Bayan Sallamar Kyari a NNPCL, Dangote Ya Yi Magana kan Sababbin Shugabanni

Bayan Sallamar Kyari a NNPCL, Dangote Ya Yi Magana kan Sababbin Shugabanni

  • Aliko Dangote ya yaba wa Bola Tinubu bisa nada sababbin shugabannin NNPCL, ya ce sun cancanta kuma za su kai kamfanin man ga ci gaba
  • Dangote ya ce sababbin shugabannin suna da ilimin fasaha da kwarewa da zai taimaka wajen sake fasalin NNPCL domin inganta tattalin arzikin kasa
  • Ya ce kalamansa game da wasu miyagu ba su da nasaba da sabon shugabancin NNPCL, wadanda ya ce ya nuna goyon baya ga burin gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Attajirin Nahiyar Afirka kuma shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya yi magana kan sababbin shugabannin NNPCL bayan sallamar Mele Kyari.

Dangote ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa zaben nagartattun shugabannin kamfanin mai na NNPCL.

Dangote ya yabawa Tinubu kan shugabancin NNPCL
Shugabancin NNPCL: Dangote ya yaba kokarin Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga.
Asali: Twitter

Dangote ya ce ya kai wa Shugaban kasa ziyara ne domin yaba masa da hadin gwiwar da ya yi wajen nada kwararrun shugabanni a NNPCL, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Dangote ya fadi masu hana cigaban kamfaninsa

Dangote ya mayar da martani kan tambayar manema labarai dangane da kalamansa kan gyara matatar man sa ta $20bn.

Ya ce wannan bayani ba shi da alaka da sababbin shugabannin NNPCL, wadanda suka nuna cikakken goyon baya ga bukatun kamfaninsa.

Ya bayyana cewa ‘miyagun’ da ya ambata su ne wasu manyan 'yan kasuwa da ke kokarin hana ci gaban tattalin arzikin Shugaba Tinubu.

NNPCL: Dangote ya kwarara yabo ga Tinubu

A cewar Dangote, sabbin shugabannin suna da hazaka da kwarewar shugabanci da za su taimaka wajen farfado da kamfanin mai na kasa.

Dangote ya ce shugabancin Bayo Ojulari yana nuna manufar Tinubu ta kawo sauyi da kirkire-kirkire a bangaren makamashi.

Ya ce:

“Muna da yakinin cewa wannan tawaga za ta magance matsalolin da ake fuskanta, ta dace da hangen Shugaba na tattalin arzikin $1trn.”

Ya ce wannan sabon shugabanci zai sake fasalin NNPCL domin inganta aiki da dorewar kasuwanci a nan gaba.

Dangote ya magantu kan sababbin shugabannin NNPCL
Dangote ya yabawa Tinubu kan shugabancin NNPCL. Hoto: Dangote Foundation.
Asali: Getty Images

Dangote ya yi alfahari da sababbin shugabannin NNPCL

Alhaji Aliko Dangote ya ce ayyuka da sauye-sauyen tsarin NNPCL sun nuna jajircewa wajen gaskiya, inganci da rikon amana a tafiyar da harkokin kamfanin.

Ya kara da cewa:

“Mutanen da ke kan gaba da manufofinsu na sauyi, na nuna kishin aiki da daukaka kwararru a harkokin makamashi.”

Dangote ya nuna kwarin gwiwa cewa sabbin shugabannin NNPCL za su kai bangaren makamashi na Najeriya zuwa mataki na gaba, Vanguard ta ruwaito.

Ya kuma tabbatar da cewa kamfanin Dangote zai ci gaba da mara wa gwamnati baya domin tabbatar da Najeriya mai albarkatu da wadata.

Tinubu ya taya Dangote murnar samun muƙami

Mun ba ku labarin cewa Shugaban kasa, Bola Tinubu ya taya attajirin dan kasuwa, Aliko Dangote murna bisa samun muƙami a Bankin Duniya.

Tinubu ya ce nadin ya dace da cancantar Dangote, la’akari da irin gudunmuwar da attajirin ya bayar ta fuskar zuba jari da samar da ayyukan yi.

Dangote zai yi aiki tare da manyan shugabannin kamfanoni na duniya domin samar da hanyoyin jawo zuba jari a kasashen da ke tasowa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a [email protected].

OSZAR »