Gwamnatin Abba Gida Gida Ta Yi Sababbin Nade Naden Mukamai a Jihar Kano

Gwamnatin Abba Gida Gida Ta Yi Sababbin Nade Naden Mukamai a Jihar Kano

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da nadin Malam Haladu Mohammed a matsayin Mai Ba da Shawara na Musamman kan ilimi
  • Sanarwar da gwamnati ta fitar ta ce wannan mataki na daga cikin kokarin Abba Kabir Yusuf na inganta tsarin ilimi tare da kara wa fannin inganci
  • Baya ga Malam Haladu, Gwamna Abba Gida Gida ya nada Muhammad Inuwa Jika a matsayin da Ramadan Yusuf a mukaman da suka jibanci sadarwa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da nadin Malam Haladu Mohammed a matsayin Mai Ba da Shawara ta Musamman kan inganta Ilimi.

Gwamnati ta ce an kirkiri mukamin ne domin kara inganta ayyukan gyaran ilimi a jihar Kano, wanda ya zo daidai da manufar gwamnatin Abba Kabir Yusuf na kawo sauyi a fannin ilimi.

Gwamnati
Gwamnan Kano ya nada sababbin mukamai a jihar Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Wannan na kunshe a cikin sanarwar da Darakta Janar na yada labaran gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Su wa gwamna Abba ya nada mukami?

Malam Haladu Mohammed kwararren masani ne a fannin ci gaba, wanda ke da gogewa sama da shekaru 30 a fannin gudanarwa, lura, tantancewa da koyar da dabarun ilimi.

Ya taba yin aiki a matsayin mai bayar da shawara a shirye-shiryen gyaran ilimi da hukumar USAID ta Amurka da kuma DFID ta Birtaniya suka dauki nauyi a Najeriya, Ghana da Liberia.

An haifi Malam Haladu a kauyen Sanakur, da ke karkashin mazabar Badume a karamar hukumar Bichi.

Kafin ya shiga kungiyoyin ci gaba na duniya a shekarar 2002, ya yi aiki a matsayin malami a Kwalejin Kere-kere, Kimiyya da Koyar da Darussa ta Kano (CAS Kano).

Sauran wadanda Abba ya nada mukamai

Sanarwar ta kara da cewa sauran mutanen da gwamna Abba ya nada sababbin mukamai sun hada da, Muhammad Inuwa Jika a matsayin Mataimaki na musamman kan gyaran kayan Sadarwa.

Sai kuma Ramadan Yusuf da aka nada Mataimaki na Musamman kan Kula da Labarai ga gwamna Abba Kabir Yusuf.

Gwamnati
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da nada mutane uku mukamai a Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Sanarwar ta ce gwamnan ya bukaci wadanda aka nada da su yi aiki da himma da kwarewa, domin cimma manufofin ci gaban jihar Kano.

Dukkan wadannan nade-naden sun fara aiki ne nan take domin fara kara inganta ayyuka a gwamnatin Kano.

Abba Gida Gida ya yi sababbin nade-nade

A wani labarin, mun wallafa cewa gwamna Abba Kabir Yusuf, ya amince da jerin sababbin nade-nade da sauye-sauye a muhimman bangarori na gwamnati, domin bunkasa ci gaba a Kano.

Sanarwar ta ce ta bayyana cewa wadannan nade-nade sun nuna kudurin gwamnatin Abba Gida Gida na aiki da kwararru masu hazaka da gogewa domin jagorantar sauyi da ci gaba a jihar

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada Jamila Magaji Abdullahi a matsayin Akanta Janar ta Kano, kuma kwararriyar ma’aikaciya ce da ta dade a fannin harkokin kudi da haraji .

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

OSZAR »