Okowa: Tsohon Gwamna Ya Maida N500bn don Hana Binciken EFCC? An Gano Gaskiya
- Tsohon gwamnan jihar Delta, Sanata Ifeanyi Okowa ya taɓo batun cewa ya mayar da N500bn zuwa cikin lalitar gwamnati
- Ifeanyi Okowa wanda ya yi takara da Atiku Abubakar a zaɓen 2023, ya bayyana cewa babu ƙamshin gaskiya a cikin jita-jitar
- Tsohon gwamnan ya bayyana cewa har yanzu hukumar EFCC na ci gaba da gudanar da bincike kan zargin da ake yi masa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Delta - Tsohon gwamnan Delta, Sanata Ifeanyi Okowa, ya yi magana kan jita-jitar da ke cewa ya mayarwa gwamnatin jihar Naira biliyan 500.
Sanata Ifeanyi Okowa ya ƙaryata jita-jitar da ke cewa ya mayar da Naira biliyan 500 ga gwamnatin jihar Delta, a matsayin wani ɓangare na binciken da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) ke gudanarwa.

Asali: Facebook
Jaridar The Punch ta ce Okowa ya musanta biyan kuɗin ne ta bakin babban sakataren yaɗa labaransa Olise Ifeajirika.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
An yaɗa jita-jita kan Ifeanyi Okowa
An yaɗa jita-jita cewa tsohon gwamnan ya mayar da fiye da Naira biliyan 500 a ɓoye ga gwamnatin jihar Delta a wani yunƙuri da ake ganin na kaucewa gurfanar da shi ne da kuma neman dawo da tasirinsa a siyasa.
Jita-jitar ta ce an mayar da kuɗin ne ba tare da an fallasa ba, a matsayin wani shiri na sirri domin kaucewa shari’a da kuma neman sulhu da hukumomin yaƙi da rashawa.
Me Okowa ya ce kan maida N500bn?
Sai dai, a martanin da tsohon gwamnan ya yi, ya bayyana cewa ko kaɗan babu ƙamshin gaskiya a cikin jita-jitar.
Olise Ifeajirika ya bayyana har yanzu hukumar EFCC na ci gaba da gudanar da bincikenta kan zargin da ake yi wa tsohon gwamnan.

Asali: Facebook
"Ba gaskiya ba ne cewa oga na, Okowa, ya mayar da irin wannan kuɗi. EFCC na da ƴancin yin aikinta."
“An gayyace shi aka nuna masa wasu takardu, kuma ya ba da amsa. EFCC tana zuwa jihar Delta tana gayyatar mutane don yin tambayoyi."
"Don haka mun yi amanna cewa ana ci gaba da bincike. Sai idan sun kammala bincike kuma sun samu hujjar da za ta sa a nemi a mayar da kuɗi ko a gurfanar da mutum a kotu."
“Babu gaskiya game da batun mayar da kuɗi ga gwamnatin Jihar Delta ko EFCC. Ina da yaƙinin cewa binciken har yanzu yana gudana kuma ba a kammala ba."
- Olise Ifeajirika
Okowa bai tsoron binciken EFCC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya bayyana cewa ba ya tsoron hukumar EFCC ta bincike shi.
Okowa ya yi waɗannan kalaman ne bayan ya amsa gayyatar da hukumar yaƙi da cin hancin ta yi masa kan badaƙalar N1.3trn.
Tsohon gwamnan ya nuna cewa akwai wani ƙulli da wasu ƴan siyasa ke yi masa a jihar saboda goyon bayan da yake ba Gwamna Sheriff Oborevwori.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng