Kwamishina Ya Tuna Allah, Ya Maida Kudin da Suka Ragu a Shirin Ciyarwa na Ramadan
- Kwamishinan ayyuka na musamman a Jigawa, Auwalu Ɗanladi Sankara ya mayar da kuɗin da suka ragu a shirin ciyarwa na Ramadan
- Ɗanladi Sankara ya mayar da kuɗi sama da Naira miliyan 300 bayan kammala shirin raba abincin buɗa baki ga marasa galihu a watan azumi
- Gwamnatin Jigawa ta yabi kwamishinan na ma'aikatar ayyuka na musamman, tana mai cewa hakan da ya yi ya cancanci yabo da jinjina
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jigawa - Kwamishinan ayyuka na musamman a jihar Jigawa, Auwalu Ɗanladi Sankara ya nuna halin rikon amana da gaskiya a bakin aiki.
Kwamishinan ya mayar da Naira miliyan 301 da suka ragu a shirin ciyar da masu azumi a watan Ramadan ga lalitar gwamnatin jihar Jigawa.

Asali: Facebook
Jaridar The Nation ta tattaro cewa kuɗin sun ragu ne bayan kammala shirin ciyar da marasa galihu da Gwamnatin Umar Namadi ta yi a watan azumin da ya gabata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Ramadan: Yadda shirin ya gudana a Jigawa
Rahotanni sun nuna cewa tun farko gwamnatin Jigawa ta ware Naira biliyan 4.8 domin aiwatar da shirin ciyar da mabukata da masu karamin ƙarfi a watan Ramadan na 2025.
Shirin ya gudana bisa tsari a kananan hukumomi 27 da ake da su a jihar Jigawa, inda aka kafa cibiyoyin raba abinci guda 700.
Kwamitin da aka kafa domin gudanar da shirin ya tabbatar da cewa a kowace rana, ana bai wa talakawa sama da 5,500 abinci tun daga farko har ƙarshen azumi.
Idan za ku iya tunawa, musulmi sun yi azumi 29 ne a watan Ramadan na bana, inda aka yi ƙaramar sallah ranar Lahadi, 30 ga watan Maris, 2025.
Kwamishina ya maida ragowar N301m
Bayan kammala aikin ciyarwar ne Naira miliyan 301 ta ragu kuma kwamishinan ayyuka na musamman, Ɗanladi Sankara bai yi wata-wata ba ya maida su lalitar gwamnati.
Majalisar zartarwa ta yaba da abin da kwamishina ya yi na mayar da kuɗin da suka ragu kasancewar ba a yi amfani da su ba, rahoton Tribune Nigeria.

Asali: Twitter
Gwamnatin Jigawa ta bayyana abin da Sankara ya yi a matsayin abin koyi wajen nuna gaskiya da rikon amana a cikin shugabanci.
Rahoton ya nuna cewa akalla mutane 300 ne ke samun abincin buɗe baki a kowanne daga cikin cibiyoyi 638 da ke fadin mazabu 287 a jihar Jigawa da azumi.
Baya ga ciyar da marasa galihu, shirin ya kuma amfani manoma da ‘yan kasuwa na cikin gida, domin an riƙa sayen kayan abinci da ake dafawa a cikin gida.
An ba jami'an tsaro mata damar sanya hijabi
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Jigawa ƙarƙashin Gwamna Umar Namadi ta amince mata jami'an tsaro su sanya hijabi.
Gwamnatin ta umurci kamfanonin tsaro masu zaman kansu uku da ke aiki a jihar da su ba mata damar sanya hijabi yayin aikin tsaro.
Wannan sanarwa ta fito ne daga majalisar zartarwa ta jihar ta bakin Kwamishinan yada labarai, Sagir Musa, bayan taron da aka gudanar a Dutse.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng