gwamna Hyacinth Alia
Gwamna Alia ya ce masu son ganin bayansa ba za su yi nasara ba Hoto: Rev. Fr. Hyacinth Iormem Alia
Asali: Facebook

Gwamnan Benue ya nemi taimakon Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya miƙa ƙoƙon bararsa ga gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Gwamna Alia ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta taimakawa jihar kan matsalar rashin tsaron da ke ci mata tuwo a ƙwarya.

Hyacinth Alia ya bayyana cewa taimako ta fannin tsaro suke buƙata domin shawo kan matsalar hare-haren ƴan bindiga, ba a ƙaƙaba musu dokar ta ɓaci ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta [email protected]

OSZAR »