Amarya Ta Kashe Mijinta Kwana 9 da Ɗaura Masu Aure a Kano, An Ji Abin da Ya Faru

Amarya Ta Kashe Mijinta Kwana 9 da Ɗaura Masu Aure a Kano, An Ji Abin da Ya Faru

  • An samu tashin hankali a Kano yayin da wata amarya, Saudat Jibrin ta daba wa angonta Salisu Ibrahim wuka har lahira a ranar Litinin
  • Rahotanni sun bayyana cewa an daura auren Saudat da Salisu a ranar 27 ga Afrilu, kuma amaryar ta kashe angonta a darensu na tara
  • Wani ganau ya ce Saudat ta yanka Salisu a wuya bayan ta nemi ya rufe idonsa da sunan za su yi wasa, kuma ya mutu bayan an kai shi asibiti

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - An shiga tsananin tashin hankali a Unguwar Farawa da ke karamar hukumar Kumbotso, jihar Kano da wata amarya ta kashe angonta.

An ce amaryar, mai suna Saudat Jibrin Adam, ta kashe angonta Salisu Idris Ibrahim, ta hanyar daba masa wuka a wuyansa a daren ranar Litinin.

Ana zargin wata amarya ta kashe mijinta a Kano
Kwamishinan 'yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Ana zargin amarya ta kashe mijinta a Kano

Gidan rediyon Dala FM da ke Kano, ya tabbatar da rahoton a shafinsa na Facebook, inda ya kara da cewa an daure auren Saudat da Salisu a ranar 27 ga Afrilu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

An ce ko kafin aurensu, akwai 'yar rashin jituwa tsakanin masoyan, amma babu wanda ya yi tunanin abin ya yi girman da Saudat za ta yi ajalin mijinta.

Rahoton gidan rediyon ya nuna cewa wasu 'yan unguwar Farawa da suka fusata da lamarin, sun yi yunkurin daukar doka a hannu, amma jami'an tsaro suka hana su.

An ce har kawo yanzu, ba a san taka mai-mai inda jami'an tsaro suka ajiye amarya Saudat ba, gudun bore daga mutanen da suka riga suka fusata.

Yadda ake zargin Saudat ta kashe mijinta

Wani ganau, ya ce Saudat ta yaudari mijinta ta hanyar yi masa gadar zare a lokacin da dare ya yi, ta nemi ya rufe idonsa, kamar za ta yi masa wasa, amma ta daba masa wuka a wuya.

Makwabcin ango da amaryar, Dini Mada, ya shaida wa jaridar WikkiTimes cewa Salisu ya yi kokarin bayyana cewa matarsa ce ta farmake shi kafin ya wuta a asibiti.

Dini Mada ya shaida cewa:

"Mun hadu a wannan daren, muka yi wa juna 'sai da safe,' kowa ya shiga gidansa. Bayan kamar mintuna 10, mahaifiyarsa, wacce gidanta ke kusa da na danta, ta kira ni, tana cewa wasu mutane sun farmaki Salisu. Amma da muka je, muka tarar an yanka masa wuya.
"Da na tambaye shi, wa ya yi maka haka? Sai ya ce 'Dini, matata ce ta yanka ni da wuka a wuya, a cikin falonmu. Ta ce na rufe ido na, za ta yi mun wasa, ashe ta boye wuka, ina rufe ido na ta daba mun."

Ganau din ya shaida cewa 'yan sanda sun kama matar da ake zargi tana waya a cikin daki, ba tare da an san tana cikin gidan ba tsawon lokacin da ake nemanta.

An ji yadda wata amarya ta sa wuka ta yanke wuyan mijinta a Kano
Taswirar Najeriya da ke nuna jihar Kano. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Rashin jituwa bayan auren Saudat da Salisu

A cewar Dini, wani abokin mamacin ya shaida cewa akwai rigimar da ke tsakanin ma'auratan, wadda kadan daga 'yan uwansu ne suka san da ita.

"Duk da cewa sun yi auren soyayya, amma ta ki yarda da mijinta ya kusance ta, kuma ta ki yarda ta dafa masa abinci.
"Ko a ranar da aka kashe shi, sai da Salisu ya sayi Gurasa da nama domin su ci abincin dare bayan da ta ki dafa abinci a ranar."

- Dini Mada.

Wasu daga cikin 'yan uwan mamacin sun tabbatar da cewa an garzaya da Salisu asibiti amma ya rasu a can. Dan uwansa, Tanimu Idris ya ce an riga an yi masa sutura.

Kakakin 'yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaida wa manema labarai cewa zai fitar da karin bayani bayan gama bincike.

'A guji auren dole' - Hajara Umar

A zantawarmu da wata matashiya, Hajara Umar Muhammad, ta ce akwai bukatar iyaye su kawo karshen wannan auren zumuncin da 'ake tilasta' samari suna yi.

"Da yawa daga cikin auren zumunci da ake yi, ma'auratan ba kaunar juna suke yi ba, kawai suna hakura ne su yi auren saboda gudun bacin ran iyayensu.
"Idan aka yi rashin sa'a, yarinyar tana da karancin shekaru, to ka ga wauta ta hadu da kiyayya, sai ka ga ta illata shi ko ma ta kashe shi, saboda zaman kiyayya suke yi."

- Hajara Umar.

Matashiyar, wacce ta ke ba da shawarwarin zamantakewa a shafinta na Facebook, ta kuma ce akwai bukatar a rika yi wa ma'aurata gwajin lafiyar kwakwalwa, don ka da a yi kitso da kwarkwata.

"Yana da kyau a rika yi wa saurayi da budurwa gwajin lafiyar kwakwalwa kamar yadda ake yi na HIV da kwayoyin halitta, domin sanin ko akwai mai ciwon damuwa, ko zafin zuciya a cikinsu.

"Mutane na iya ganin kamar wannan ba wai wani abu ba ne, amma a zahiri, ciwon damuwa, zafin zuciya na sa mutum ya rika hawa dokin zuciya, ya aikata abin da zai zo daga baya yana da-na-sani."

- Hajara Umar.

Wata amarya ta hallaka mijinta a Neja

A wani labarin, mun ruwaito cewa, al'ummar Neja sun shiga jimami da alhini bayan wata sabuwar amarya ta aika mijinta lahira kasa da watanni biyu da aurensu.

An rahoto cewa amaryar ta yanke shawarar kawo karshen rayuwar mijinta ta hanyar daba masa wuƙa.

Rundunar 'yan sandan jihar Neja ta tabbatar da aukuwar wannan lamari, inda ta ce suna ci gaba da bincike don kama amaryar da ta gudu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

OSZAR »